Aminiya:
2025-10-20@10:20:16 GMT

Nnamdi Kanu: Masu zanga-zanga sun yi watsi da gargaɗin ’yan sanda

Published: 20th, October 2025 GMT

’Yan sanda da jami’an tsaron farin kaya (DSS) sun shiga shirin ko-ta-kwana a birnin Abuja bayan masu zanga-zangar neman a saki shugaban ’yan awaren Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, sun yi watsi haramcin kotu kan yin hakan a kusa da Fadar Shugaban Ƙasa.

An shirya zanga-zangar ce ƙarƙashin jagorancin tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma mai fafutukar #RevolutionNow, Omoyele Sowore, domin matsa wa gwamnati lamba ta saki Kanu, wanda ke tsare tun shekarar 2021, kan zargin ta’addanci da cin amanar ƙasa.

Shaidu sun bayyana cewa an fara sanya shingayen bincike a wasu manyan hanyoyi da ke kaiwa Majalisar Dokoki ta Ƙasa, hedkwatar rundunar ’yan sanda, dandalin Eagle Square da Kotun Ɗaukaka Ƙara tun ranar Lahadi.

Nnamdi Kanu, wanda ke fuskantar tuhumar ta’addanci da cin amanar ƙasa, an fara kama shi a 2015, aka ba shi beli a 2017, kafin ya tsere bayan harin da sojoji suka kai gidansa a Abia.

Juyin mulki: Ana zargin tsohon gwamnan da ɗaukar nauyin sojojin Najeriya NAJERIYA A YAU: Shin Ya Kamata A Saki Shugaban IPOB Nnamdi Kanu?

Duk da cewa kotuna da dama sun bayar da umarnin a sake shi, Gwamnatin Tarayya ta ƙi bin hukuncin, abin da ke haifar da ƙarin fushi da nuna rashin jin daɗi daga jama’a.

Da yake jawabi kafin zanga-zangar, Sowore ya ce za su ci gaba da tafiyar da shirin kamar yadda aka tsara, yana mai jaddada cewa ’yan Najeriya na da cikakken ’yancin yin zanga-zanga cikin lumana.

“Tsare Nnamdi Kanu ba bisa doka ba ne, kuma abin kunya ne ga ƙasa,” in ji Sowore. “Kotun Ɗaukaka Ƙara ta wanke shi tun 2022, amma gwamnati ta ƙi bin hukuncin.”

Ya kuma roƙi sabon Kwamishinan ’Yan Sanda na Abuja da kada ya yi amfani da ƙarfi wajen tarwatsa masu zanga-zangar.

“Duk wani jami’i da ya ci zarafin masu zanga-zanga za a ɗauki mataki a kansa. Lokaci ya wuce da ake danniya da take haƙƙin jama’a,” in ji Sowore.

Sai dai Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya umurci jami’ansa su tabbatar da bin umarnin kotun tarayya da ta hana gudanar da zanga-zanga a kusa da Fadar Shugaban Ƙasa da wasu wurare masu muhimmanci a Abuja.

“Rundunar ’yan sanda za ta ci gaba da tabbatar da doka da oda bisa tsarin mulki,” in ji mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin.

“Duk wanda ya karya doka ko ya tayar da hankalin jama’a za a kama shi kuma a gurfanar da shi.”

A cewar ’yan sanda, matakin na nufin kare tsaron ƙasa da hana tashin hankali a muhimman wuraren gwamnati.

A nasa bangaren, masanin harkokin tsaro kuma shugaban cibiyar RULAAC, Mista Okechukwu Nwanguma, ya gargaɗi gwamnati da ta guji amfani da ƙarfi wajen murƙushe masu fafutuka, yana cewa hakan na iya tayar da ƙarin fitina.

“Kungiyar IPOB ta samo asali ne daga jin an ware su da rashin adalci,” in ji shi. “Idan gwamnati ta saki Kanu ta hanyar tattaunawa da bin doka, hakan zai taimaka wajen kawo zaman lafiya a kudu maso gabas.”

Ya kuma bukaci gwamnati ta rage amfani da ƙarfin sojoji a yankin, ta ƙarfafa ’yan sanda na al’umma, tare da magance matsalolin rashin aiki, talauci da jin wariya.

A cewarsa, lamarin Nnamdi Kanu gwaji ne ga gwamnatin Najeriya wajen tabbatar da adalci, hadin kai da mutunta dokar ƙasa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda zanga zangar

এছাড়াও পড়ুন:

Akwai Bukatar Al’umma Ta San Aikin Da Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFUND) Ya Yi  – Masari

 

Shin menene makasudin shirya irin wannan taro na masu ruwa da tsaki akan sha’anin ilimi da aka gudanar a yau?

Makasudin wannan taro shi ne a fadakar da mutane ayyukan wannan hukuma ta TETFUND da take yi, sannan kuma a yi magana da wadanda suka fi amfana da shi wannan tsari na TETFUND. Kamar jami’ai da makarantu da kuma dalibai sannan kuma a karbi shawarwari ga jama’a akan yadda za a bunkasa wannan aikin na hukumar tallafawa manyan makarantu na gaba da Sakandire a Nijeriya.

Wannan shi ne makasudi kuma na farko da ake san a jawo al’umma a ciki su dan abinda ake yi da yadda ake kashe kudaden da kuma yadda ake tarawa da makasudin tara su da makarantun da ake ba kudaden da kuma su makarantu yadda suke amfani da kudin

 

Shin kamar bangarori nawa ne suka halarci wannan taro na masu ruwa da tsaki a wannan hukuma ta asusun TETFUND?

Aminu Bello Masari: Na farko akwai bangarorin makarantu da Dalibai da ‘yan jarida da masu bukata ta musamman da kungiyoyin Malaman jami’o’i wata ASUU da da COUSU da duk masu ruwa da tsaki akan harkar ilmin gaba da Sakandire da kungiyoyin farar hula duk sun halarci wannan taro, bayan jami’an gwamnati wadanda suka zo daga fanni-fanni da tsofaffin shugabanni da majalisar tarayya da suke da hakkin kudaden da ake kashewa baki daya.

 

Jama’a da dama sun yi magana akan zama wasu sun mika kokon barar su akan ilmin gaba da Sakandire wani mataki zaku dauka a kan haka?

Daman ma’anar wancan zama shi ne domin a samu karin shawarwari daga al’umma da masana ta yadda za a cigaba da lissafin kasafin kudi na shekarar 2026, samun wadannan shawarwari za mu zauna mu kalle su, mu duba wadanda za su iya yiyuwa bana, wasu kuma sai an tura gaba, amma dai za a yi wani abu akan shawarwarin da aka samu insha’Allahu.

 

Masu bukata ta musamman sun samu wakilci kuma har sun mika bukatun su, me zaka ce game da haka?

To, na farko dai su masu bukata ta musamman darkatan da ke kula da gine-gine ya ce to yanzu dole ne duk ginin da za a yi dai an tabbatar da yana da tsari na kula da masu bukata ta musamman. Kuma sun kawo bukatar suna san a yi masu wani gurbi a ofishin shi sakatare na hukumar tallafawa manyan makarantun gaba da Sakandire, wannan kuma wani abu ne da sai mun zauna wajen taro zamu kalli abubuwan sannan abinda ke yiyuwa kuma shi za a yi.

 

A takaice me kake son cimmawa na ganin an ciyar da wannan hukuma ta TETFUND gaba?

Ai babban al’amari shi ne, a sanya mutane a cikin hidimar su san abinda ake yi, kuma su ba da shawarwari yadda za a kara bunkasa abin da ita wannan ma’aikata take yi, kudi ake amsa masu yawa kuma wajibi ne a gayawa jama’a yadda ake sarrafa wadannan kudaden a dukkan jami’o’in gwamnatin tarayya kusan 250 banda kwalejojin da sauran su ba wanda bai amfana da wadannan kudadai duk shekara.

 

Zuwa yanzu an kashe nawa a wannan hukuma mai tallafa wa manyan makarantun gaba da Sakandire a Nijeriya?

Yanzu abin da za mu iya cewa shi ne mun yi kasafin kudi, wanda zuwa yanzu an baiwa su makarantun daunin su na kaso hamsin (%50) bisa dari wanda yanzu lissafin da aka yi ya wuce biliyan 500 wanda aka ba su Makarantun a hannun su, to kuma za su kawo yadda za su kashe kudaden, sannan sauran an yi aikin lafiya da su wanda yanzu haka an fada a wajen taron da kuma aikin wuta da aikin tsaro duk wadannan wurare ne da aka sanya kudi da ayyuka na musamman.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tattaunawa Abba Ya Dace Ya Zama Gwamnan Kano Na Har Abada Ba Shekaru 8 Kaɗai Ba – Arch Ali Hassan June 23, 2025 Tattaunawa Nijeriya Na Da Karfin Tattalin Arzikin Sarrafa Kayan Dandanon Da Muke Bukata A Cikin Gida – Yahaya Yakubu May 24, 2025 Tattaunawa Ma’aikatar Kasuwanci Da Zuba Jari Ta Gudanar Da Bikin Makon Abokan Cinikayya October 18, 2024

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja
  • Jami’an tsaro sun buɗe wa masu zanga-zangar Nnamdi Kanu wuta a Abuja
  • NAJERIYA A YAU: Shin Ya Kamata A Saki Shugaban IPOB Nnamdi Kanu?
  • Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu
  • Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU
  • Matasa sun yi zanga-zanga kan yunwa a Adamawa
  • Akwai Bukatar Al’umma Ta San Aikin Da Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFUND) Ya Yi  – Masari
  • Ba mu ji dadin yi wa mahaifinmu afuwa tare da riƙaƙƙun masu laifi ba – Iyalan Herbert Macaulay
  • Batun Yin Afuwa Ga ‘Yan Yankin Ogoni Huɗu