Kwamandan Rundunar Kudancin Amurka ya sanar da murabus kan batun ayyukan soji a yankin Caribbean
Published: 18th, October 2025 GMT
Tashar talabijin ta CNN ta bayar da rahoton cewa, Janar Alvin Holsey, kwamandan rundunar sojin Amurka ta Kudu, ya yanke shawarar yin murabus nan da watan Disamba, saboda takun-saka tsakaninsa da sakataren tsaron Pete Hegseth, kan rashin jituwar da aka samu game da batun ayyukan sojojin Amurka a yankin Caribbean.
Rahoton ya bayyana cewa, a makwannin da suka gabata ne Janar Holsey ya bayyana damuwarsa kan sahihancin wadannan ayyuka, yayin da Hegseth ya nuna takaicinsa kan yadda ayyukan ke tafiyar hawainiya, lamarin da ya janyo cece-kuce tsakanin bangarorin biyu.
A cewar rahoton, manyan jami’an biyu sun tayar da jijiyoyin wuya ne a yayin wani taro a ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon a makon da ya gabata, inda suka yi musayar miyau da kuma yi wa juna zafafan kalamai, lamarin da ya kai ga sanar da murabus din Holsey a hukumance.
Janar Holsey ya karbi mukaminsa ne a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata kuma ya jagoranci Rundunar sojin Amurka a yankin Kudancin kasar a daidai lokacin da ake samun karuwar ayyukan sojin Amurka a yankin Caribbean.
Jaridar New York Times ta bayyana cewa Janar Holsey zai bar mukaminsa a karshen shekara.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kwamandan Dakarun Sa Kai Na Iran Ya Bayyana Cewa: Iran A Yayin Yaki Da Isra’ila Ta Tarwatsa Wasu Muhimman Wurare 21 October 17, 2025 Abokan Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya Sun Ce: Sake Dawo Da Takunkumin Da Aka Kakaba Kan Iran Baya Kan Doka October 17, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Wuce Gona Da Irin Isra’ila Kan Kudancin Kasar Lebanon October 17, 2025 Kungiyar Hamas Ta Yi Kira Da Matsa Wa Isra’ila Lamba Da Ta Cika Sharuddan Yarjejeniyar Gaza October 17, 2025 Zanga-Zangar Miliyoyi A Yemen Ta Jaddada Alkawari Ga Shahidai Da Ci Gaba Da Goyon Bayan Al’ummar Falasdinu October 17, 2025 Yemen Ta Sanar Da Nadin Sabon Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Kasar October 17, 2025 Iran Tayi kira Da A Warware Rikici Tsakanin Afghnistan Da Pakistan Ta Hanyar Diplomasiya October 17, 2025 Hizbullah: Amurka ِDa Isra’ila Ba za Su Iya Yin Nasarar Akanmu ba. October 17, 2025 Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin sabon Shugaban INEC October 17, 2025 Shugaban Kasar Sudan Yana Ziyarar Aiki A Kasar Masar October 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Araghchi: Halayyar Amurka ce yin matsin lamba maimakon diflomasiyya a dangantaka ta kasa da kasa
Ministan Harkokin Wajen Iran ya ce: “Bayan zagaye biyar na tattaunawa, yayin da muke shirin zagaye na shida, ɓangaren Amurka ya karya hanyar diflomasiyya da kuma ƙoƙarin shiga tsakani da ake yi.”
Seyyed Abbas Araghchi, Ministan Harkokin Wajen Iran, ya ce a wata hira da ya yi da shirin “Ma’a Musa al-Far’ei” a ranar Litinin: “Abin takaici dokokin ƙasa da ƙasa da tsarin duniya sun yi tasiri ga yanayin Amurka na amfani da ƙarfi a dangantakar ƙasa da ƙasa.”
A cewar Pars Today, Araghchi ya ƙara da cewa: “Wannan ya bayyana a cikin tsoma bakin soja na ba bisa ƙa’ida ba da kuma aiwatar da ayyukan kisan kai duk inda suka ga dama.”
Ya jaddada cewa: “Abin da muke gani a yau ya zama tushen damuwa ta duniya.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Aljeriya: Taron Kasashen Afirka Don Amincewa Da Mulkin Mallaka A Matsayin Laifi December 2, 2025 Lebanon: An Gudanar Da Taron Musulunci da Kiristanci a Beirut tare da halartar Paparoma December 2, 2025 Chuck Schumer: Trump Ba Shi da Ikon Kaddamar da Yaki Kan Venezuela December 2, 2025 Najeriya: Matatar Dangote Za Ta Mika Tataccen Mai Lita Biliyan 1.5 A Watan Disamba December 2, 2025 Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Trump na ware Afirka ta Kudu daga G20 December 2, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165 December 1, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164 December 1, 2025 Baqaei: Amurka Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya December 1, 2025 Paparoma Leo Na 14 Yana Ziyarar Aiki Na Kwanaki 3 A Kasar Lebanon December 1, 2025 Kamaru: Madugun Adawa Ya Rasu A Gidan Kaso December 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci