Shugaban Kasar Iran Ya Ce Kungiyar ECO Ta Yi Tir Da Hare-Haren HKI Kan Kasarsa
Published: 6th, July 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya bayyana cewa dukkan kasashe mambobia a kungiyar ECO ta raya tattalin arziki na kasashen yankin sun yi tir da HKI a taron kungiyar wanda aka gudanar a birnin Khankendi. Na kasar Azerbaijan. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka bayan tawowarsa daga taron a daren jumma’a a kuma shafinsa na X.
Shugaban ya bayyana cewa yana godiya ga dukkan kasashen kungiyar ECO da kuma sauran kasashen yankin da sauran kasashen duniya wadanda suka nuna goyon bayansu ga kasarsa bayan yakin kwanaki 12 da HKI da kuma Amurka.
Daga karshe yace yana fatan kasar da sauran kasashen kungiyar ECO zasu kai ga gurunsu na bunkasar tattalin arziki ta shekara ta 2035.
A ranar jumma’a 13 ga watan Yuni ne jiragen yakin HKI suka kai hare-hare a kan Iran inda suka kashe manya-manyan jami’an sojojin kasar da masana fasahar Nukliya da kuma fararen hula wadanda basu san hawa ko sauka ba. Sannan Amurka ta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliya na kasar da suke fordo Natanz da kuma Esfahan.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kungiyar ECO
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Amurka Yace Yana Jirin Hamas Cikin Sa’o’i 24 Masu Zuwa Don Tsagaita Wuta Na Kwanaki 60
Shugaban kasar Amurka Donal Trump Ya Bayyana cewa nan da kwana guda ko sa’o’ii 24 masu zuwa ne zai sani, ko kungiyar Hamas ta amince da ‘shawararsa ta tsagaita wuta da HKI kuma ta karshe a gaza.
Shafin yanar gizo ta labarai ‘Arabnews ta kasar Saudia’ ta nakalto Trump yana fadar haka a yau jumma’a.
A wani bangare shugaban ya ce yayi magana da gwamnatin kasar Saudia dangane da fadada yarjeniyar Ibrahimia wacce ya samar da ita a shugabancinsa na baya wacce take bukatar kasashen larabawa su samar da huldar jakadanci da HKI, wanda kuma ya sami nasarar a kan wasu kasashen larabawa na yankin tekun Farisa.
Daga shekara ta 2023 ya zuwa yanzu yahudawan sun kashe falasdinawa kimani 56,000 sannan fiye da dubu 12000 suka ji rauni.
Majiyar Falasdinawan ya zuwa yansu, ta bayyana cewa fatansu shi ne tsagait wutar ta kaika ta zamam din-din din.