Georgieba ta kuma gargadi duniya kan barazanar da fitar da kudade ta haramtacciyar hanya (IFFs) ke yi, inda ta ce wannan matsala ta zama babbar abin da ke lalata tattalin arziki da tsarin kudi na kasashe a fadin duniya.

 

A cewarta, fitar da kudade ta haramtacciyar hanya wacce ta hada da satar kudaden gwamnati, kudaden da suka fito daga ayyukan laifi, da mu’amalolin dijital da ba a iya bibiyarsu na ci gaba da lalata tsarin mulki, rage kudaden gwamnati, da durkusar da kokarin ci gaba, musamman a kasashe masu tasowa.

 

A cikin wani jawabin manufofi na baya-bayan nan, jami’an IMF sun bayyana cewa IFFs yanzu suna zuwa ta fannoni da dama. Wannan ya hada da karkatar da kudaden haraji kai tsaye zuwa aljihun wasu mutane da kuma karkatar da kudaden masu zaman kansu zuwa haramtattun harkoki da ke barazana ga jin dadin kasa.

 

Sun kara da cewa tattalin arzikin dijital ya kara tsananta wannan matsala, inda kudaden dijital kamar Bitcoin ke ba da damar yin mu’amalolin kudi ba tare da a san masu aikata su ba.

 

Shugabar IMF ta ce: “Za ka iya samun kudi, kudin da aka sace kai tsaye daga al’ummar masu biyan haraji. Haka kuma akwai kudaden masu zaman kansu da ake karkatawa zuwa ayyukan laifi da ke lalata jin dadin ‘yan kasa.”

“Yanzu da kudaden dijital, ana iya tallafa wa ayyukan laifi ba tare da a gano su ba. Wannan babbar matsala ce, kuma dole ne mu dauke ta da muhimmanci.”

Dabarar IMF Wajen Yakar Kudaden Haram:

A martaninta, IMF ta bayyana cewa ta karfafa tsarinta na yaki da safarar kudade da kuma hana tallafa wa ta’addanci (AML/CFT) bayan cikakkiyar bita da aka gudanar a shekarar 2023.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Majalisar Wakilai Ta Gayyaci CBN Da Bankuna Kan Cire Wa Kwastomomi Kudi Ba Dalili October 18, 2025 Labarai Tawagar Bankin Duniya Ta Gana Da Gwamnan Katsina Kan Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira Muhallinsu October 17, 2025 Labarai Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja October 17, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki

Baba-Ahmed, ya bayyana cewa, abin da danginsa suka fuskanta a hannun masu garkuwa da mutane a bara ya tabbatar masa da cewa rashin tsaro a yanzu yana da nasaba da siyasa.

Ya kuma danganta kisan jama’ar da aka yi wa mabiya Shi’a a Zariya a shekarar 2015 da wani shiri na gwamnati don murƙushe masu sukarsu a wancan lokaci.

Ya jaddada cewa El-Rufai da jam’iyyar APC ba za su iya tserewa daga alhakin halin da Nijeriya ke ciki na rashin tsaro ba.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato October 16, 2025 Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October 16, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ya Ƙara Raguwa Zuwa Kashi 18.02% October 15, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnan Katsina Ya Bukaci Al’umma Su Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro
  • Majalisar Wakilai Ta Gayyaci CBN Da Bankuna Kan Cire Wa Kwastomomi Kudi Ba Dalili
  • Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA
  • Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja
  • Zan Tabbatar Ana Tafiyar Da Ayyuka A Tashoshin Jiragen Ruwa A Afrika Ta Yamma —Dantsoho
  • Taron Malamai Ya Nemi Haɗin Kai Domin Magance Rashin Tsaro, Talauci Da Rarrabuwa A Arewa
  • ’Yan sanda sun kama gungun masu fashi a kan hanyar Katsina zuwa Kano
  • Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki
  • Kafafen Sada Zumunta Na Zamani Suna Taimakawa Wajen Ta’azzara Matsalar Tsaro A Arewa – Yari