Sojoji sun kashe ’yan bindiga 31, sun lalata sansaninsu a Katsina
Published: 16th, March 2025 GMT
Dakarun Sojin Najeriya sun kashe ’yan bindiga 31 tare da lalata sansaninsu a Jihar Katsina, yayin wasu hare-hare guda biyu da suka kai.
A farmaki na farko, dakarun Operation Fansan Yamma sun yi artabu da ’yan bindiga a garin Maigora da ke Ƙaramar Hukumar Faskari.
Abba ya mayar da filin Idi cibiyar harkokin addinin Musulunci Afirka ta Kudu ta yi martani kan korar jakadanta daga AmurkaDa farko, sojojin sun kashe ’yan bindiga biyar bayan sun kai farmaki garin.
Sai dai lokacin da suka sake haɗuwa don kai harin ramuwar gayya, sojojin sun sake kashe guda bakwai, ciki har da Dogo, wanda babban Kwamanda ne a cikinsu.
Haka kuma, sojojin sun ƙwace babura guda bakwai da ‘yan bindigar ke amfani da su.
A wani farmakin, rundunar sojojin sama ta yi luguden wuta a maboyar ’yan bindiga da ke dajin Unguwar Goga, Ruwan Godiya, a Ƙaramar Hukumar Faskari.
Sun lalata sansanin shugabannin ’yan bindiga biyu; Alhaji Gero da Alhaji Riga, inda suka kashe aƙalla mahara 19.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa sojojin Najeriya na ƙara ƙaimi wajen murƙushe ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma, tare da lalata sansaninsu.
Har ila yau, sojojin na ci gaba da sintiri ta sama da ƙasa don daƙile yunƙurin ’yan bindiga na sake hare-hare.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga dakaru hare hare yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Lukurawa Sun Kashe Mutane 15 a Sakkwato
Wasu ‘yan bindigar da ake zargi Lukurawa ne a wani sabon hari sun kashe mutane sama da 15 a Qaramar Hukumar Tangaza ta jihar Sakkwato, ranar Litinin da ta gabata.
Babban Jami’i a Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Qasa(Red Cross) reshen Sakkwato Alhaji Abubakar Ainu ya tabbatar wa Aminiya harin wanda ya yi matuqar tayar da hankalin mutanen yankin ganin an xauki dogon lokaci kafin kawo irin wannan hari mai muni.
Ainu ya ce, “jami’anmu na sa kai sun ziyarci qauyen Kwalajiya na mazabar Magoho a garin Tangaza domin jajantawa da kuma halartar sallah janaza ta muanen da ‘yan bindigar suka kashe sama da 15. Waxanda suka jikkata an kai su Asibitin Kashi na Wamakko da Asibitin Koyarwa ta Xanfodiyo da na Qwararru a birnin jiha domin karvar magani.”
Ya ce yankin na cikin wuraren da ke fama da matsalar tsaro ta varayin shanu da masu tayar da qayar baya.
“Wannan lamari baya da daxi ko kaxan, dubi yadda aka mayar da wasu mata zawarawa aka mayar da wasu yara marayu domin biyan wata buqata wadda addini bai yarda da ita ba, ina kira ga hukuma ta sake salon yaqar ‘yan bindiga da take yi,” in ji Ainu.
Wani mazauni qauyen Kwalajiya ya ce ‘yan bindigar Lukurawa sun zo a qauyen a daren Lahadi har zuwa Asuba ta ranar Litinin in da suka kashe wasu mutane a harin da suka kai, a lokacin da suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.
“Bayan sun kashe mana mutane sun tafi da dabbobi masu yawa, duk da mutanenmu sun yi qoqari amma yawan mutane da makaman da suke xauke da su ya sa suka fi qarfinmu. Har zuwa yanzu ba mu san adadin waxanda aka kai asibiti ba domin suna da yawa, sai dai waxanda suka rasu 15 muka yi wa Sallah.
“Muna kira ga jami’an tsaro su mayar da hankali wurin korar mana waxannan ‘yan bindigar don mu samu zaman lafiya a jiha baki xaya.”