Madalla da hutu ga ’yan makaranta domin azumi
Published: 17th, March 2025 GMT
Wasa wasa dai Musulunci na dawowa gidansa wato Nijeriya ta Arewa ta hanyoyi iri-iri. Ba dai sai an nanata ba.
Arewacin Nijeriya da ma sassa da dama a jamhuriyar Nijar da Ghana har ya zawa Senegal sassa ne na Musulunci inda ƴan mulkin mallaka na Ingila da Faransa suka yi iyakar ƙoƙarin su rusa shi. Ya ƙi ya bace, duk da yake an yi masa rotse.
Tarihi ya bayyana yadda wata ƙungiyar musulmi daga Mali ta zo Kano a ƙarni na sha biyar ta zauna ta fasa wucewa zuwa aikin Hajjin da ta fito yi.
Waɗannan mutane da ake kira Wangarawa suna cikin na farko-farko da suka yaɗa Musulunci a Kano.
Shehin malamin tarihi M.A. Al Hajj wani mutumin Sudan ya yi rubutu a kansu a mujallar Kano Studies wadda Jami’ar Bayero ta riƙa bugawa tun tana Abdullahi Bayero College wato tana ƙarƙashin Jami’ar Ahmadu Bello Zaria.
Zuwan Wangarawa muhimmi ne domin sun zo ne a matsayin ƙungiya wato da yawansu, ba irin zuwan shehin malami ƙwara ɗaya ba kamar babban malamin nan Al-Maghili Al Tilmisani wanda ya yaɗa musulunci a ƙasar.
Sauran ƙasashen Hausa su ma sun amfana da gudummawar malamai musamman Larabawa wajen yaɗa musuluncin.
Marigayi Farfesa Ahmad Kani Shehin tarihi ya ambaci wasu daga cikinsu da irin ayyukan da suka yi a ƙasar Katsina.
Daga baya malamai ƴan gida su ma sun bayar da tasu gudummwar kamar Muhammad Ibn Muhammad Al-Katsinawi al-Fulani wanda ya rasu a Misira a shekarar 1741 kafin ma a haifi Shehu Usman Danfodiyo.
Shi ne aka ce ya koyar da littafin Imam Malik- Muwaɗɗa a masallacin Manzon Allah SAW Madina.
Da tafiya ta yi tafiya sai ƙasar Hausa ta fara yi wa kanta kirari da kanta ta fuskar samar da malamai Hausawa.
Duk wanda ya ji an ambaci Wali Ɗan Marina ai ya ji sunan Bahaushe. Bahaushen ma na tsakiyar birni.
Duk da yake Turawa da ƴan barandarsu sun yi ƙoƙarin su nuna malamin ba wani malami ne na a–zo-a gani ba.
Tarihi da rubuce-rubacen da Farfesa John O. Hunwick da Dr Bobboi suka fitar a ƴan shekarun nan sun nuna cewa Wali Ɗan Marina babban malami ne da aka yi a birnin Katsina, kuma ya yi rubuce-rubuce da Larabaci da Hausa masu ƙayatarwa.
Sarkin Musulmi Muhammad Bello wato ɗan Mujaddadi Usman wanda ya fara mulkin ɗaya daga cikin biyu na Daular Usmaniyya bayan jihadi ya jinjina masa.
Ga irin abin da ya ce a game da shi a cikin littafinsa Infaq al Maysur.
Ya kira shi Al-ustaz, mai haskakawa kuma hanyar saman ilmi. Ya kuma ambaci wasu rubuce-rubucensa.
Waƙar da Wali Ɗan Marina ya yi a shekarar 1659, wato yau shekara 366 ke nan wadda ya yaba wa Sarkin Katsina na lokacin ta tabbatar da cewa ashe tun kafin 1659 gararuwan ƙasar Hausa da shari’a suke mulkinsu.
Waƙar ta yaba wa Sarkin ne domin ya sanya an kashe mutumin da ya yi iƙirarin cewa shi ne Annabi Isa.
Da malaman gari suka gaya wa Sarki mutumin ya yi ridda sai mai martaba ya bayar da umurni aka yi masa hukuncin da ya dace da na yin ridda su kuma jama’ar gari hankalinsu ya kwanta suka daina ƙorafi.
Zuwan Turawan mulkin mallaka ne aka yi ta yi wa Musulunci bugun kawo-wuƙa.
Turawa sun yi watsi da tsarin ilmin da suka iske. Sun rusa makarantu ta ruwan sanyi, sun wulaƙanta malamai da almajiransu.
Har bayan da suka kafa irin nasu makarantun waɗanda bahaushe ya kira na ƙarya na giri da yaudara wato Boko, sai malamin da ke koyar da addinin Musulunci da Larabci ya zama shi ne abin ƙyama.
Albashinsa ɗan tsito ne in an kwatanta shi da na mai koyar da lissafi ko Ingilishi, harshen da suka dauka shi ne harshen manzanni.
Kusan duk wata hukuma ta Musulunci sai da Turawa suka lalata ta suka ƙirƙiro tasu.
A yau ba ƙarƙashen mulkin mallaka muke ba. Tun shekarar 1959 Lardin Arewa ya samu ‘yancinsa.
Tun 1960 aka ba Nijeriya cin gashin kanta.
Saboda haka idan har jihohin Arewa sun ce sun bayar da hutu domin ɗalibai da malamansu su yi azumi cikin natsuwa to, ina yin haka ya saɓa wa cin gashin kan? Ko gashin kan na nufin a gasa wani ya ci?
Mun yaba wa Gwamnan jihar Bauchi da ya bi sahun ‘yanuwansa gwamnonin Kano da Katsina da Kebbi da ma waɗanda ban ambata ba a kan bada hutu domin azumi.
Azumi wani abu ne mai muhimmanci a rayuwar musulmi.
Soki burutsun da kungiyar kiristoci da wani ɗan amshinsu wai shi sakataren yaɗa labaran kungiyar ɗalibai suke yi duk shure-shure ne na ganin guguwar Musulunci da ta taso.
Idan zan tambayi ƙungiyar Kiristoci da ta ce wasu ƙasashen larabawa irin su U.A.E da Kuwait ba su ba da hutu domin azumi, wannan ya isa hujja kada a bayar a duk wata jiha ta musulmi?
Idan ma duk Larabawa sun ce ba su ƙara yin azumi ko salla ko ma in ɗebo ta da faɗi, su ce ba su ba addinin, sai Hausawa su ce su ma sun bar addinin?
Musulunci ba addinin Larabawa ne ba. Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wa sallam ba Annabin Larabawa ne ba.
Annabi ne ga duk duniya har da shugabannin ƙungiyoyin wasu addinai da za su gane.
Annabi Muhammad (SAW) rahama ne ga dukkan ‘yan Adam.
Azumi ginshiƙi ne a tsarin Musulunci. Duk wanda ya ƙi yin sa, ya yi wa kansa sakiyar-da–babu–ruwa.
Banda ɗauke nauyin zuwa makaranta to akwai wani abu ma da masu azumin ke buƙata.
Ƙasa ta bushe tun ma a cikin damina. A yayyafa wa talakawa ruwa su ji daɗin yin tarawihi.
Da ruwan ciki ake jan na rijiya. Mayunwaci bai iya daɗewa a salla.
Bari ma in yi waiwaye. In yi bi-ta-da-ƙulli.
Da jihohin Arewa na musulmi suke yin hutun Lahadi ba su zuwa aiki to don su je gidan uban wane ne?
A Katsina dai wannan ba zagi ne ba. A maye gurbinsa da hutun Juma’a ranar zuwa sallar Juma’a. Ranar Idi ce. Da ake yin hutu lokacin kirsimati ko wata Ista shi kuma hutun menene ne?
Har yanzu Turawan na nan ne? Idan aka ce a yi hutu lokacin da yara ke taya iyayensu aiki a gona za su gane hikimar wannan tunda abinci zai zo gida.
Lokaci ya yi da musulmi za su nuna wa duk wani mai shishshigi da takalar faɗa yatsa.
Tsarin dimokuraɗiyya tsari ne na masu rinjaye a majalisa, su yi doka ta dace da mutane ma fi rinjaye.
Ko musulmin Abiya ko Kuros Ribas sun nemi a ba ƴaƴansu hutu domin azumi?
A yi amfani da hutun a yi karatu, karatun ilmi na haƙiƙa.
Da ‘yan bokon da ke mulki sun je makarantar Ramadan sun sauke kamar yadda suka je sakandare suka gama, wasu ma har sun je jami’a da ba su zama ɓarayi a ofis ba.
Da ba a riƙa tallata su a talabijin sun yi laya da biliyoyi ba.
Da ba mu ga uba da dansa ba a gaban alkali ana cewa ku ɓarayi ne suna musu har lauyoyinsu na shedar zur.
A sha ruwa lafiya.
Adamu Ibrahim Malumfashi, Ahmadu Bello University, Zaria
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Adamu Ibrahim Malumfashi Arewa makarantu Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Duk Wani Kutse Na Isra’ila A Kudancin Kasar
Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya yi Allah wadai da keta hurumin kasarsa da Isra’ila ke yi a kudancin kasar, yana mai kira da a dauki tsauraran matakai kan duk wani kutse da sojojin mamaye za su yi a nan gaba a cikin Lebanon.
A lokacin wata ganawa da Kwamandan Rundunar Soja Rodolphe Heikal, Shugaba Aoun ya bayyana cewa dole ne Lebanon ta “fuskanci duk wani kutse da Isra’ila ta yi wa yankunan kudancin da aka ‘yantar don kare filayenmu da kuma tsaron ‘yan kasa.”
Wannan jawabi ya zo ne bayan harin da Isra’ila ta kai wa gundumar Blida, inda sojojin Isra’ila suka kashe wani ma’aikacin gundumar a lokacin wani hari da suka kai kan ginin ofishin karamar hukuma.
Daga baya, karamar hukumar ta tabbatar da cewa Ibrahim Salameh, wanda ya kwana a cikin ginin, ya yi shahada bayan da sojojin mamaya suka harbe shi. Aoun ya yi Allah wadai da kisan, yana mai cewa wani bangare ne na ayyukan “Isra’ila” kan fararen hula kuma ya zo ne ‘yan sa’o’i bayan taron da kwamitin da ke sa ido kan yarjejeniyar dakatar da fadan ya gudanar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci