Kalmar demokuradiyya kalma ce da jagoran ‘yan awaren Taiwan Lai Ching-te ke yawan ambata, amma aikin da ya yi bai bi hanyar demokuradiyya ba. A baya-bayan nan, Lai Ching-te ya gabatar da wani shirin neman ‘yancin kan Taiwan, har ma ya ce wai Taiwan wata kasar demokuradiyya ce mai mulkin kanta. Lai Ching-te ya kan yin amfani da demokuradiyya don ya cuci jama’ar yankin Taiwan da sauran kasashen duniya, amma a wannan karo kowa ya san yunkurinsa na neman mulki irin na kama karya ta hanyar demokuradiyya.

Ya kamata a yi amfani da demokuradiyya don tabbatar da hakkin jama’a, a maimakon kawo illa ga hakkin jama’a. Jama’ar yankin Taiwan suna neman zaman lafiya, da samun ci gaba, da yin mu’amala, da kuma yin hadin gwiwa. Bisa binciken shekara kan huldar dake tsakanin bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan da kafofin watsa labaru na yankin Taiwan suka bayar a shekarar 2024, kashi 87 cikin dari na jama’ar yankin Taiwan sun yi tsammanin cewa, akwai bukatar kiyaye yin mu’amala a tsakanin bangarorin biyu na mashigin tekun Taiwan. Amma tun lokacin da mahukuntan jagoran ‘yan awaren Taiwan Lai Ching-te suka kama aiki a watan Mayu na shekarar bara, sun yi amfani da hanyoyin ayyukan gwamnati da dokoki da kafofin watsa labaru don hana yin mu’amala a tsakanin bangarorin biyu na mashigin tekun Taiwan.

Mahukuntan Lai Ching-te sun yi aika-aikar da ta janyo koma baya a tarihi da keta ‘yanci da hakkin dan Adam na jama’ar yankin Taiwan, kana tana son shigar da jama’ar cikin ayyukan ‘yan awaren Taiwan, da bayyana cewa wai yankin Taiwan muhimmin yanki ne da ke tabbatar da demokuradiyya a duniya. Yunkurinsa na neman ‘yancin kan Taiwan wanda ya keta bukatun jama’a da demokuradiyya ba zai samu nasara a tarihi ba. (Zainab Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: jama ar yankin Taiwan a ar yankin Taiwan da demokuradiyya

এছাড়াও পড়ুন:

Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya October 13, 2025 Manyan Labarai Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako October 13, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don  Halartar Taron Tsaro Na Aqaba October 12, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama mata da miji suna safarar makamai a Kaduna
  • Juyin mulki: Shugaba Rajeolina ya tsere daga ya rushe majalisa
  • Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi
  • Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba
  • Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano
  • Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano
  • Zaɓen Kamaru: Tchiroma Bakary na da kwarin gwiwa a yayin da ake jiran sakamako
  • Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta
  • Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan
  • Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22