Lamarin da ya haddasa daya daga cikin bala’i da mutane suka taba fadawa, inda sama da mutum miliyan 12 suka tsere daga gidajensu.

Darfur ta kasance yankin da nan da nan rikici kan tashi, inda RSF ke iko da yawancin yankin, in banda birnin el-Fasher wanda ya ci gaba da kasancewa a hannun rundunar sojin kasar da kawayenta.

Birnin el-Fasher ya sha ruwan bama-bamai a yayin da RSF ke kokarin kama shi.

A watan Afirilu RSF din ta sanar da shirin kafa gwamnati domin zama kishiya ga gwamnatin soji, abin da ya haddasa fargaba cewa hakan zai kai ga rarraba kasar.

Alawia ta ce yayin da fadan ya tsananta ake ta ruwan bama-bamai a watan da ya gabata, dole ita da mutanen gidansu suka tsere a kafa zuwa Tawila da ke yamma da el-Fasher.

‘Ya’yanta Marwan Mohamed Adam, mai shekara 21, ya gaya wa BBC cewa mayakan da ke da alaka da RSF sun ci zarafinsa a hanya inda suka lallasa shi da duka, har suka yi masa fashin ‘yan abubuwan da yake dauke da su.

Marwan ya ce ya tsira daga hannun gungun ne saboda ya yi musu karya daga inda ya fito.

Ya ce maharan sun debe matasan da suka gaya musu cewa daga el-Fasher suke suka je suka harbe su.

”Saboda haka a lokacin da suke yi min tambayoyi na ce musu daga Shakra nake – wanda zango ne a kan hanyar zuwa Tawila,” in ji shi.

“Za ka ji tsoro da fargaba, kana cikin tashin hankali, ka ji kamar ma ka riga ka mutu,” in ji Marwan mai shekara 21, a hirarsa da BBC, inda ya kara da cewa ya ga gawawwaki uku a kan hanya.

Wata matar, Khadija Ismail Ali, ta gaya wa BBC cewa “ga gawawwaki nan yashe a titi.”

Ta ce an kashe mutum 11 ‘yan gidansu a lokacin da ake yi wa el-Fasher ruwan makamai ta sama, kuma kananan yara uku sun mutum a lokacin tattakin da suka yi na kwana hudu daga birnin zuwa Tawila.

“Yaran sun rasu ne sakamakon kishirwa a hanya,” in ji Khadija.

‘Yanbindiga masu alaka da dakarun RSF sun kai hari kan kauyen iyalinta, el-Tarkuniya, a watan Satumba da ya wuce, inda kuma suka sace musu amfanin gona.

A lokacin suka tsere zuwa sansanin Zamzam inda ake fama da yunwa, daga nan kuma suka kara gaba zuwa el-Fasher yanzu kuma zuwa Tawila.

Kungiyar bayar da agajin lafiya – Alima ta ce ‘yanbindiga sun kwace filaye da gonakin yawancin iyalai a lokacin da suka kai musu hari.

Kungiyar ta kara da cewa wadanda suke zuwa Tawila, yawanci yara tuni sun kamu da cutar tsananin yunwa.

Alawia ta ce ‘yar uwarta ta jefar da dan abincin da suka yi guziri a lokacin da suke neman tsira daga hare-haren sama da suka gamu da su bayan sun wuce Shakra.

“Dan wani guntun wake ne da ya rage da dan gishiri muka rike a hannunmu domin ciyar da yara,” ta ce. Haka suke ta tattaki ba tare da ruwa ko abinci ba, har suka hadu da wata mata da ta ce musu za su iya samun ruwa a wani kauye da ke kusa.

Tawagar tasu ta tashi cikin dare domin ci gaba da tafiya zuwa wannan kauye, to amma ba su san cewa ashe suna yanki ne da ke karkashin ikon mayakan RSF ba.

“Mun gaishe su, amma kuma ba su amsa mana ba. Sun umarce mu, mu zauna a kasa, suka bincike kayanmu,” in ji Alawia.

Mayakan sun karbe kudin da muke rike da su fan 20,000 (na Sudan) (daidai da Dala 33), gaba daya kudin da iyalan ke da shi, tare da tufafi da takalman da suke dauke da su.

“Takalmana ba su da kyau amma duk da haka suka kwace su,” in ji Alawia.

Ta kara da cewa mayakan RSF sun ki su ba su ruwa, saboda haka suka ci gaba da tafiya har sai da suka kai kauyen el-Koweim.

A can suka hangi wata rijiya da mayakan RSF ke tsare da ita.

“Mun roke su, su ba mu ruwa akalla ko don yaron nan maraya, amma suka ki,” in ji Alawia.

Ta kara da cewa ta matsa domin ta je rijiyar amma mayakan suka mangare ta.

Iyalan sun ci gaba da tafiya haka a galabaice cikin kishirwa har sai da suka kai Tawila, inda isar su ke da wuya sai Alawia ta zube kasa, nan da nan aka garzaya da iya asibiti.

An sallame ta bayan an yi mata magani.

Haka shi ma yayanta Marwan an yi masa maganin raunukan da ya ji a lokacin da mayakan suka yi masa duka.

Alawia ta ce daga nan ne suka shiga neman dangin wannan yaron da suka ceto, bayan sun same su, suka danka musu shi.

A yanzu Alawia da iyalanta na zaune a Tawila, inda wasu iyalai suka karbe su, suka ba su masauki a gidansu.

“Yanzu dai rayuwa mun gode wa Allah, amma muna da fargabar yadda za ta iya kasancew

a a nan gaba,” Alawia ta shaida wa BBC.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: kara da cewa zuwa Tawila

এছাড়াও পড়ুন:

Sheikh Na’im Kasim Yace Kare Kasa Baya Bukatar Izini Daga Wani

Sheikh Na’in Kasem shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa kungiyar bata bukatar Izini don kare kasar Lebanon daga makiyanta. Yama fadar haka ne ga wanda suka cika kunnen duniya kan cewa dole ne kungiyar ta mika makamanta ga gwamnatin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto Sheikh Kasim yana fada a wani jawabin da ya gabatar a ranakun Ashoora na Imam Hussain (a) ta kafar Bidiyo. Ya kuma kara da cewa wadanda suke maganar kungiyar Hizbullah ta mika makamanta ga gwamnatinsa kasar, ya fiye masu sauki su fadawa yan mamaya su fice daga kasar Lebanon su kuma dakatar da hare-haren ta’addancin da suke kawo mata.

Ya kara jaddada cewa kungiyarsa zata ci gaba da rike makamanta sannan bata bukatar izini daga wani don kare-kasar Lebanon daga makiyanta.

Malaman ya kara da cewa, wani mai hankali ne zai amince ya mika makamansa a dai dai lokacinda mikiyan kasar Lebanon suna ci gaba da kawo hare-hare kan  kasar a ko wace rana. Maimakon su yi allawadai da mai shisgigi sai suka sa idanso a kan makaman hizbulla.

Yace idan wasu a kasar Lebanon sun zami mika kai ga HKI da Amurka to wannan zaminsa ne, amma mu ba masu mika kai ga makiyammu ne ba. Shi’arimmu shi ne {bama daukar kaskanci}.

Ya ce kun yi kuskure da kuka dogara da karfin wasu don takurawa masu gwagwarmaya. Masu gwagwarmaya basa jin tsoron makiya. Ya ce manufarmu ita ce yantar da kasa daga hannun makiya itace manufarmu.

Ya kammala da cewa makiyarmu it ace HKI, dole ne ta fice daga kasar Lebanon, kuma gwagwarmaya ita ce hanya tilo ta korar yan mamaya daga kasarmu. Idan kuma wani yana ganin akwai wata hanya korar makiya daga kasarmu a shirye muke mu shiga tataunawa da shi, ya gamsar damu a kan shirin nasa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Taron Ashura Ya Zama Lamari Mafi Girma Da Cinkoson Jama’a, Inda Masu Ziyara Daga Sassan Duniya Suka Isa Karbala
  • Babban Mufti Na Masarautar Oman Ya Yi Kakkausar Suka Kan Masu Son Kulla Alaka Da H.K.Isra’ila
  • Ma’aikatan MDD Masu Kula Da Ayyukan Makamashin Nukliya Na Kasar Iran Su Fice daga Kasar
  • Sheikh Na’im Kasim Yace Kare Kasa Baya Bukatar Izini Daga Wani
  • Shugaban Amurka Yace Yana Jiran Amsar Hamas Cikin Sa’o’i 24 Masu Zuwa Don Tsagaita Wuta Na Kwanaki 60
  • Haɗarin Da Ke Ƙunshe Da Jin Ɓangare Ɗaya Na Labari
  • Shugaban Amurka Yace Yana Jirin Hamas Cikin Sa’o’i 24 Masu Zuwa Don Tsagaita Wuta Na Kwanaki 60
  • Filato: Mahara sun cire hannun matashi a kan hanyar komawa gida daga jana’iza
  • Kwamandan Sojojin Iran Ya Ziyarci Gidan Babban Jami’in Sojin Kasar Da Ya Yii Shahada Lokacin Yakin Baya-Bayan Nan