Muhimman Kamfanonin Jiragen Sama A Duniya Sun Farfado Da Zirga-Zirgaf Zuwa Iran
Published: 6th, July 2025 GMT
Kamfanin jiragen sama na UAE airlines ko emirate ya sake farfado da zirga zirga zuwa kasar Iran bayan da aka rufe sararin samaniyar kasar Iran a ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata.
Jaridar National ta kasar Amurka ta bayyana cewa kasashe da dama a duniya sun dakatar da zirga zirga zuwa JMI saboda yakin da HKI da Amurka suka kai mata daga 13 ga watan zuyi har zuwa kwanaki 12.
Labarin ya kara da cewa kasashen Iraki da Jordan sun dakatar da zuwa kasar Iran saboda yaki kuma saboda gwamnatin Iran ta hana jiragen sama tashi ko kuma zuwa kasar.
A ranar Alhamis ne JMI ta gabata ne hukumomin Iran suka bude sararin samaniyar kasar wanda ya nuna al-amura suna komawa kamar yadda suke bayan yakin kwanaki 12. A halin yanzu dai tashar jiragen saman na Esfahan ne kawai ba’a sake budewa ba, mai yuwa sai kwani m asu zuwa idan an kammala gyare gyaren da yakamata a yi, bayan hare-haren da HKI ta kai mata.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta gaggauta dakatar da shuka kiyayya, da haifar da tashin hankali, da rura wutar gaba a tekun kudancin kasar Sin, kana ta kyale a dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin. Lin Jian, ya bayyana hakan ne yau Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da aka yi masa tambaya kan batun.
Wasu rahotanni daga kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, a baya bayan nan, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya fitar da sanarwa dake cewa Amurka na goyon bayan kasar Philippines, game da watsi da ta yi da tsare-tsaren kasar Sin na kafa yankin kare muhallin halittu a tsibirin Huangyan Dao.
Lin ya ce “Mun gabatar da kakkarfan korafi a yau, dangane da kuskuren da Amurka ta tafka. Tsibirin Huangyan Dao yankin kasar Sin ne tun fil azal”, kuma kafa yankin kare muhallin halittu a tsibirin na karkashin ikon mulkin kai na Sin, wanda hakan ke nufin yana bisa turba, ya dace da doka, bai kuma cancanci suka ba. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp