Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bi sahun dan rajin kare hakkin dan adam kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, wajen yin kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sakin jagoran kungiyar Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu.

 

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na D, Atiku, ya bayyana ci gaba da tsare Kanu a matsayin “rashin girmama bin doka a Nijeriya.

 

Kanu dai, na fuskantar tuhumar ta’addanci ne da cin amanar kasa da kuma nuna tunzura a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, wanda kuma a lokuta da dama yake musanta hakan. Har ila yau, ya kasance a tsare tsawon shekaru duk da hukuncin da kotu ta yanke na bayar da umarnin a sake shi.

 

Atiku, tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ya bayyana cikakken goyon bayansa da fafutukar da Sowore ke yi na ga nin an saki Kanu.

 

Da yake yin jawabi a wajen taron, Kwamared Gamji ya bayyana cewa; “Mun zo nan ne, domin mu nuna fushinmu da rashin amincwar mu da kuma nuna wa duniya cewa, ba ma tare da ‘yan siyasa masu neman mulki ido rufe a Nijeriya, wadanda ke son yin amfani da tsare Nnamdi Kanu wajen tayar da zaune tsaye a kasar.

 

“Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma mamallakin gidan jaridar Sahara Reporter, Mista Omoleye Sowore, da babanmu, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, na shirin shirya wani gangamin taro, domin sakin Nnamdi Kanu.

 

Ya kara da cewa, mun ji wannan sanarwa tasu, sannan kuma ba ma tare da su. “Saboda son rai irin naku, kuna so ku yi amfani da jinin matasan Nijeriya, wajen cimma burinku,” in ji Gamji.

 

“Babban kuskuren da za su tafkawa shi ne, ranar da za su fito, ita ce ranar da matasa sama da miliyan 63, wadanda jiga-jigan matasan Arewa ne; su ma za su fito tare da rokon Shugaba Ahmed Bola Tinubu, da ya ci gaba da gudanar da kyawawan ayyukan da sanya a gaba.

 

Kwamared Gamji ya kara da cewa, “Za mu mamaye dukkannin titunan Abuja, daga ranakun 20, 21 zuwa 23 ga watan Oktoba, domin nuna goyon bayanmu ga Shugaba Tinubu”.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci October 17, 2025 Labarai ‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci – Shettima  October 17, 2025 Labarai Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma October 17, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An harbe manomi saboda rikici kan filin kiwo a Borno

Rikici kan filin kiwo tsakanin wani makiyayi da wani manomi ya yi sanadin mutuwar wani manomi mai shekaru 32 a kauyen Muva da ke cikin karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.  

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, a ranar 2 ga watan Disamba, 2025, da misalin karfe 4:00 na yamma, Alhaji Usman, wanda ke kiwon shanu, ya samu rashin jituwa da Jauro Ishaya mai shekaru 43, kan rikicin filin kiwo.

A cewar majiyar, yayin takaddamar ne aka zargi Jauro Ishaya da harba bindigar gida wadda ta sami Alhaji Usman a ciki, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.

An garzaya da wanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Askira, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa nan take.

Rundunar ’yan sandan jihar ta ce ta kama wanda ake zargi, kuma tana ci gaba da kokarin kwato bindigar da aka yi amfani da ita a lamarin.

Majiyoyi sun kara da cewa, sashen binciken manyan laifuka (CID) na rundunar ’yan sanda a Maiduguri ya fara gudanar da bincike kan lamarin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Zama Zakaran  Duniya A Wasan “Taekwondo” Na Masu Shekaru Kasa Da 21
  • Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno
  • Yan Sanda Sun Kama Muhuyi Magaji, Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci a Kano
  • Limamin Tehran:  Idan Abokan Gaba Su Ka  Sake Yin Kuskure Akan Iran Za Su Sake Cin Kasa
  • An harbe manomi saboda rikici kan filin kiwo a Borno
  • Ziyarar Putin a Indiya alama ce da ke nuna cewa New Delhi na yin watsi da gargadin Trump?
  • An kashe matashi yayin rikici a wajen raɗin suna a Bauchi
  • Matashi ya rasu yayin rikici a wajen radin suna a Bauchi
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar da Wutar Lantarki a Yankunan Kananan Hukumomin Jihar
  • Tinubu ya naɗa tsohon kantoman Ribas da Dambazau a matsayin Jakadun Najeriya