Majiyar kafafen yada labarai na Amurka sun bayyana cewa akalla mutane 52 suka rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwan sama a jihar Texas.

Jaridar US Today ta bayyana cewa an kubutar da daruruwan mutane daga halaka, amma kuma har yanzun ba san makamon daruruwan mutane ba. Sannan kungiyoyin bada agaji suna ci gaba da neman masu sauran shanruwa.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ne ya sauka a jiya Asabar ya kuma ciika kogin Guadalupe wanda yayi ambaliya ya kuma rufe garuruwa da dama da suke bakin kogin.

Gwamnatin Jihar Tezas Dan Patrick ya bayyana cewa an kubutar da mutane kimani 850 amma yawan matattu kuma yana karuwa a lokacinda jami’an agaji suke ci gaba da neman gawaki da kuma masu sauran numfashi.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare

Fitattun dalibai akalla 12 ne  daga makarantun gwamnati suka samu guraben tallafin karatun sakandare  a ƙarƙashin Asusun Tallafin Karatu na Jihar Kwara (Kwara-ETF).

A wajen taron gabatarwa ga waɗanda suka fara cin moriyar shirin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa ci gaban harkar ilimi a Najeriya abu ne mai tsada kuma ya zama wajibi kowa ya bayar da gudummawarsa.

Ya roƙi masu masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wajen gina makarantu ko kuma su ɗauki nauyin daliban da suka nuna bajinta da jajircewa a harkar karatu.

A cewarsa, an zabo daliban 12 ne  sakamakon bajintar da suka nuna a matakai daban-daban na tantancewa da Kwara ETF ta gudanar.

Gwamnan ya bayyana cewa tallafin ya kunshi dukkan kuɗin da ake buƙata a karatun sakandaren daliban.

“Muna kira da jama’a su ba da gudummawa da kuma ɗaukar nauyin ɗalibai. Kada a bar wannan aiki ga gwamnati da iyaye kadai. Ilimantar da ‘ya’yanmu hakki ne da ya rataya a kanmu gaba ɗaya,” in ji Gwamna.

Ya yaba da tsarin zaɓen kuma ya taya waɗanda suka yi nasara murna.

A nata jawabin, Babbar Shugabar Kwara ETF, Oluwadamilola Amolegbe, ta ce daliban 12 sun fito ne daga cikin jerin ɗalibai 640 da aka fara tantancewa bisa cancanta.

Ta bayyana cewa tsarin zaɓen ya fara ne da rubuta jarabawa ga dukkan daliban firamare na aji shida da suka amfana da shirin KwaraLEARN na koyon fasahar zamani, har zuwa lokacin da aka kammala tantancewa.

 

Ali Muhammad Rabi’u 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
  • Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Ta Kama Bisa Kuskuren Safarar Ƙwayoyi
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara