2025-04-30@22:11:49 GMT
إجمالي نتائج البحث: 119

«Siminalayi Fubara»:

      Cikin adadin, masu bayyana ra’ayoyi daga kasashen Saudiyya da Serbia, suna cikin mafiya bayyana matukar baiken matakin na Amurka, da karin kaso 28.5 bisa dari. Yayin da a daya bangaren al’ummun Malaysia, da Isra’ila, da Australia, da Singapore, da Philippines, da Najeriya, da Portugal, da Pakistan, da Afirka ta kudu, kasonsu na nuna baiken...
    Wata tsohuwa mai shekara 80 a kasar Turkiyya za ta shafe sama da shekara 4 a gidan yari, saboda ta daki jikarta ’yar shekara 18 da silifa a lokacin da suke takaddama. Asiye Kaytan na zaune tare da jikarta Vural a unguwar Topraklık da ke Denizli a Kudu maso Yammacin Turkiyya. Tuntuni dai iyayen yarinyar...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ya bayyana kalaman gwamnatin ‘yan sahayoniyya a matsayin wani rudu da ba shi da amfani da har zai yi tasiri a zaman tattaunawan Iran da Amurka Wanda ba na kai tsaye ba, yana mai cewa duk wani hari ko da karami ne za a kai kan Iran zai zama tamkar tartsatsin...
    Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila’ tana aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa ana gani kai tsaye a tauraron dan Adam Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a yau Talata ta yi Allah wadai da shirun da duniya ta yi game da yadda gwamnatin...
    Rikicin sarautar Kano da aka shafe kusan shekara guda ana yi, ya ɗauki sabon salo. Abin da ya fara a matsayin rikicin neman halacci tsakanin sarakuna biyu —Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero —yanzu ya kai su ga yin naɗin sarautu iri guda a fadodinsu daban-daban a masarauta ɗaya. A ranar 9 ga Afrilu,...
    A cewarsa, tuni aka shirya wuraren kwana da abinci ga maniyyatan a kasar Saudiyya.   Abdulkadir ya tabbatar da cewa, ana shirye-shirye, inda za a yi alluran rigakafi a ranar 28 ga Afrilu, za a raba tufafi a 30 ga Afrilu, sannan kuma za a raba jakunkuna a ranar 1 ga Mayu.   Ya kara...
    Gwamna Dauda Lawal ya amince da nadin Amirul Hajj karkashin wani kwamiti don sa ido kan ayyukan Hukumar Alhazai ta Jiha a Saudiyya don tabbatar da bin ka’idojin gida da na Saudiyya gaba daya a duk lokacin gudanar da aikin Hajjin 2025.   Sakataren gwamnatin jihar, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya sanar da hakan...
    Sabuwar gwamnatin Siriya tana kara matsa lamba kan bangarorin ‘yan gwagwarmaya domin Isra’ila ta janye daga wasu yankunan kasarta Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da tura kayayyakin soji zuwa tsaunukan Dutsen Harmon, yayin da suke hanzarta gina abin da suka kira “Katangar tsaro.” Har ila yau, sun karfafa wuraren tsaro da suka kafa a...
    Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta tabbatar da tsare-tsaren da kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta Sin da majalisar gudanarwar kasar suka tsayar don gaggauta kyautata tsarin tafiyar da ciniki daidai da zamani, da ingiza ingantaciyar bunkasuwar cinikin sarin kaya da sayen kayan masarufi bisa matakai daban-daban. Bisa alkaluman da hukumar kididdigar Sin ta fitar a...
    Nahiyar dake da yawan mutane fiye da biliyan 1.4 na da babbar kasuwa. Matakin Donald Trump ka iya samar wa kasashen nahiyar damar karfafa hadin gwiwarsu da inganta tsarin masana’antu. Ban da wannan kuma, kasashen Afirka suna iya samun mafita ta hanyar kara hadin gwiwa da kasashe masu tasowa musamman ma kasar Sin.   Cikin...
    Kungiyar Hamas ta yi watsi da kudirin baya bayan nan na Isra’ila na kwance damarar kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa domin tsagaita bude wuta a Gaza, tana mai kiran hakan a matsayin wani yunkuri na gurgunta ‘yancin Falasdinu. Tattaunawar da ake ci gaba da yi tsakanin Isra’ila da Hamas ta tsaya cik, inda Isra’ila ta matsa kaimi...
    Ilimi na da muhimmanci wajen gina al’umma, amma ga daliban Makarantar Firamare ta Bare a karamar Hukumar billiri, Jihar Gombe, wannan lamari ya zama kamar mafarki mai wahalar tabbatuwa. Duk da ikirarin da Gwamnatin Jihar Gombe ke yi na cewa, tana fifita ilimi ta hanyar manyan ayyuka kamar gine-ginen makarantu masu hawa biyu a kowace...
    Gao ya kara da cewa, Sin da kasashen Afirka sun zamo misali na bunkasa hadin gwiwar kasashe masu tasowa, suna kuma gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama, kana sun nunawa duniya cewa kasashe masu tasowa na da ikon samar da sabon salon wayewar kan bil’adama na kashin kan su, kuma za su...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakisatan ta kara jaddada matsayinta na rashin amince da HKI a matsayin kasa tana kuma goyon bayan Falasdinawa a gwagwarmayan da suke yi na kwatar yencinsu da kuma kasarsu daga hannun HKI da kuma kasashen yamma musamman Amurka masu goya mata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran wannan sanarwan tazo...
      Ya kara da cewa, CMG ta dade tana kasancewa ingantacciyar gada dake inganta fahimtar juna tsakanin kasashen biyu, kuma ya yi imanin cewa, hadin gwiwarsu a wannan karo zai kara karfafa daddaden dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
    Paris St Germain ta kai zagayen daf da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai duk da rashin nasara da ta yi a hannun Aston Villa ranar Talata a Villa Park. Aston Villa ta yi nasarar cin PSG 3-2, inda Tielemans da McGinn da kuma Konsa suka ci mata ƙwallayen a wasa falle na biyu a...
    A yayin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai kasar Malaysia, daga yanzu manyan kafofin sadarwa kamar kafar yada labarai ta kasar Malaysia za su fara nuna shirin bidiyon “Bayanan magabata dake jan hankalin Xi Jinping” na harshen Malay wanda CMG ya shirya.   Shirin ya mai da hankali ne kan...
    Lauyoyin Landan suna tattara bayanai kan ‘yan Birtaniya da suka yi aiki a cikin rundunar sojojin mamayar Isra’ila Kwararru kan harkokin shari’a na kasar Biritaniya sun ce gurfanar da wasu ‘yan kasar masu takardar ‘yan kasa biyu da ke aiki a cikin sojojin mamayar Isra’ila a gaban kuliya bisa zargin hannu a tafka laifukan yaki...
    Gabanin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi a Malaysia, firaministan kasar Datuk Seri Anwar Ibrahim, ya zanta da manema labarai na CMG a jiya Litinin, inda ya darajanta bunkasar huldar kasashen biyu.   Anwar Ibrahim ya kuma bayyana matukar amincewa da tunanin Xi Jinping na ingiza al’adu da wayewar kan...
    A yammacin yau ranar 15 ga watan Afrilu ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Kuala Lumpur ta jirgin sama na musamman, domin gudanar da ziyarar aiki a kasar Malaysia.   Xi Jinping ya gabatar da rubutacciyar jawabi a filin tashi da saukar jiragen sama, inda ya ce, yana fatan daukar wannan...
    Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata. Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa. Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne...
    Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata. Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa. Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne...
    Gwamnatin kasar Ajeriya ta bayyana jami’an diflomasiyyar Faransa da suke kasar su 12 a matsayin ‘wadanda ba a bukatar ganinsu” a cikin kasar, tare da yin kira a gare su da su fice a cikin sa’oi 48. Bugu da kari kasar ta Aljeriya ta yi suka da kakkausar murya akan ministan harkokin wajen Faransa Bruno...
    Wata ’yar kasar Jamus mai suna Alexandra Hildebrandt mai shekara 66 ta ja hankalin jama’a bayan ta haifi ɗanta na 10 ba tare da maganin haihuwa ba. Haihuwar ta faru ne a ranar 19 ga Maris a Asibitin Charité da ke Berlin da taimakon likita. Bello Turji ya kashe manoma 11 a Sakkwato ’Yan bindiga...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani muhimmin abun lura ma shi ne ita kanta Amurka ba za ta tsira daga mummunan tasirin wannan yaki na cinikayya da take rura wutarsa ba. Ko shakka babu matakin zai haifarwa Amurka matukar koma bayan tattalin arziki, da hauhawar farashi a cikin gida, da dakile guraben ayyukan yi da sauransu. Tuni ma kasuwannin Amurkan...
    Sojojin kasa na kasashen Iran ta Armenia sun fara atisayen soje na hadin guiwa a tsakaninsu, don kyautata tsaro na kan iyakar kasashen biyu na kuma tsawon kwanaki biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran ne suke jagorantar wannan atisayen. Da nufin...
    Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya ce kasarsa na shirin amincewa da yankin Falasdinawa a matsayin kasa nan da watanni masu zuwa. Ya ce hakan na iya faruwa a farkon watan Yuni nan wannan shekarar a taron Majalisar Dinkin Duniya da za a gudanar a New York. kawo yanzu, Kasashe 147 ne suka amince da...
    A wani mataki na kara nesanta kanta da Faransa da ta yi mata mulkin mallaka, Nijar ta ayyana harshen Hausa a matsayin yaren ƙasa a madadin Faransanci. Kamfanin dillancin labarin kasar AFP ne ya ruwaito hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 31 ga Maris. Boko Haram na sake ƙwace ikon wasu yankuna a...
    Ya ce karin wa’adin na baya-bayan nan ya biyo bayan cikar wa’adin farko na ranar 1 ga Afrilu, 2025, wanda aka sanya tun da farko a ranar 24 ga watan Janairu.   Umar ya kara da cewa, duk da wannan karin wa’adin, amma an ci gaba da samun karancin fitowar masu filaye domin sabunta takardunsu....
    Jami’in ya ce, barazanar da Amurka ke yi game da kara tsananta matakin da za ta dauka, kuskure ne dake nuna muguwar aniyarta ta dakile moriyar sauran kasashe, kuma tabbas Sin ba za ta amince ba ko kadan.   Kasar Sin ta sake nanata ra’ayinta cewa, ba wanda zai ci gajiyar tayar da zaune tsaye...
    Mazauna yankin ƙaramar hukumar Funtua ta Jihar Katsina sun ce ’yan bindiga sun shiga wasu ƙauyukan yankin, inda suka kwashi mutane sama da 50 da suka hada da mata da ƙananan yara. Maharan sun kuma kashe akalla mutum shida, inda suka sake kai wani hari a yankin Ƙaramar Hukumar Ɗandume ta jihar. Rahotanni sun ce...
    Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta bayyana cewa za ta fata tattaunawa wacce ba ta kai tsaye ba da Amurka a ranar Asabar mai zuwa a kasar Oman. Ministan harkokin wajen Iran din ne Abbas Araghchi ya bayyana hakan a shafinsa na ‘’X’’ a safiyar Talata. “Iran da Amurka za su gana a Oman ranar Asabar...
    Jamhuriyar Nijar ta ayyana harshen Hausa a matsayin na kasa, yayin da Faransanci ya zama harshen aiki mai sauki, don haka, Faransanci ba yaren hukuma ne ba. Matakin dai ya dogara ne da shawarwarin da babban taron kasar ya gabatart a watan Fabrairu, wanda kuma shugaban kasar Janar Abdourahamane Tiani ya amince da shi a...
    Hakazalika, Lin Jian ya jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su bi ka’idojin yin shawarwari da samun ci gaba da more fasahohi da juna, da kiyaye bin ra’ayin bangarori daban daban, da kin amincewa da ra’ayin bangare daya da ba da kariya ga cinikayya, da tabbatar da tsarin kasa da kasa bisa tushen MDD...
    A bisa wannan dalili ne yasa akwai bukatar mutane su rungumi fannin noman Aya, duba da cewa; hanya ce ga wanda ya zuba jarinsa a fannin, zai iya kara samar wa da kansa kudaden shiga. Sai dai, akasari an fi yin nomanta a Arewacin Nijeriya, musamman ma kuma a Jihar Katsina. Haka zalika, fannin na...
    Mai magana da yawun jam’iyyar APC a Jihar Ogun, Tunde Oladunjoye, ya rasu. Ya rasu ne a ranar Juma’a, 4 ga watan Afrilu, 2025, yayin da yake jinya a ƙasar waje kan wata rashin lafiya da ba a bayyana ba. An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai Yadda aka yi jana’izar Dokta...
    Matakan harajin fito na Amurka na haifar da koma-bayan tsarin cinikayyar duniya. Game da wannan batu, kafar CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, ta gudanar da wani binciken jin ra’ayin al’umma ga masu amfani da intanet na sassan kasa da kasa, inda suka yi tir da irin wannan abun da...
    Wata gobara da ta tashi da yammacin ranar Alhamis ta lalata wani sashe na shahararren gidan Ado Bayero da ke ƙofar Nassarawa a Kano. Aminiya ta samu rahoton cewa lamarin ya faru ne a hawa na tara na ginin da cibiyar Jami’ar Northwest University take. Matafiya sun maƙale bayan ruftawar gada a Taraba Ruwan sama...
    Jami’ar Bayero Ta Kaddamar da shirin amfani da adaidaita Sahu wajen zirga zirga a Jami’arA wani gagarumin yunkuri na bunkasa zirga zirga da walwalar dalibai, Shugaban Jami’ar Bayero Kano Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya kaddamar da shirin amfani da babura masu kafa uku ko adaidaita a harabar jami’ar a hukumance. Wannan yunƙurin na nufin samar...
    Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya nanata shirin Tehran na shiga tattaunawar da Amurka kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya, yana mai gargadin cewa barazanar soji daga Amurka na dagula halin da ake ciki a yanzu. “Jamhuriyar Musulunci, kamar yadda ta kasance a baya, a shirye take don yin shawarwari na hakika,” in...
    Masarautar Zazzau ta sanar da soke Hawa Bariki a wannan sallar ta bana — daya daga cikin haye-hayen shagulgulan Sallah na al’ada da masarautar ke gudanarwa a washegarin idin karamar Sallah. A bisa al’adar Hawan Bariki, Sarkin Zazzau ya kan kai wa Gwamna gaisuwar sallah tare da duk hakimansa yayin da mazauna za su yi...
    Jam’iyyun siyasa a kasar Gabon sun fara yakin neman zabe wanda za’a gudanar a ranar 12 ga watan Afrilu na wannan shekara ta 2025 a jiya Asabar. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto shugaban kasar Riko Brice Clotaire Oligui Nguema wanda ya jagoranci juyin mulki wa tsohon shugaban kasar Ali Bongo, sannan...
    Kasashen Iran, Lebanon, Iraki, da kuma Yemen sun kaddamar da wani atisayen hadin gwiwa na sojojin ruwa domin nuna goyan baya ga  Falasdinawa a zirin Gaza, wadanda ke ci gaba da fuskantar zalinci  na gwamnatin Isra’ila. An fara faretin hadin gwiwa a tekun Fasha, da yankin gabar tekun Makran, da kuma tekun Caspian da ke...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300...
    A jiya Asabar 22 ga watan nan, jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng, ya amsa gayyatar halartar taro na 2 na tattaunawar sassan Sin da na Amurka game da batun tattalin arziki karkashin cibiyar Jimmy Carter, inda ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.  A cikin jawabinsa, jakada Xie Feng ya ce ko kadan,...
    “Saboda haka, za a soke sunayen kadarorin da suka shafe sama da shekara goma ba a biya musu haraji ba nan take, Bugu da kari kuma, ana bayar da wa’adin kwanaki 21 ga masu rike da gidajen da ake rike da bashin kudin haraji na tsawon shekara daya zuwa goma, sannan kuma za a soke...
    Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umurnin a gudanar da bincike don gano abinda ya hadda hatsarin day a faru a kan gadar Karuk an titin Abuja Keffi a daren Labaran da ta gabata, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da kuma jikatan wasu. Jaridar Premium Times ta nakalto shugaban kasar yana fadar haka...
    Gwamnatin Jihar Yobe ta kafa cibiyoyin bayar da abinci 85 domin samar wa almajirai abinci a dukkanin Ƙananan Hukumomin 17 na jihar, a lokacin azumin Ramadan. Sakataren zartarwa na Hukumar Ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Jihar Yobe, Malam Umar Abubakar ne, ya bayyana hakan a wata hira da Daily Trust a ranar Alhamis. Sanƙarau...
    A wani gagarumin yunkuri na karfafa harkokin mulki da inganta ayyukan yi, gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nada wasu mukamai da karin girma.   Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.   Sabbin canje-canje da suka samo asali...