Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano
Published: 22nd, September 2025 GMT
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama gungun wasu mutane da ake zargi da safarar mata zuwa kasar Saudiyya.
Hisbah ta dakile yunkurin mutanen ne a yayin da suke kokarin safarar wasu mata hudu daga jihohin Kano da Jigawa da Yobe, ta hannun wakilansu da ke sassan kasashen Yammacin Afirka?
Mataimakin Babban Kwamnand Hukumar, Dakta Mujahideen Aminudeen, ya ce masu safarar matan sun yaudarin matan da aka ceto cewa za su yi musu biza zuwa kasar Ghana inda daga nan za su wuce da su zuwa Saudiyya domin sama musu ayyukan yi.
An kana daya daga cikin mutanen ne a ranar Lahadi, wanda hakan ya kai ga cafke shugabansu da ake kira Bashir Sani Ibrahim.
Ballon d’Or: Wa zai lashe kyautar 2025? Yadda aka kashe jami’an tsaro 53 cikin mako biyu NAJERIYA A YAU: Yadda Wata Bakuwar Cuta Take Cin Naman Jikin Mutanen MalabuUku daga cikin matan masu shekaru 30 sn fito ne daga jihohin Kano da Jigawa a yayin da hudun mai shekara 35 da fito daga Jihar Yobe.
Dakta Aminudeen ya bayyana cewa matan sun biya mutanen Naira milian bibbyu, za su ciko Naira miliiyan 1.5 kowannensu domin sama musu biza.
Ya ce, “Wannan shi ne abin da muke ta gargadin mutane a kai — kar a yarda da tafiya ba tare da sanin inda za a kai su ba. Ana yaudarar mutane, ana kwace musu kuɗinsu, kuma da zarar sun isa ƙasashen waje ana tilasta musu shiga harkar karuwanci, fataucin miyagun ƙwayoyi ko kuma tsunduma cikin rayuwar kunci.”
Ya shawarci ’yan Najeriya da su guji irin waɗannan haɗurran tafiya, yana mai jaddada cewa kuɗin da ake ɓatawa wajen irin wannan safarar ya fi dacewa a saka shi a harkokin kasuwanci a gida.
“Da naira miliyan biyu ko uku da rabi, mutum zai iya fara kasuwanci mai kyau a Najeriya maimakon fadawa tarkon waɗannan miyagun dabaru,” in ji shi.
Ya nuna godiya cewa an samu damar dakile wannan yunkuri, yana mai cewa da masu safarar mutanen sun ci nasara, da lallai matan sun ɓace ba tare da sahu ba.
“Mun tattara bayanansu da fasfofonsu muka mika su ga Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane (NAPTIP). Za mu ci gaba da sa ido har sai an kammala bincike kan lamarin,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: safarar mata Saudiyya
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda, Sun Kama Masu Laifi
Rundunar sojojin ta ce waɗannan hare-hare sun nuna ƙudirin gwamnati wajen yaƙi da rashin tsaro a faɗin ƙasar nan.
Ta kuma tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa za ta ci gaba da ƙoƙari domin kare al’umma daga ‘yan ta’adda da sauran masu laifi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp