Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin sabon Shugaban INEC
Published: 17th, October 2025 GMT
Majalisar Dattawan ta Najeriya ta tabbatar da naɗin Farfesa Joash Amupitan, mai mukamin SAN, a matsayin sabon shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a yammacin ranar Alhamis.
Tabbatar da Farfesa Amupitan, ta kasance ta hanyar kuri’ar murya da ‘yan majalisar suka gudanar bayan kammala tantance shi tare da amsa tambayoyi daga mambobin majalisar na tsawon kusan sa’o’i biyu.
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ne ya gabatar da sunan Amupitan, don maye gurbin tsohon shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya sauka daga mukamin makonni biyu da suka gabata.
Amupitan, wanda ya samu rakiyar gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Ododo, da wasu jami’ai zuwa majalisar, ya gabatar da tarihin inda ya yi aiki kafin fara amsa tambayoyin ‘yan majalisar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Sudan Yana Ziyarar Aiki A Kasar Masar October 17, 2025 Lebanon: Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Hrin Wuce Gona Da Iri Na HKI October 17, 2025 WSJ: Amurka Tana Tara Rundunonin Yaki A Zagayen Kasar Venezuela October 17, 2025 Shugabannin Kasashen Amurka Da Rasha Za Su Hadu A Kasar Hungary October 17, 2025 Larijani ya isar da sakon Ayatullah Khamenei ga Putin a ziyarar da ya kai Rasha October 17, 2025 Madagaska : Ranar Juma’a za’a rantsar da Kanar Randrianirina October 16, 2025 Pezeshkian Ya Yi Gargadi Akan Makircin Makiya A Tsakanin Al’ummar Musulmi October 16, 2025 Euro-Med ta bukaci bangarori su shiga Gaza domin tattara bayanai kan kisan kiyashin Isra’ila October 16, 2025 Kenya : An dawo da gawar Raila Odinga gida October 16, 2025 Iran Ta Bukaci Kasashen Kungiyar NAM Su Hada Kai Don Fuskantar Rashin Bin Doka Da Oda A Duniya October 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Afirka Ta Kudu: An Kashe Mutane 11 A Wani Bude Wuta Na Kan Mai Uwa Da Wabi
Rahotanni da suke fitowa daga birnin Pretoria sun ce, adadin mutanen da su ka kwanta dama sanadiyyar bude wuta ta kan mai uwa da wabi, sun kai 11 daga cikinsu har da karamin yaro dan shekaru uku.
Jami’an ‘yan sandan kasar ta Afirka Ta Kudu ne su ka sanar da cewa an bude wutar ne a cikin wani gidan shan barasa dake birnin Pretoria a jiya Asabar. Haka nan kuma sun sanar da kama wasu mutane uku da ake zargin suna da hannu a abinda ya faru.
Kananan yara uku ne dai kisan ya hada da su, biyu daga cikinsu shekarunsu uku-uku ne, sai daya mai shekaru 12. Kuma da akwai wata buduruwa ‘yar shekaru 16 da ita ma lamarin ya rutsa da ita.
Wani sashe na sanarwar ya ce da akwai wasu mutane 14 da su ka jikkata sanadiyyar bude wuta na daban da aka yi a garin Solsifl.
Kasar Afirka Ta Kudu dai tana fuskantar matsaloli irin wannan na bude wuta akan mutane.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Dubban Mutane Suna Guduwa Daga Gabashin DRC Saboda Barkewar Sabon Fada December 7, 2025 Mutane Biyar Ne Suka Mutu A Wata Musayar Wuta Tsakanin Sojojin Afghanistan Da Pakistan December 6, 2025 Iran Da Masar Sun yi Kira Da Kawo Karshen Keta Hurumin Gaza da Labanon da Isra’ila ke yi December 6, 2025 Qatar Tayi Gargardi Game Da Gakiyar Yarjejeniyar Gaza Matukar Isra’ila Bata Janye Ba December 6, 2025 Gwamnatin Najeriya Za ta Karbi Sabon Bashin Dala Miliyan 500 A Bankin Raya Kasashen Afrika December 6, 2025 Kungiyoyin Kare Hakkin Bil Adama Sun Yi Gargadi Game Da Yunkurin Isra’ila Na Kashe Barghusi December 6, 2025 Gasar FIFA: Iran Ta Fada Cikin Group Mai Sauki A Gasar Kwallon Kafa Ta FIFA 2026 December 6, 2025 Kasashen Musulmi 8 Sun Ki Amincewa Da Korar Falasdinawa Daga Gaza December 6, 2025 Sojojin Afganistan Da Pakistan Sun Yi Musayar Wuta A Tsakaninsu Duk Tare Da Tsagait Wuta December 6, 2025 Rasha Tace Ta Kakkabo Jiragen Drones Na Ukrai 116 A Daren Jiya December 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci