Juyin mulki: Ana zargin tsohon gwamnan da ɗaukar nauyin sojojin Najeriya
Published: 20th, October 2025 GMT
Hukumar Leƙen Asirin Soji ta Najeriya (DIA) tana gudanar da bincike kan wani tsohon gwamna bisa zargin sa da ɗaukar nauyin sojoji da nufin yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu juyin mulki.
Majiyoyin Aminiya sun bayyana cewa akwai zargi mai karfi cewa tsohon gwamnan, wanda ɗan asalin yankin Kudu ne kuma tsohon babban jami’in gwamnati a ɓangaren albarkatun mai da iskar gas ne, ya ɗauki nauyin yunƙurin juyin mulkin, wanda da aka shirya aiwatarwa a ranar 25 ga watan Oktoban nan da muke ciki.
A ƙarshen mako ne kafofin watsa labarai na Shahara Reporters da Premium Times suka ruwaito cewa wasu hafsoshin soji 16, —waɗanda Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta ce sun shiga hannu saboda aikata abubuwan da saɓa ƙa’idar aiki— an tsare su ne saboda zargin su da yunƙurin kifar da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Daga cikin sojojin da aka kama akwai wani mai muƙamin Birgediya-Janar da wani Kanar da wasu na ƙasa da su da ke Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro (ONSA).
NAJERIYA A YAU: Shin Ya Kamata A Saki Shugaban IPOB Nnamdi Kanu? Magidanci na neman shawarar ’yan sanda kan ƙara aure a KanoMajiyar Aminiya ta tabbatar da cewa akwai ƙamshin gaskiya a rahoton zargin yunƙurin juyin mulkin.
Majiyar ta ce, “Gaskiya ne. Akwai hannun fararen hula, ciki har da wani tsohon gwamna, kuma ana bincike domin gano irin rawar da suka taka a ciki. A halin yanzu, sojoji 16 da ake zargi suna tsare.
“Tsohon gwamnan da ke ake zargin tsohon mai babban muƙami ne a ɓangaren albarkatun mai da iskar gas, amma ba a riga an kai ga tabbatar da sa hannunsa a ciki ba.”
Wata majiyar kuma ta shaida mana cewa binciken na ƙoƙarin gano irin alaƙar da kuma tattunawar da ke tsakanin tsohon gwamnan da sojojin da aka kama.
Ta ƙara da cewa akwai yiwuwar za a gayyaci tsohon gwamnan domin amsa tambayoyi idan har aka samu ƙwararan dalilai game da alaƙarsa da sojojin da ake zargi da neman kifar da gwamnati.
Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar Leƙen Asirin Soji ce take gudanar da binciken, tare da wakilai daga rundunonin sojin ƙasa da sojin sama da kuma Sojin Ruwa ta Najeriya.
“Mambobin kwamitin binciken sun haɗa da manya-manyan hafsoshin soji, bisa jagorancin wani mai muƙamin Manjo-Janar. An tsananta sirranta jerin sunayen waɗanda ake binciken.”
Manyan waɗanda ake zargiMajiyoyinmu sun bayyana cewa Manjo-Janar ɗin da ke jagorantar binciken ɗan asalin Jihar Neja ne.
“Akwai wani Kanar ɗan asalin wani babban gida daga Jihar Nasarawa. Mahaifinsa basarake ne kuma ɗan uwan tsohon Gwamnan Jihar, Umar Al-Makura,” in ji majiyar.
Binciken da muka gudanar a garin Lafia, hedikwatar Jihar Nasarawa, ya gano cewa zuri’ar Al-Makura suna cikin damuwa.
Ɗaya daga cikinsu da ya shaida wa wakilinmu a ranar Lahadi da dare, ya ce, wanda ake zargin “Kawuna ne. Gaba ɗaya danginmu sun shiga damuwa. Ni kaina ina cikin tashin hankali, … Haka ma matar hafsan sojin. Addu’armu dai ita ce, Allah Ya sa kada a kama su da laifin abin da ake zargi.”
Ƙarin sojoji sun shiga SojojiBinciken da muka gudanar ya gano cewa an ƙara jama wasu sojojin domin amsa tambayoyi kan alaƙarsu da zargin yunƙurin juyin mulkin.
“Baya ga tsohon gwamnan akwai wasu manyan ’yan siyasa daga yankin Kudu da kuma Arewa da bibiyar duk wani motsinsu,” in ji majiyarmu.
Ba mu ambaci juyin ba — SojojiA ranar Asabar Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta fitar da wata sanarwa ta hannun Daraktan Yaɗa Labaranta, Birgediya-Janar Tukur Gusau, da ke ƙaryata rahotanni da ke cewa zargin yunkurin kifar da gwamnati ne ya sa aka dakatar da bikin zagayowar ranar samun ’yancin cikar Najeriya karo na 65 a ranar 1 ga watan nan na Oktoba.
Manjo-Janar Tukur Gusau ya buƙaci jama’a da su yi watsi da labarin, yana mai bayyana masu yaɗa shi a matsayin maƙarya kuma marasa kishin ƙasa.
Sanarwar mai taken ‘DHQ ba ta ambaci juyin mulki ba, ta ce, “DHQ ta lura da wani labarin ƙarya da wasu kafofin watsa labarai na intanet suka wallafa da ke riya cewa an soke bukukuwan zagayowar ranar cikar Najeriya shekara 65 da samun ’yanci ne saboda zargin yunƙurin juyin mulki.
“Labaran suna nuni ga wata sanarwar DHQ na baya-bayan nan game da tsare wasu hafsoshin soji 16 da ake bincikar su kan saɓa kai’idar.
“Rundunar Tsaron Najeriya na sanar da al’umma cewa abin da kafofin watsa labaran suka wallafa ƙarya ce tsagwaronta, kuma an ƙirƙira ta ce domin sanya mutane cikin fargaba da rashin yarda da juna.
“An yanke shawarar dakatar da bikin ne domin ba wa Shugaban Ƙasa damar halartar wani muhimmin babban taro a ƙasar waje da kuma ba wa sojijojinmu damar ci gaba da ragargazar a ayyukan ’yan ta’adda da ’yan bindiga da ke addabar ƙasar .
“Hedikwatar Tsaro tana kuma tabbatar wa ’yan Najeriya cewa binciken da ake yi kan hafsoshin sojan guda 16, abu ne na yau da kullum a gidan soja, domin tabbatar da ɗa’a da kuma ƙwarewa a kowane mataki.
“An riga an kafa kwamitin bincike yadda ya kamata kuma nan gaba za a sanar da al’umma sakamakon binciken
“DHQ na kira ga ’yan ƙasa masu kishin zaman lafiya da su taimaka wa jami’an da duk wata gudunmawa d ta dace. Gwamnatin Tarayya da ɓangaren Majalisa da ɓangaren Shari’a suna aiki kafaɗa-da-kafaɗa domin tabbatar da tsaro da ci-gaba da kuma walwalar al’ummar Najeriya da kuma ɗorawar tsarin dimokuraɗiyya.
“Hedikwatar tana kuma kira ga jama’a da su yi watsi da labaran ƙarya da maƙiyan wannan ƙasa suke yaɗawa. Rundunar Tsaro ta Najeriya ta tsaya kai da fata wajen tabbatar da biyayyarta da kuma kare kundin tsarin mulkin Najeriya a ƙarƙashin jagorancin Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR.”
Neman a bayyana su da ainihin zarginTun bayan ɓullar labarin zargin yunƙurin kifar da gwamnati ’yan Najeriya ke ta kira ga rundunar sojin ƙasar ta bayyana sunayen waɗanda ake zargin da ake tsare.
’Yan Najeriya a kafofin sada zumunta sun buƙaci hukumomin soji su bayyana haƙiƙanin laifin da ake zargin hafsoshinta 16 da ta ce tana tsare da su.
Adelabi Gbenga, ya wallafa a Facebook cewa: “Zuwa ga rundunar soji, muna buƙatar ku sanar da ’yan Najeriya haƙiƙanin laifin hafsoshi 16 kafin kunga,a da su. Ruwa ba ya tsami banza.”
“Saɓa wa ƙa’idar aiki? Ku gaya mana ne suka yi takamaimai. Kar ku da mu a cikin duhu. Kuma da kuɗaɗen harajinmu ake biyan ku albashi,” i. Ji Edidiong Jackson a kafar X.
Zakaria Olambeloye ya wallafa a Facebook cewa, “Su sojojin nan ko… Shi ya sa ba na son shiga aikin. Tun da mutane sun aikata laifi, ku fito ku faɗi irin laifin kuma shi ne wahala? Ku gaya mana su waye su, kuma wane laifi suka aikata.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ɗaukar nauyin juyin mulki Kifar da Gwamnati Tsaro tsohon gwamna zargi kifar da gwamnati zargin yunƙurin tsohon gwamnan da ake zargi yan Najeriya a ɓangaren tabbatar da ta Najeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Har yanzu ban bar yin waqa ba-Yusuf Lazio
Har yanzu ban bar yin waqa ba-Yusuf Lazio
Daga Musa Kutama, Kalaba
Yusuf Muhammad Abdullahi da aka fi sani da Yusuf Lazio, fitaccen jarumi ne a Masana’antar Finafinan Hausa, wato Kannywood. Jarumin ya yi shura a fim xin Na-Ladidi, inda ya ce, haxa waqa da fim a lokaci xaya, a wurinsa ba wani abu ba ne, hasali ma mawaqi ne shi kafin ya fara fitowa cikin fim.
Ga yadda hirar ta kasance:
Gabatar da kanka ?
Sunana Yusuf Mohammad Abdullahi ana kira na da Yusuf Lazio.
Dama can kana da alaqa da Lazio ne ko kuwa kulob xin ne ake kiran ka da shi?
A’a sunan ya samo asali ne daga goya wa qungiyar wasan qwallon qafa ta Lazio baya da nake yi.
An lura a ‘yan kwanakin nan ka xauke qafa a harkar fim, ka fi karkata a kan waqa. Me za ka ce a nan?
Ba xauke qafa na yi ba, ina nan ina fitowa a wani fim mai suna Gidan Sarauta sannan kuma yanzu haka ina aiki ma a wani fim xin daban.
Ga alama ka fi mayar da hankali wajen yin waqa a kan fim, wane qarin bayani za kayi a nan?
Har yanzu ina yin waqa kuma ina yin fim, domin waqa ce ta fara fito da ni. Sannan kafin ma in fara fitowa a fim da ma ni waqa nake yi sannan na dawo yin fim.
Kana ganin za ka iya haxa taura biyu?
Eh, ba za su yi wahala ba, tunda duk biyun suna da alaqa.
Tsakanin yin fim da kuma waqa wanne ya fi wani wahala?
Gaskiya wannan wata harka ce da zan ce ma kamar ado ne. Ita waqa ana yin ta daban, abu ne na basira. Sannan fim ma abu ne na sha’awa, don haka haxa biyun bai ba ni wahala ba kwatakwata.
Ka lura da irin sauyi da ci gaban da ake samu ta harkar fim da kayan aiki na zamani ya kawo?
Eh, to dama ai kasan duk mai sana’a duk wacce ta fi kawo maka riba ai ita za ka fi mayar da hankali a kai. Cikin ikon Allah mun samu sauyi mai yawa, mun samu nasara a kan haka, wanda a da qaramin jarumi ba zai iya yin fim nasa na kansa ba. Amma yanzu zai iya fitowa, ya yi fim nasa, ya bayar da umarni. Hakan ya sa na yi matuqar farin ciki da wannan ci gaba da aka samu.
Da ka ce an samu ci gaba ta wane vangare sai ka yi bayani?
Yanzu idan ka duba, zan iya yin fim ba darakta, ka ga zan iya yi, in sanya a Youtube, mutane su kalla. Ka ga wannan ba qaramin ci gaba ba ne aka samu a fannin yin fim. Sannan kuma yanzu ba sai ka naxi fim a kaset ko a wani CD ba, kana iya shiga Youtube ka sa, a kalla.
Ko kwalliya na biyan kuxin sabulu a sanya finafinanku ta kafar sada zumunta. Kuxaxen da kuka sanya aka yi aikin ko suna fitowa hala har ma a sa rai za a samun riba?
Qwarai ana samun nasara a kan haka, akwai riba.
Shin xora waqoqi ko fim a YouTube kana ganin zai magance satar fasahar waqa ko fim?
Ka san kowane mai sana’a yana yi don riba ce. Alhamdulillahi, wannan sabuwar dabara nasara ce a cikin sana’armu, duk da yake ba za a rasa samun qananan abubuwa da za su riqa tasowa ba.
Ya alaqa take tsakaninku da Hukimar Tace Finafinai lura da cewa, yanzu ana sanya fim a YouTube mai yiwuwa ba tare da an kai mata, ta tantance fim xin ba?
Gaskiya ni ban tava karo da su ba, domin ni duk abin da nake yi ina tabbatar da cewa na kare abin da addinina yake so na kuma kiyaye abin da ba ya so. Ka ga ba zan shiga wani layi ba da na san abin zai kawo min zubar da mutuncina.
Bari mu koma kan waqa, ka ce ka haxa biyu fim da waqa wane vangare kake yi wa waqa ‘ya siyasa ko masu kuxi ko iya ta fim ka tsaya?
Gaskiya na fi mayar da hankali a waqoqin gambara, wato Hiphop na Hausa. Akwai albom da nake aiki a kansa na wasu sababbin waqoqin da na yi wanda na gambara ne gaba xaya.
Kuma kwalliya na biyan kuxin sabulu ?
Alhamdulillahi.
Wacce shawara kake xauke da ita ga masu tasowa don su mayar da hankali a kan abin da suka sa gaba?
Shawarata ita ce su mayar da hankali su tabbatar sun cim ma burinsu.
Tauraron Finanfinan Indiya na Bollywood, Dharmendra ya rasu yana da shekara 89
Dharmendra ya rasu ranar Litinin a wani asibiti a birnin Mumbai na Indiya bayan gajeruwar rashin lafiya.
Firayim Ministan Indiya, Narendra Modi ya yi ta’aziyyar jarumin a cikin, yana mai cewa rasuwarsa “ta kawo babban givi a Masana’antar Fim ta Indiya”.
An haifi tsohon tauraron Bollywood a ranar 8 ga Disambar 1935 a qauyen Nasrali da ke Gundumar Ludhiana ta Punjab.
Mahaifinsa malamin makaranta ne, kuma shi ya sanya masa suna Dharam Singh Deol.
A lokacin rayuwarsa, Dharmendra ya bayyana kansa a matsayin “mutum mai sauqin kai”, wanda ya sami qauna da aminci daga miliyoyin magoya bayansa.
Ya taka rawar gani da dama, amma an fi sanin sa da Veeru, a cikin fim xin Sholay na 1975. Duk da haka, Dharmendra ya fito a finafinai sama da 300 da waqoqi da yawa,waxanda suka ja hankalin masu kallo tsawon shekaru da yawa.
A wani lokaci, jarumin, wanda aka tava yi masa laqabi da “Asalin Mutumin Bollywood” da “Garam wato mai zafin nama”, ya shiga jerin “mazaje mafi kyau” a duniya a lokacin da ya kai qololuwar nasararsa; kuma akasarin magoya bayansa mata ne, inda ta kai har suna kwana da hotunansa a qarqashin matashin kansu.
Ya bar mata biyu Prakash Kaur da Hema Malini da ‘ya’ya shida, Sunny Deol da Bobby Deol da Esha Deol da Ahana Deol da Vijeta da Ajeeta Deol da kuma jikoki goma sha uku.