Rushe Kasuwar Alaba Rabo: ’Yan Arewa sun bukaci a biya su diyya
Published: 25th, August 2025 GMT
’Yan Arewa a Kasuwar Alaba Rago, shahararriyar kasuwar ’yan Arewa a Jihar Legas sun roki gwamnatin jihar ta biya su diyya kan asarar da suka yi sakamakon rushe kasuwar da gwamnati nta yi.
Sun bayyana cewa asarar da suka tafka ta haura Naira biliyan 20 bayan Gwamnatin Legas ta rusa masallatai sama da 40 da shaguna kimanin 3,000 a Kasuwar wadda suka kafa shekara 45 da suka gabata a jihar.
A karo na biyu a ’yan kwanakin nan mahukunta a Jihar Legas suka rushe sassa da dama na kasuwar, wadda ta yi fice da kasuwancin kayan abinci da dabbobi da karafa da sauran kayan masarufi, wacce Hausawa suka kafa a shekarar 1979.
A cikin watan Mayun 2024, jami’an hukumar ’yan sandan jihar Legas sun mamaye kasuwar, inda suka ce an gudanar da aikin ne domin kawar da bara-gurbi a kasuwar.
NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyan ‘Ya’yan Su Yau Shugabannin Tsaron Afrika 54 ke taro a Abuja Zargin N6.5bn ya dabaibaye hadimin Gwamnan KanoA ranar Lahadin makon jiya, 17 ga watan Agusta, kuma aka fara rusau na baya-bayan nan a kasuwar, lamarin da ya ci gaba zuwa ranar Laraba 20 ga watan Agustan, inda dubban ’yan kasuwa suka rasa matsugunnansu.
Alhaji Adamu Katagum, Wazirin Sarkin Alaba Rago, ya shaida wa Aminiya cewa sama da shaguna 3,000 ne aka rushe ciki har da masallatai 40, inda ya kiyasta cewa asarar da ’yan kasuwa suka yi ya haura Naira biliyan 20.
Ya ce ’yan Arewa ne suka kafa kasuwar tun lokacin da wajen yake jeji ne da kuzazzabai, inda suka zuba jari mai yawa don bunkasa ta.
“A wancan lokacin, wannan wurin ya kasance da kurmi da fadama, babu hanyar sadarwa, ‘yan kasuwa Hausawa ne suka bunkasa ta da albarkatunsu da kuma kudin shigarsu tsawon shekaru da dama.
“Gwamnati ba ta taba kashe ko sisi daya a nan ba, duk da haka muna biyan haraji da hakkin gwamnati a kowane mataki, sai suka zo suka rushe abin da muka yi ta yi tsawon shekaru 50 muna ginawa ba tare da bin ka’ida ba, wannan babbar asara ce ga mu ’yan Arewa da ke kokarin samun abin dogaro da kai a nan,” Inji Katagum.
Ya kuma bayyana takaicinsa, inda ya ce, “Mun shafe sama da shekara 50 muna gina wannan kasuwa, mun sha wahala wajen kafa sana’o’inmu a nan, kuma a rana guda suka rusa komai ba tare da gargadi ba, mun kirga akalla masallatai 40 da aka lalata.”
Wani da abin ya shafa, Alhaji Muhammed Rabiu ’Yan Masarain, ya koka da abin da ya bayyana a matsayin rashin adalci duk da irin gudunmawar da ’yan kasuwar ke bayarwa wajen bunkasa tattalin arzikin Jihar Legas.
Ya kara da cewa al’ummar yankin sun goyi bayan jam’iyya mai mulki a Legas tun a shekarar 1999, kuma ya ce wannan ba hanya ce da ta dace ba don saka musu da biyayyar da suke yi.
“Mu ’yan Najeriya ne, kuma Legas wani bangare ne na Najeriya, muna da ’yancin kasancewa a nan, inda muka zauna muna fatauci tunda ba komai ba ne sai fadama. Mu ba zaune muke a matsugunan da ba bisa ka’ida ba ne, kadarorinmu suna da takardun doka, kuma muna biyan duk haraji da ake bukata.
“Duk da haka, mun tashi ne a safiyar ranar Litinin, sai muka yi taho-mu-gama da ’yan sanda dauke da makamai, wadanda suka yi rakiya ga wadanda suka rusa mana dukiyoyinmu da rayuwarmu suka ruguje su cikin kiftawa da bisimillah,” inji Rabiu a cikin wata murya mai cike da damuwa.
Kawo yanzu dai ’yan kasuwar na ci gaba da kasuwanci a yashe cikin rana da dari yayin da ruwan sama ke bugun su a lokacin da ya sauka.
Zuwa lokacin hada wannanl labairn yanzu Gwamnatin Jihar Legas ba ta fitar da wata sanarwa ba game da aikin na rusau da aka yi a daya daga cikin kasuwannin jihar da ke tara jama’ar Arewa, kuma kasuwa mafi yawan jama’ar Arewa jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan kasuwa Alaba Rago Arewa Gawmnatin Jihar Legas Kasuwar Alaba Rago Yan Arewa Jihar Legas jihar Legas
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma
A nata bangare, Amurka za ta dage aiwatar da matakai bisa bincikenta karkashin sashe na 301 na dokar cinikayya ta 1974, wanda zai shafi sashen jiragen ruwa na Sin, da hidimomin sufurinsu, da na kirar jiragen ruwan na Sin da karin shekara daya. Sakamakon hakan, ita kuma Sin za ta dage aiwatar da matakan martani ga sashen Amurka a wannan fanni da shekara daya, da zarar Amurkan ta aiwatar da na ta matakan.
Kakakin ya ce “An Kai Ruwa Rana” kafin cimma wannan sakamako, kuma Sin na fatan ganin ta ci gaba da aiki tare da tsagin Amurka, ta yadda za su hada karfi wajen tabbatar da an aiwatar da sakamakon, da ingiza karin tabbaci, da daidaito cikin dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu, da kuma tattalin arzikin duniya baki daya. (Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA