Aminiya:
2025-07-06@15:42:02 GMT

An kama ɗan Najeriya yana taimaka wa Rasha a yaƙinta da Ukraine

Published: 6th, July 2025 GMT

Sojojin Ukraine sun kama wani ɗan Nijeriya da ke taimaka wa Rasha a yaƙin da suke gwabzawa sama da shekaru biyu biyo bayan mamayar ƙasarsu.

Wani bangaren sojin da ke ƙunshe da mayaƙan Rasha da ke goyon bayan Ukraine a wannan yakin, wanda ake kira ‘Freedom Of Russia Legion ne ya kama Kehinde Oluwagbemileke mai shekaru 29 a yankin Zaporizhzhia bayan shafe watanni biyar yana yaƙi a cikin mayaƙan Rasha.

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 41 a Nijar Kwankwaso ba zai yi mana takara a 2027 ba — NNPP

Oluwagbemileke ya shafe shekaru huɗu yana zaune a ƙasar Rasha kafin a kama shi akan laifin da ke da nasaba da miyagun ƙwayoyi.

An ruwaito cewa matashin ya amince ya shiga wannnan yaƙi ne domin a rage masa yawan shekarun da zai shafe a gidan yari sakamakon laifin da aka kama shi da shi.

Gbemileke yana daga cikin dubban sojojin haya daga ƙasashe masu tasowa da ke taimaka wa Rasha a yaƙinta da Ukraine.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kehinde Oluwagbemileke Nijeriya Rasha Ukraine

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya umarci sojoji su murƙushe ’yan ta’adda a faɗin Najeriya 

Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya umarci dakarun sojin Najeriya da su murƙushe ’yan ta’adda, masu tada ƙayar baya, da ’yan awaren Biyafara da ke barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Yayin bikin Ranar Sojoji ta 2025 da ya gudana a Jihar Kaduna, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya wakilci Shugaba Tinubu.

Mutum 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–Kano Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC

Tinubu ya ce: “Lokacin tashi ya yi. Ina tare da ku ɗari bisa ɗari don murƙushe masu yunƙurin rusa Najeriya. Ku ne ƙarfina, goyon bayana da addu’o’ina.”

Ya gargaɗi cewa barazanar da ake fuskanta ba ƙananan abubuwa ba ne.

“Waɗannan miyagun ba sa bambanta tsakanin coci da masallaci. Suna mayar da yara marayu ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba,” in ji shi.

Tinubu, ya kuma sha alwashin ci gaba da inganta walwalar sojoji da ba su kayan aiki na zamani.

“Za mu ci gaba da zuba jari a makamai, bayanan sirri da horo. Sojojinmu dole su kasance a shirye a koyaushe don kare Najeriya.”

Ya jinjina wa sojojin da suka rasa rayukansu wajen kare ƙasa.

“Jininsu ba zai zube a banza ba. Za mu ci gaba da tunawa da su har abada.”

Shugaban Hafsan Soji, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya yaba wa jarumtar dakarun sojin Najeriya.

“Karfinmu na gaske shi ne jarumta da sadaukarwar sojan Najeriya,” in ji shi.

Bikin ya ƙayatar da dandazon jama’a da manyan baƙi, inda aka nuna kayan aikin dakarun na zamani.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya umarci sojoji su murƙushe ’yan ta’adda a faɗin Najeriya 
  • Ana Tuhumar Tsohon Ɗan Wasan Arsenal Thomas Partey Da Laifin Fyaɗe A Ƙasar Ingila
  • Sin: Tsawaitar Rikicin Ukraine Ba Zai Amfani Kowa Ba
  • Lardin Hainan Na Kasar Sin Ya Samu Karuwar Cinikayyar Hajoji Da Aka Daukewa Haraji Cikin Shekaru Biyar
  • ’Yansanda Sun Kama ’Yan Bindiga 17 Tare Da Kashe 3 A Abuja
  • SON Ta Bada Shaidar Ingancin Kayayyaki Ga Wasu Kamfanoni A Kaduna
  • NAJERIYA A YAU: Shin Ko Hadakar Sabuwar Jamiyyar ADC Za Ta Fidda Wa ‘Yan Najeriya Kitse Daga Wuta?
  • Rasha ta amince da gwamnatin Taliban a Afghanistan
  • Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 1,191, Sun Ceto 543 Cikin Watanni Uku