Abba ya tarbi tagwayen da aka raba da juna bayan yi musu tiyata a Saudiyya
Published: 13th, September 2025 GMT
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tarbi tagwayen da aka haifa manne da juna, inda aka raba su da juna ta hanyar yi musu tiyata a Ƙasar Saudiyya.
Tagwayen waɗanda ’yan asalin Najeriya ne, sun iso filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda tawagar Saudiyya ta tarbe su.
Ambaliya: SEMA ta raba kayan tallafi ga gidaje 90 a Gombe ’Yan bindiga sun harbi fasinjoji 2, sun sace makiyaya a NejaAn yi musu tiyata a Asibitin Ƙwararru na Yara King Abdullah da ke Riyadh, bisa umarnin Sarki Salman bin Abdulaziz Al-Saud da Yarima Mohammed bin Salman.
Hassana da Husaina sun tafi Saudiyya tun a watan Oktoban 2023, inda likitoci suka gano cewa suna manne da juna ne ta ƙasan cikinsu, ƙugu da ƙashin baya, lamarin da ya sa matsalar ta yi tsanani.
Tawagar ƙwararrun likitoci 38 daga fannoni daban-daban kamar masu tiyatar yara, k5wakwalwa, ƙashi, fitsari da fata ne, suka shafe sa’o’i 14 suna aiki a matakai tara kafin su raba su cikin nasara.
Wannan aiki ya kasance ɗaya daga cikin mafi wahala amma ya yi nasara cikin shirin Saudiyya na raba tagwaye.
Jakadan Saudiyya a Kano, Khalil Ahmed Al-Admawi, ya yaba da nasarar aikin, inda ya bayyana cewa hakan alama ce ta jajircewar Saudiyya wajen taimakon bil adama.
Ya kuma ce za su ci gaba da tallafa wa ƙasashe irin su Najeriya ta hanyar Cibiyar Agaji ta Sarki Salman.
A nasa jawabin, Gwamna Abba ya yi alƙawarin ɗaukar nauyin kula da lafiyar tagwayen, iliminsu da sauran buƙatunsu na yau da kullum.
Wannan ita ce tiyatar raba tagwaye ta 65 da aka yi nasara a shirin Saudiyya, wadda ta taimaka wa tagwaye 150 daga ƙasashe 25 cikin shekaru 35 da suka wuce.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Cibiya Gwamna Abba Nasara Rabawa Saudiyya Tagwaye Tiyata
এছাড়াও পড়ুন:
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna
Wannan mataki ne awanni kaɗan bayan ɓangaren Damagum ya dakatar da Anyanwu da wasu mutane uku, lamarin da ya ƙara ta’azzaea rikicin shugabanci a cikin jam’iyyar PDP.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA