Ana zargin wa da ƙani da yi wa almajiri yankan rago a Adamawa
Published: 17th, March 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Adamawa ta cafke wani ƙani da yayansa — Aliyu Abdulmalik da Ibrahim Abdulmalik — kan zargin yanke kan wani almajiri ɗan shekara 10, Abdallah Lawali.
Bayanai sun ce ’yan uwan junan biyu sun aikata wannan ta’asa ce a ranar 7 ga watan Maris a unguwar Sarkin Yamma da ke Ƙaramar Hukumar Jada.
Sanarwar da rundunar ’yan sandan ta fitar ta ce an kama ababen zargin ne da gangar jikin almajirin a cikin wani buhu, yayin da aka ƙwaƙulo kansa a cikin wani rami da suka binne a harabar gidansu.
Rundunar wadda ta ce yanzu haka bincike ya kankama a kan lamarin, ta kuma bayyana cewa ababen zargin sun yi iƙirarin aikata laifin da suka alaƙanta da sharrin shaiɗan.
Kwamishinan ’yan sandan jihar CP Dankombo Morris, ya tabbatar da cewa za a yi adalci a lamarin, yayin da yake kira ga al’umma da su kasance masu lura da miƙa rahoton duk wani motsi da su aminta da shi ba zuwa ofishin mahukunta mafi kusa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Adamawa Wa da ƙani
এছাড়াও পড়ুন:
Dalilin da ya sa muka gayyaci Sheikh Lawal Triumph – ’Yan sanda
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta bayyana dalilin da ya sa ta gayyaci malamin addini Sheikh Lawal Triumph.
A wata sanarwa da ta fitar, ’yan sanda sun ce sun sani cewa wasu daga cikin wa’azozin da Sheikh Triumph ke yi suna haddasa rashin jituwa a tsakanin al’ummar jihar.
Ya kamata mulkin Najeriya ya ci gaba da zama a hannun ’yan Kudu — Hannatu Musawa Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – ƊangoteRundunar ta ce kowa na da ’yancin faɗin albarkacin bakinsa, amma dole ne komai ya kasance bisa doka.
Saboda haka ne Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, ya gayyaci Sheikh Lawal Triumph don tattaunawa da jami’an gwamnati, shugabannin addini da na al’umma.
Manufar ita ce a nemi hanyar hana irin wannan rikici sake faruwa a nan gaba.
Rundunar ta kuma buƙaci al’umma da su kwantar da hankalinsu su guji yin abubuwan da za su haifar da tashin hankali.
“Yana da muhimmanci a girmama ra’ayin juna da abin da mutane suka gaskata, kuma a tabbatar da cewa duk abin da mutum zai faɗa ko zai yi bai saɓa wa doka ba,” in ji rundunar.
Wannan lamari ya fara ne bayan wani wa’azi da Sheikh Lawal Triumph ya yi, wanda ya tayar da ƙura.
Ya faɗi haka ne a matsayin martani ga waɗanda suke musanta wani hadisi da ke cewa kwarkwata ƙazanta ce.
Wannan ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda wasu suka fara kiran a kashe Sheikh Lawal Triumph bisa zargin ya yi izgili ya Manzon Allah (S.A.W).
Rundunar ta kuma shawarci jama’a da su kai koken su ga hukumomin da suka dace, maimakon yaɗa saƙonni da za su iya tayar da hankali a shafukan sada zumunta.