Aminiya:
2025-06-15@09:58:10 GMT

Hajji 2025: Kamfanin Saudiyya zai maka Najeriya a Kotun Duniya

Published: 18th, February 2025 GMT

Kula da walwalar maniyyatan Najeriya ya shiga tangal-tangal bayan wani kamfanin kula da alhazai na kasar Saudiyya ya yi barazanar maka Najeriya a Kotun Hukunta Manyan Laifuka na Duniya (ICC), kan saba yarjejeniyar kwangilar aikin Hajji.

Kamfanin Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi na kasar Saudiyya, wanda Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohin suka ba wa kwangilar kula da alhazan Najeriya a aikin Hajjin 2025, ne ya yi barazanar, yana mai zargin Najeriya da yaudarar sa.

Mashariq Al Dhahabiah Al-Mutawazi ya yi barazanar maka Najeriya a Kotun Duniya ne bisa zargin Hukumar NAHCON da karya yarjejeniyar da suka kulla kan aikin kula a alhazan, musamman a Mina da Filin Arfa.

A wata wasika da ya aike wa Shugaban Ofishin Aikin Hajjin Najeriya da ke birnin Makkah a kasar Saudiyya a ranar Litinin 17 ga watan nan na Fabrairu, 2025, kamfanin ya zargi NAHCON da saba yarjejeniyar da suka kulla cewa kanfaninsu ne kadai hukumar za ta wa kwangilar aikin a bana, musammana a Mina da Arafah.

NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar Dattijon Neja Delta Edwin Clark ya rasu

Daga nan sai ya ba wa hukumar kwana 20 ya koma kan sharudan yarjejeniyar da suka rattaba hannu a kai, idan ba haka ba ta maka hukumar a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC).

Binciken wakilinmu ya gano a ranar 17 ga watan Janairu ne kamfanin da NAHCON suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kula da alhazan Najeriya a Kasa Mai Tsarki.

Amam daga bisani Kungiyar Hukumomin Jin Dadin Alhazan Jihoi suka daga kara cewa Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman Saleh, ya yi gaban kansa wajen soke yarjejeniyar, kwanaki kadan kafin cikar wa’adin biyan kudi ga kamfanonin da kasashe suka ba wa aikin.

Farfesa Abdullahi Usman Saleh dai ya musanta yin gaban kansa wajen soke yarjejeniyar, yana mai cewa hukumomin Saudiyya ne suka yi.

Ana zargin NAHCON ta raba aikin gida biyu tsakanin Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi da kuma kamfanin Ikram Diyafa kafin cikar wa’adin ranar 14 ga watan Janairu da hukumomin Saudiyya suka sanya.

Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi na zargin NAHCON da ba shi aikin kula da alhazai 26,287, duk kuwa da cewa hukumar ta sanar cewa ta samu tantunan alhazai 52,544 da za su gudanar da aikin Hajjin, wanda hakan ke nufin hukumar ta ba wa daya kamfanin aikin kula da ragowar alhazai 26,257 ke nan.

Kamfanin ya bukaci zama na gaggawa da mahukuntan NAHCON kan lamarin domin yanke shawara kan mataki na gaba da za a dauka.

Wakilinmu ya yi iya kokarinsa domin samun martanin hukumar NAHCON a game da wannan dambarwa, amma abin ya faskara.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kotun Duniya kwangila Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi Najeriya yarjejeniya Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi

এছাড়াও পড়ুন:

 Iran Za Ta Kara Yawan Sanadarin Urani’um Da Take Tacewa A Wuri Na Sirri

A wani bayani na hadin gwiwa da hukumar makamashin Nukiliya ta Iran da kuma ma’aikatar harkokin wajen Iran su ka fitar, sun bayar da umarnin a bude wani wuri na daban na sirri domin ci gaba da tace sanadarin Urani’um, sannan kuma a maye gurbin bututu tace sanadarin mai  mataki na daya, da mai mataki na shida a cibiyar “Pardo.”

Bayanin dai ya zo ne a matsayin mayar da martani ga sanarwar da ta fito daga kwamitin alkalai na hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa akan Iran.

Bugu da kari, bayanin na Iran ya kuma ce; A kodayaushe jamhuriyar musulunci ta Iran tana aiki da nauyin da ya rataya a wuyanta, kuma har ya zuwa yanzu babu wani rahoto na hukumar wanda ya bayyana cewa; Iran ba ta aiki da ka’idojin hana yaduwar makaman Nukiliya.”

Haka nan kuma bayanin ya ambaci cewa; Tare da cewa Iran tana daukar rahoton da cewa na siyasa ne, wanda Amurka da kasashen turai suke amfani da hukumar a matsayin makami, ba tare da dogaro da wani dalili na ilimi ba.

Har ila yau Iran din ta zargi Amurka da kasashen na turai da wuce gona da iri wajen tsara rahoton da yake cin karo da rahoton da shugaban hukumar ta makamashin Nukiliya ya fitar, wanda bai sami wani abu mai  shiga duhu ba a cikin Shirin na Iran na zama lafiya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kula Da Kanki Bayan Haihuwa Abu Ne Muhimmi
  • Gwamnati Ta Yi Barazanar Matakai Masu Tsauri Kan Masu Fasa Bututun Mai
  • Wani Gidan Gona A Jihar Ogun Zai Fitar Da Tarwada Ta Kimanin Naira Biliyan Shida A 2025
  • Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi
  • Hajjin 2025: Yadda Alhazan Nijeriya 7 Suka Rasa Rayukansu A Saudi Arabiya
  • NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya
  • Aliko Dangote Ya Sauka Daga Shugabancin Kamfanin Sukarin Dangote
  • Babu wanda ya tsira daga hatsarin Jirgin Air India mai dauke da fasinjoji 242
  •  Iran Za Ta Kara Yawan Sanadarin Urani’um Da Take Tacewa A Wuri Na Sirri
  • Zamfara: APC Za Ta Maka PDP A Kotu Kan Zargin Matawalle Da Hannu A Satar Mutane