Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alhinin Rasuwar Edwin Clark
Published: 18th, February 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya tayi matukar alhinin rasuwar Dattijo kuma Tsohon Kwamishinan Yada Labarai na Tarayya, Cif Edwin Clark, wanda ya rasu yana da shekaru casa’in da bakwai.
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja.
Ya ce, Marigayi Cif Clark gwarzo ne mai kishin kasa, mai fafutukar tabbatar da adalci da gaskiya, kuma ginshiki ne a ci gaban dimokuradiyyar Najeriya.
Mohammed Idris, ya kara da cewa, Marigayi ya sadaukar da kansa wajen bautawa kasa a fannoni da dama, musamman a matsayin shi na ɗan siyasa da mai kishin kasa, wanda ya bar gagarumar alama a harkokin mulki, hadin kai, da ci gaban Najeriya.
“Fafutukarsa da hikimarsa da jajircewarsa wajen ci gaban kasa sun sa, ya zama murya mai matukar tasiri a siyasar Najeriya,” in ji Minista.
“Za a yi matukar rashin shawarwarinsa masu hikima da gudunmawarsa wajen gina kasa.”
“Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan Cif Clark, gwamnatin da al’ummar Jihar Delta, da dukkan ‘yan Najeriya da suka amfana da rayuwarsa mai albarka. Muna rokon Allah Ya jikansa, Ya kuma bai wa iyalansa da duk masu jimamin wannan rashi babban hakuri da karfin zuciya.”
Rel/Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Clark Gwamnatin Rasuwar Tarayya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
Daga Abdullahi Shettima
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna.
Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin kasuwanci daga Asiya, Fasifik, Turai da Afirka. Taken taron shi ne “Haɗin Gwiwa. Ƙarfafawa. Sauyi.”
A jawabinsa mai taken “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa,” Gwamna Uba Sani ya bayyana yadda Kaduna ke samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma da tallafawa jama’a. Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki, kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su cim ma nasara a rayuwarsu.
Haka kuma, ya halarci baje kolin birnin Dubai mai taken “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira da Tasirin Zamantakewa,” inda ya jaddada muhimmancin jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha wajen buɗe damarmaki ga al’umma.
A yayin taron, Gwamnan ya gudanar da ganawa ta musamman da Marwan Bin Galita, Darakta-Janar na birnin Dubai, inda suka tattauna batutuwan kirkirar makamashin sharar gida, kula da sharar zamani, da tsare-tsaren gine-ginen birane na zamani.
Duk ɓangarorin biyu sun amince da zurfafa haɗin kai a fannin fasaha da musayar ƙwarewa domin tallafawa sauyin tattalin arzikin Kaduna zuwa mai ɗorewa.
Gwamna Sani ya bayyana cewa halartar Kaduna a taron (APCS 2025) na nuna shirin jihar na shiga sahun gaba wajen yin haɗin kai, ƙirƙira da zama abin koyi a fannin ci gaba mai ɗorewa — a Najeriya da duniya baki ɗaya.
Karshe.