Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, taron goron gayyata ne na kafa Nijeriya a matsayin cibiyar samar da makamashi tare da sabuntawa a Afirka, sannan kuma sauyin da aka samu na makamashi Nijeriya, ya bayar da damar zuba jari na sama da dala biliyan 410, daga tsakanin yanzu zuwa shekarar 2060.

Ya kara da cewa, “Daga cikin wannan, ana kuma bukatar sama da Naira biliyan 23, domin fadada hanyoyin samar da makamashin da kuma hada miliyoyin ‘yan Nijeriya, wadanda har yanzu suke rayuwa cikin matsalar wutar lantarki, amma yanzu babban burinmu shi ne, samar da tsarin samar da wutar lantarki mai karfin mega wat 277, nan da shekarar 2060.

Cikar wannan buri, ya wuce batun zuba hannun jari kadai, domin yana bukatar kirkire-kirkire, bayar da gudunmawa a cikin gida da kuma sadaukarwa.

“Wannan shi ne dalilin da yasa taken taron na bana ya kasance a matsayin, Aiwatar da Manufofin Nijeriya na Farko da Gudanar da Ci gaban Abubuwan Cikin Gida da kuma Samar da Makamashi, yana da matukar muhimmanci. Kazalika, yunkurinmu na dabarun masana’antu a Nijeriya na kira gare mu da mu dage kan makomar hanyoyin samar da makamashi na Afirka a nan gida.”

Ya kara da cewa, a karkashin wannan, an hada sama da dala miliyan 400 na sabbin alkawuran saka hannun jari a bangaren sabunta makamashi mai a Nijeriya.

“Wannan ya hada da na’urorin hasken rana na sola da fanel-fanel, mita ta zamani, batiri da sauran makamantansu. Babu shakka, ana hasashen wadannan kayayyaki za su samar da ayyukan yi kai tsaye sama da 1,500 a fadin jihohi da dama da kuma nuna kwarin gwiwa a duniya, kan shirin samar da makamashi mai tsafta a Nijeriya”.

A nasa bangaren, Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ya ce; taron NRIP na 2025, ba wani taro ne da kawai aka shirya ba, sai dan shelanta cewa, Nijeriya a shirye take ta jagoranci sauye-sauyen makamashin da ake samu a Afirka.

Taken taron na bana shi ne, ‘Aiwatar da Manufofin Najeriya na Farko’, yana magana ne a kan wani abu mai mai muhimmanci da ya dara masana’antu, wanda ya kunshi jajircewa, kwarewar masana’antu da kuma dorewar tattalin arziki na tsawon lokaci.

“A bangaren samar da wutar lantarki, manufar Najeriya ta farko ta nuna aniyar tabbatar da cewa; zamani na gaba na fasahar samar da makamashi mai inganci, tun daga na’urori masu amfani da hasken rana har zuwa na’urorin adana makamashin batiri da aka baza a fadin kasar, na alfahari tare da dauke da lakabin, “Wanda aka samar a cikin gida Nijeriya’.”

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma October 17, 2025 Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025 Labarai Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara October 16, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: samar da makamashi

এছাড়াও পড়ুন:

Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan October 19, 2025 Daga Birnin Sin Tawagar Likitocin Sin Ta Samar Da Tallafin Jinya Ga Kananan Yara Kyauta A Togo October 19, 2025 Daga Birnin Sin An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin October 18, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jihar Jigawa Za Ta Kashe Sama Da Naira Biliyan 2 Wajen Binciken Albarkatun Kasa
  • Labarin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya ƙarya ne – Sarkin Musulmi
  • Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa
  • Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia
  • Mutane 3,433 Sun Rasu a Hatsarin Mota 6,858 Cikin Wata 9 A Nijeriya – FRSC
  • NAJERIYA A YAU: Halin Da Muka Shiga Sakamakon Haihuwar ’Ya Mai Cutar Motsewar Kwakwalwa
  • EFCC ta ƙwato fiye da naira biliyan 500 a shekara biyu — Shetima
  • Jihohin Jigawa, Katsina Da Kano Za Su Kaddamar Da Asusun Wutar Lantarki Mafi Girma A Najeriya
  • Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka
  • Talauci ne babban maƙiyin ɗan Adam — Atiku