Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, wanda ake zargin wanda aka ce shi ne Shugaban kungiyar ‘yan acaɓa reshen Ejiba, ya amsa cewa, ya siyo ƙwayoyin ne a wani shagon sayar da magunguna da ke Egbe domin kai wa abokan hulɗar sa da ke cikin dajin.

 

Babban sakataren yaɗa labarai na shugaban karamar hukumar Yagba ta yamma, Adeyemi Babarinde Sunday, ya ce an kuma samu wanda ake zargin da kuɗi har ₦600,000, wanda ake zargin kudaden hada-hadar ta’addanci ne.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza October 19, 2025 Labarai Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani October 19, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi October 19, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a Yobe 

Gwamnatin Yobe ta bayyana cewa aƙalla mutane 9,854 ne ke ɗauke da cutar AIDS a jihar, kuma dukkaninsu na karɓar maganin ceton rai.

Hukumar ta tabbatar da cewa waɗannan marasa lafiya suna rayuwa cikin ƙoshin lafiya, tare da rage yiwuwar yaɗa cutar ga wasu.

Babban Daraktan Hukumar Kula da Cutar AIDS ta Jihar Yobe (YOSACA), Dakta Jibril Adamu Damazai, ne ya bayyana cewa Yobe na da mafi ƙarancin adadin masu ɗauke da cutar a ƙasar nan da kashi 0.4%, inda ya danganta hakan da dabarun yaƙi da cutar da ake aiwatarwa a jihar.

“Ba mu tsaya a kan wannan nasara ba, muna ƙara ƙoƙari don rage yawan kamuwa da cutar,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta kashe sama da Naira miliyan 120 wajen sayen kayan gwaji, abin da ya bai wa ƙungiyoyi damar gano mutanen da ba a san suna ɗauke da cutar ba a cikin al’umma, domin a ba su magani.

A cewarsa, Yobe na kan gaba wajen daidaita dabarun yaƙi da cutar AIDS, musamman ganin yadda ake samun sauye-sauye a kuɗaɗen da ake kashewa a duniya.

Dakta Damazai ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta fara shirye-shiryen samar da magungunan ƙwayar cutar HIV a cikin gida.

Ya yaba da jajircewar gwamna Mai Mala Buni, wanda ya ƙara kuɗaɗen da ake bai wa hukumar kula da cutar AIDS da kashi 400%, tare da samar da katafaren ofis na dindindin ga hukumar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a Yobe
  • Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokinta
  • Rikicin Kungiyoyin Asiri Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Matashi A Jihar Kwara
  • Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a Yobe 
  • Jagoran ‘Yan Democrat a Majalisar Dattawa: Trump Ba Shi da Ikon Kaddamar da Yaki Kan Venezuela
  • An kama ’yan bindiga 4 a Kano
  • MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar
  • ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Garin Eruka Na Jihar Kwara
  • Gwamnatin Kano Ta Kara Jaddada Dokar Haramcin Yin Haya da Babur a Jihar
  • ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa  masu ibada a Kogi