Aminiya:
2025-09-20@17:23:52 GMT

Duk shugaban da bai yi aiki ba bai kamata a sake zaɓarsa ba — Jonathan

Published: 20th, September 2025 GMT

Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce duk wani shugaba da bai yi aiki yadda ya kamata ba, bai kamata a sake zaɓarsa ba.

Ya yi gargaɗin cewa maguɗin zaɓe na ɗaya daga cikin manyan barazana ga dimokuraɗiyya a Afirka, kuma idan ba a gyara tsarin ba, ’yan kama-karya za su zama wajen zama.

Yadda za ka dawo da kuɗinka da ka yi kuskuren turawa wa wani An tsinci gawar kwamandan hukumar NDLEA a otel a Kalaba

Jonathan, ya yi wannan jawabi ne a taron shekara-shekara na Tattaunawar Gidauniyar Goodluck Jonathan da aka gudanar a Birnin Accra, na Ƙasar Ghana.

Ya ce mutanen Afirka na son a yi amfani da ƙuri’unsu don su samu shugabanni da za su inganta ilimi, tsaro, kiwon lafiya, ayyukan yi.

A cewarsa, idan shugabanni suka gaza bayar da waɗannan abubuwa, jama’a kan rasa muradi da kyakkyawan fata.

Ya ƙara da cewa a inda ake gudanar da sahihin zaɓe, jama’a kan iya tsige shugaban da bai yi aiki , amma a ƙasashen Afirka, ’yan siyasa na amfani da maguɗin zaɓe don ci gaba da yin mulki ko da jama’a ba sa so.

Tsohon shugaban ya kuma yaba da yadda matasa ke ƙara shiga harkokin siyasa, sai dai ya jaddada cewa har yanzu suna buƙatar jagoranci da hikimar dattawa domin su yi nasara.

A wajen taron, Shugaban Ƙasar Ghana, John Dramani Mahama, tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya Olusegun Obasanjo, da wasu shugabanni sun yi kira da a gaggauta gyara tsarin dimokuraɗiyya a Afirka.

Mahama ya ce dimokuraɗiyya ba za ta ɗore ba idan ‘yan Afirka ba su tsaya tsayin daka wajen kare ta da ɓunƙasa ta ba.

Ya ce dole a bunƙasa cibiyoyi, a kawo ci gaba, a tabbatar da gaskiya da riƙon amana, tare da kare ’yancin ’yan jarida.

Obasanjo, wanda shi ne ya jagoranci taron, ya ce yadda ake tafiyar da dimokuraɗiyya a Afirka a yanzu ba za ta ɗore ba, dole sai an yi wa tsarin gyara.

Sauran mahalarta taron kamar Shugaban Hukumar ECOWAS, Doktq Omar Touray, da Bishop Matthew Hassan Kukah na Katolika a Sakkwato, sun jaddada cewa dimokuraɗiyya a Afirka bai kamata ta tsaya kan zaɓe kawai ba, sai an haɗa da gaskiya da riƙon amana.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Dimokuraɗiyya gidauniya taro dimokuraɗiyya a Afirka

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Guinea-Bissau Ya Goyi Bayan Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Da Sin Ta Gabatar

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Halarci Ɗaurin Auren Ɗan Yari, Ya Kai Ziyara Gidan Tsohon Shugaban Ƙasa Buhari
  • An Kammala Taron Dandalin Tattauna Batun Tsaro Na Xiangshan
  • Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna
  • Nan Ba Da Jimawa Ba Hauhawar Farashin Kayayyaki Za Ta Zama Tarihi —Fadar Shugaban
  • Najeriya Ta Shirya Karɓar Wasannin Kungiyar Kasashen Renon Ingila A 2030– Tinubu
  • Shugaban Guinea-Bissau Ya Goyi Bayan Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Da Sin Ta Gabatar
  • Shugaban Kasar Iran Ya bayyana Yadda Hadin Gwiwa Tsakanin Iran Da Rasha Ya Kawo Ci Gaba Tsakaninsu
  • Uwargidan Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu Ta Yi Kira Ga Zaman Lafiya A Duniya
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers