Aminiya:
2025-11-02@12:29:42 GMT

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 50 a Amurka

Published: 6th, July 2025 GMT

Hukumomi a Jihar Texas ta Amurka sun ce gomman mutane sun riga mu gidan gaskiya ciki har da kananan yara sakamakon wata mummunar ambaliyar ruwa a ranar Asabar.

Sai dai ya zuwa yau Lahadi, adadin wadanda suka mutu sun kai 50 ciki har da kananan yara 15 yayin da ake ci gaba da aikin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su kamar yadda wani babban jami’in dan sanda na yankin, Larry Leitha ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.

An kama ɗan Najeriya yana taimaka wa Rasha a yaƙinta da Ukraine Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 41 a Nijar

Tuni dai Shugaba Donald Trump ya sanar da cewa gwamnati na yin duk mai yiwuwa wajen kai dauki yankin na Texas, inda ya ce shi da mai dakinsa Melania na mika sakon jaje da ta’aziyya ga iyalan wadanda suka mutu.

Trump ya kara da cewa jami’an hukumar kashe gobara da sauran jami’an agaji na ta fadi tashin kubutar da al’umma tare kuma da kokarin dakile tasirin ambaliyar.

Baturen ’yan sandan yankin Kerr County, ya sanar da cewa masu aikin ceto sun yi nasarar kubutar da mutane sama da 800 yayin da ake ci gaba laluben kananan yara galibinsu mata da aka nema aka rasa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ambaliyar ruwa Jihar Texas kananan yara

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

Bug da kari Tinubu ya jinjina wa Shugaban jami’ar, Farfesa Wahab Olasupo Egbewole (SAN)da ‘yan tawagarsa wajen maida hankalin da suka yi na bunkasa Jami’ar da kumna kudurinta na muradun ci gaban da ake bukata.

Shi ma anashi jawabin Shugaban Jami’ar Sarkin Katsina, Alhaji. Abdulmumin Kabir Usman, wanda Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Idah ya wakilta, ya nuna jin dadinsa kan irin kokarin da UNILORIN saboda bunkasar ilimi da kumasamar wuraren koyon kaaratu masu kyau da kuma suka dace.

Ya yi ma kallon ayyukan da ak kaddamar a matsayin“ irin abubuwan da ake bukatar gani ke nan”da za su taimakawa lamarin koyarwa, koyo,da kuma bincike, inda ya kara da cewa yadda Jami’ar ta maida hankalinta wajen bunkasa dabarar koyon yin abubuwa zai taimakawa dalibai su tashi da sun koyi abubuwan da zasu yi baya rayuwar da suka yi cikin aji.

A nashi jawabin mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa. Egbewole ya nuna farin cikinsa da godew a Shugaban kasa Tinubu kan yadda ya amince da gaiyar da Jami’ar ta yi ma shi, da kuma taimaka mata wajen tafiyar da bunkasar abubuwan jin dadi.

“Muna nan muna sa ido saboda ci gaban samun abubwan da suke taimakawa ci gaba kwarai da gaske a kowace rana kamar yadda yace yana da amincewa da yardarm ci gaba da samun hakan’’.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna November 1, 2025 Manyan Labarai Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami November 1, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su November 1, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda
  • An Yi Wa Yara Sama Da Miliyan Biyu Allurar Rigakafin Mashaƙo Da Sankarau A Zamfara
  • ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara 
  • Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja
  • Kamfanin Amazon na shirin sallamar ma’aikata 600,000 don maye gurbinsu da mutum-mutumi