Babban malamin Tijjaniyya, Sheikh Umar Bojude, ya rasu
Published: 24th, August 2025 GMT
Ɗariƙar Tijjaniyya a Jihar Gombe, ta yi babban rashi bayan rasuwar ɗaya daga cikin fitattun malamanta, Sheikh Umar Bojude.
Sheikh Bojude shi ne babban limamin Masallacin Juma’a na Alhaji Gidado Dalibi Yahaya (AG Dalibi).
Japan za ta bai wa Najeriya rancen $190m don inganta wutar lantarki Rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC a GombeMalamin ya rasu a ranar Lahadi, kuma an yi jana’izarsa a unguwar Jan Kai da misalin ƙarfe 5 na yamma.
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ta bakin Daraktan Yaɗa Labaransa, Isma’ila Uba Misilli.
Ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga ɗariƙar Tijjaniyya, iyalansa da kuma al’ummar jihar.
“Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalan marigayi, ɗariƙar Tijjaniyya, Fityanul Islam da dukkanin Musulmi a Gombe da Najeriya baki ɗaya.
“Haƙiƙa rasuwarsa babban rashi ne,” in ji Gwamna Yahaya.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa, Ya jikansa da rahama, Ya kuma sanya shi cikin Aljannar Firdausi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗariƙa rasuwa Tijjaniyya
এছাড়াও পড়ুন:
An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya (NUT) reshen Jihar Gombe, ta ziyarci shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar, Barista Sani Ahmad Haruna, a ofishinsa da ke Gombe.
Shugaban ƙungiyar, wanda shi ne shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, ya bayyana cewa gwamnati da shugabannin ƙananan hukumomi za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen inganta walwalar malamai.
Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyiYa ce: “Ba za mu taɓa barin malamai su shiga cikin matsanancin hali ba. Za mu duba matsalolinsu domin tabbatar da walwalarsu da ci gaban ilimi a jihar.”
Sani, ya kuma yaba da yadda NUT ke tattaunawa cikin lumana da kawo shawarwari maimakon ɗaukar matakan da za su iya kawo tsaiko ga harkar ilimi.
A nasa jawabin, shugaban NUT na jihar ya ce sun kai ziyarar ne domin tattauna matsalolin da malamai ke fuskanta, musamman na makarantun firamare da ƙananun sakandare da ke ƙarƙashin kulawar ƙananan hukumomi.
Ya ƙara da cewa manufar NUT ita ce samar da fahimtar juna da haɗin kai tsakaninsu da shugabannin ƙananan hukumomi domin gano hanyoyin magance matsaloli cikin lumana.