Leadership News Hausa:
2025-11-02@16:57:52 GMT

Tsohon Ɗan Takarar Gwamna A Legas  Ya Koma APC Daga PDP

Published: 17th, March 2025 GMT

Tsohon Ɗan Takarar Gwamna A Legas  Ya Koma APC Daga PDP

Tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Legas na jam’iyyar PDP, Dr. Olajide Adediran, wanda aka fi sani da Jandor, ya sanar da koma wa jam’iyyar APC mai mulki. Wannan sanarwar ta zo ne bayan kwanaki biyu kacal da ya fice daga jam’iyyar PDP.

Jandor ya ba da sanarwar koma wa jam’iyyar APC ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishin yaƙin neman zaɓensa da ke Ikeja a ranar Litinin.

Ya bayyana cewa ya yi shawarwari da shugaban ƙasa Bola Tinubu, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, da wasu manyan mutane a fagen siyasa bayan ya fice daga PDP.

El-Rufai Ya Yi Alƙawarin Haɗa Abokan Hamayya Don Yaƙar APC A Zaɓen 2027 Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – Atiku

Kakakin Jandor, Gbenga Ogunleye, ya tabbatar da cewa taron da ya yi da shugaban ƙasa ya gudana ne a ranar Litinin da ya gabata. Ya kuma bayyana cewa Jandor ya gana da wasu manyan shugabanni kamar tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Babangida, tsohon shugaban mulkin soja Abdusalami Abubakar, da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP a zaben 2023, Prince Adewole Adebayo, domin yin shawarwari kan matakin da ya ɗauka.

Haka kuma, sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa da wasu shugabannin jam’iyyar sun ziyarce shi kwanan nan domin roƙonsa ya dakata kan matakin ficewa daga jam’iyyar. Duk da haka, Jandor ya ƙuduri aniyar ci gaba da shirye-shiryensa na siyasa a cikin jam’iyyar APC.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Gwamna

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda

Daga Usman Muhammad Zaria

 

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.

Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.

Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.

Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen  tsaro.

CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum
  • PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike
  • PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu da ke da alaƙa da Wike
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Dan Majalisar Jema’a/Sanga, Daniel Amos, Ya Koma Jam’iyyar APC
  • Kotu ta dakatar da gudanar da babban taron PDP
  • Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa
  • Kotu ta dakatar da babban taron PDP
  • Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
  • Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano Spalleti