Larijani ya isar da sakon Ayatullah Khamenei ga Putin a ziyarar da ya kai Rasha
Published: 17th, October 2025 GMT
A yammacin jiya Alhamis ne sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow inda ya isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ga shugaban na Rasha.
Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka hada da huldar dake tsakanin kasashen biyu, da hadin gwiwar tattalin arziki, da ci gaban yankin, da kuma sauran batutuwa na kasa da kasa.
A makon da ya gabata, Putin ya ce mahukuntan Isra’ila sun bukaci ya isar da sako ga Iran cewa ba su niyar sake kaddamar da wani hari a kan kasar ta Iran.
“Muna ci gaba da samun sakonni daga jagorancin Isra’ila suna neman a isar da wannan ga abokanmu na Iran cewa, Isra’ila tana son ganin an warware wanann takaddama, kuma ba su da niyyar bude wani sabon babi na yaki da Iran,” in ji shi.
Takaddama tsakanin Iran da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kara ta’azzara ne bayan da gwamnatin Sahyoniya ta kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan Iran a ranar 13 ga watan Yuni wanda ya haifar da yakin kwanaki 12. Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kashe manyan kwamandoji da masana kimiyyar nukiliya tare da kashe daruruwan fararen hula a fadin kasar Iran. Ita ma Amurka ta shiga yakin kai tsaye daga bisani, inda ta jefa bama-bamai a wasu cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku, wanda hakan ya saba wa dukkanin dokoki na kasa da
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Madagaska : Ranar Juma’a za’a rantsar da Kanar Randrianirina October 16, 2025 Pezeshkian Ya Yi Gargadi Akan Makircin Makiya A Tsakanin Al’ummar Musulmi October 16, 2025 Euro-Med ta bukaci bangarori su shiga Gaza domin tattara bayanai kan kisan kiyashin Isra’ila October 16, 2025 Kenya : An dawo da gawar Raila Odinga gida October 16, 2025 Iran Ta Bukaci Kasashen Kungiyar NAM Su Hada Kai Don Fuskantar Rashin Bin Doka Da Oda A Duniya October 16, 2025 Iran: Yawan Karafan Da Ake Sayarwa Zuwa Kasashen Waje Ya Kai Dalar Amurka Billion $4 October 16, 2025 Falasdinu: Masu Gadin Gidajen Yari A HKI Sun Sun Daki Marwan Barghouti Har Ya Suma October 16, 2025 Venezuela Ta Bada Sanarwan Sabbin Matakan Tsaro A Kan Iyakar Kasar Da Colombia October 16, 2025 Tarayyar Afirka AU, Ta Jingine Samuwar Madagaska Daga Cikin Kungiyar October 16, 2025 Iran Ta Jaddada Cewa: A Shirye Take Ta Tattauna Amma Ba Zata Amince Da Juya Akalarta Ba October 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gaza: Fiye da Falasdinawa 350 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila tun bayan tsagaita wuta
Hukumomi a Gaza sun ce akalla Falasdinawa 357 ne sukayi shahada yayin da wasu 903 suka jikkata a hare-haren Isra’ila tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba.
Yawancin wadanda abin ya shafa mata ne da yara, in ji ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza a cikin wata sanarwa.
A cewar ofishin, sojojin Isra’ila na kuma tsare da mutane 38 ba bisa ka’ida ba.
ofishin ya ce ya lissafa laifukan tsagaita wuta guda 591, ciki har da harbi kai tsaye kan fararen hula, gidajensu, da tantuna, da kuma bama-bamai da rushe gidaje.
Sanarwar ta ce, wadannan laifukan, suna “nufin mamayar na wargaza yarjejeniyar da kuma haifar da mummunan yanayi wanda ke barazana ga tsaro da kwanciyar hankali a yankin Gaza.”
Ofishin ya yi kira ga Shugaban Amurka Donald Trump, da masu shiga tsakani da kuma masu ba da garantin tsagaita wutar, da kuma Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da su dauki matakai masu inganci don kawo karshen hare-haren Isra’ila da kuma tilasta wa Tel Aviv ta bi dukkan ka’idojin yarjejeniyar.
Yarjejeniyar tsagaita wuta, wacce Turkiyya, Masar, da Qatar suka shiga tsakani tare da goyon bayan Amurka, ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba don kawo karshen hare-haren Isra’ila na shekaru biyu da suka kashe mutane sama da 70,000, galibi mata da yara, tare da jikkata sama da 170,000 tun daga watan Oktoban 2023.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas : Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta December 1, 2025 Nijar : zamu sayar da uranium dinmu ga wanda muka ga dama_ Janar Tiani December 1, 2025 Tawagar ECOWAS za ta je Guinea-Bissau, bayan juyin mulkin soji December 1, 2025 Ministan Harkokin Wajen Turkiya Ya Isa Birnin Tehran Kuma Ya Gana Da Takwaransa Na Iran December 1, 2025 Pezeshkian: Makiya na neman kawo cikas ga ci gaban kasashen Musulmi December 1, 2025 Maduro Ya Gargadi Amurka Game Da Hankoron Mamaye Rijiyoyin Mai Na Venezuela December 1, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Isra’ila Yayin Da Natanyaho Ke Neman Afuwa Kan Batun Cin Hanci Da Rashawa December 1, 2025 Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Saudiya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran. December 1, 2025 Lebanon: Sakon Kungiyar Hizbullah Ga Paparoma December 1, 2025 Ireland Ta Sauya Sunan Wurin Shakatawa Daga Na Shugaban “Isra’ila” Zuwa Na Shahidiyar Falasdinu November 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci