Pakistan: Makaman Nukiliyarmu Suna Cikin Yarjejeniyar Tsaro Da Mu Ka Kulla Da Saudiyya
Published: 20th, September 2025 GMT
Ministan tsaron kasar Pakitsan Khaje Asif ya fada a jiya Juma’a cewa, makaman Nukiliyar da kasarsa take da su, wani sashe ne na yarjejeniyar tsaro da su ka kulla da kasar Saudiyya. Haka nan kuma ya kara da cewa; Yarjejeniyar ta tsaro ce tsagwaronsa, kuma manufarta ita ce aiki tare a tsakanin kasashen biyu a wannan fagen.
Asif wanda tashar talabijin din “Geo News” ta yi hira da shi ya kuma ce; Idan daya daga cikin kasashen ta fuskanci hari,to za mu mayar da martani na hadin gwiwa.”
Ministan tsaron na kasar Pakistan ya kuma ce; Ba tare da ambaton suna ba,amma duk wanda ya kai harin wuce gona da iri, to zai fuskanci mayar da martani na hadin gwiwa.
Da yake amsa tambaya akan ko sun shawarci Amurka akan kulla wannan irin yarjejeniya ta tsaro da Saudiyya, ministan tsaron na kasar Pakistan ya ce, babu bukatar a shigar da wani bangare na uku a cikin batun.
Da yake magana akan sauye-sauyen siyasa da suke faruwa a duniya, ministan tsaron Pakistan Asif ya ce; Ba da jimawa ba, kasar China za ta zama mai jagorantar duniya.
A ranar Laraba din da ta gabata ne dai kasashen Pakistan da Saudiyya su ka kulla yarjejeniyar tsaro,wacce fira minista Shahbaz da yarima mai jiran gado Muhamad Bin Salman su ka rattaba hannu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Adadin Falasdinawa Da HKI Ta Kashe Da Jikkatawa Sun Haura 230,000 September 20, 2025 Sheikh Na’im Kassim Ya Kira Yi Saudiyya Da Ta Bude Sabon Shafi Da Gwagwarmaya September 20, 2025 Arqchi: Iran Ba Ta Amince Da Duk Wani Matakin Matsin Lamba Da Rashin Adalci Ba September 20, 2025 Jakadan Iran A MDDuniya Ya Ce: Kwamitin Sulhu Ya Rasa Damar Tattaunawa Da Fahimtar Juna September 20, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Jaddada ‘Yancin Kasar Na Mayar Da Martani Kan Sabawa Doka September 20, 2025 Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Mayar Da Martani Kan Zargin Shugaban Kasar Faransa September 20, 2025 Shugaban Kasar Faransa Zai Amince Da Kasar Falasdinu A Ranar Litinin Mai Zuwa A Birnin New York September 20, 2025 Tinubu Zai Dauki Nauyin Gasar Wasanni Commonwealth A 2030 September 19, 2025 Kungiyar Tarayyar Turai EU Ta Mika Bukatunta Ga Kasar Iran. September 19, 2025 Dakarun Sojin Yamen Su Kai Hare-hare A Muhimman Wurare A HKI. September 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher
Qatar ta bayar da tallafin gaggawa ga mutanen da suka rasa matsugunansu a Sudan
Gwamnatin Qatar ta aika da agajin gaggawa da tallafin jin kai zuwa birnin Ad-Dabba da ke Jihar Arewacin Sudan domin rage wa dubban mutanen da suka rasa matsuguninsu da ke tserewa daga El Fasher, babban birnin Jihar Arewacin Darfur.
Ma’aikatar Harkokin Waje ta Qatar ta bayyana cewa: “Wannan tallafin ya zo ne a cikin tsarin jajircewar Qatar na tallafawa ‘yan uwantaka na Sudan, musamman idan aka yi la’akari da mawuyacin halin jin kai da fararen hula ke ciki, ciki har da karancin abinci mai tsanani da kuma karuwar bukatar matsugunai da kayan masarufi.”
Sanarwar ta kara da cewa wannan tallafin wani bangare ne na kokarin da Qatar ke yi na tsayawa tare da ‘yan uwantaka na Sudan da kuma rage musu wahalhalun da rikicin yaki da makamai ya haifar. Haka nan ya kunshi rawar da Qatar ke takawa wajen karfafa martanin jin kai da kuma gina gadoji na hadin kai da al’ummar da abin ya shafa a fadin duniya.
Tallafin ya kunshi kimanin buhuhunan abinci 3,000, tantuna 1,650, da sauran kayayyakin bukatu, wanda Asusun Ci Gaban Qatar da kuma Hukumar Ba da Agaji ta Qatar suka bayar, don tallafawa wadanda suka rasa matsuguninsu daga El Fasher da yankunan da ke kewaye. Ana sa ran sama da mutane 50,000 za su amfana daga wannan tallafin, wanda ya haɗa da kafa sansanin agaji na musamman na Qatar mai suna Qatar Charity.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya November 2, 2025 Amurka : zamu dauki matakin soja idan Najeriya ta gaza kawo karshen kashe Kiristoci November 2, 2025 Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza November 2, 2025 Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci