Ma’aikatar Ilimin Amurka Na Shirin Korar Ma’aikata 1,300
Published: 16th, March 2025 GMT
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp.এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Gombe ya ƙaddamar da shirin tallafa wa karatun yara mata
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da shirin AGILE na tallafin karatun yara mata da tallafin gyaran makarantu, domin inganta ilimi a faɗin jihar.
A wajen bikin da aka gudanar a Otal ɗin Custodian, Gwamna Inuwa, wanda Mataimakinsa Dakta Manasseh Jatau, ya wakilta, ya ce gwamnati na da niyyar kawar da duk wani abin da ke hana yara mata zuwa makaranta.
’Yan sanda sun ƙwato miyagun ƙwayoyi a Gombe Ba mu ji dadin yi wa mahaifinmu afuwa tare da riƙaƙƙun masu laifi ba – Iyalan Herbert MacaulayYa ƙara da cewa: “Idan ka ilmantar da ’ya mace, ka ilmantar da al’umma gaba ɗaya; idan ka karfafe ta, ka karfafu zuri’a baki ɗaya.”
Gwamnan, ya gode wa Bankin Duniya, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, da Kwamitin AGILE saboda haɗin kansu wajen inganta ilimi a jihar.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tare da su domin ɗorewar shirin.
Kwamishiniyar Ilimi ta Jihar Gombe, Dokta Aishatu Umar Maigari, ta ce wannan shiri babban ci gaba ne wajen inganta makarantu da bunƙasa tsarin kula da su ta hannun SBMCs.
Ta buƙaci masu ruwa da tsaki su tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗaɗen tallafin yadda ya kamata.
A nata ɓangaren, Kodinetar Shirin AGILE, Dokta Amina Haruna Abdul, ta ce dubban yara mata za su amfana da tallafin domin rage matsin tattalin arziƙi da ke hana su karatu.
Ta kuma yaba da jajircewar gwamnatin jihar, wajen tallafa wa ilimi, inda ta ce hakan zai ƙara wa yara mata ƙwarin gwiwa su ci gaba da neman ilimi a faɗin jihar.