2025-06-16@11:29:31 GMT
إجمالي نتائج البحث: 405
«Watsi Da Korafi»:
Gwamnatin kasar Iran ta yi kakkausar suka ga gwamnatin HKI kan hare-haren da ta kaiwa wani sansanin yan gudun hijira a gaza inda ta kashe ko takai mutanen da dama ga shahada, daga ciki har da mata da yara jarirai. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran...
Wannan rangwamen farashin duk da cewa ba a hukumance yake ba, amma ya bai wa kwastomomin Dangote damar siyar da mai akan farashi mai rahusa a tsakanin Naira 830 zuwa N835 kan kowacce lita. Wannan nasarar ta zo ne makonni kadan bayan da matatar ta yi ragin farashi sau biyu a jere a cikin...
Sojojin HKI sun ci gaba da kai hare hare kan birane da garuruwan yankin yamma da kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, hare-haren jiya sum sun fi maida hankali ne a garin Tulkaram da kuma sansanin yan gudun hijirar yankin A wannan karomma sojojin HKI sun bada umurni ga...
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana fatan ganin kasashen India da Pakistan sun kai zuciya nesa, tare da warware sabani ta hanyar shawarwari da tattaunawa, kana su gujewa sake rura wutar tashin hankali. Wang ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, yayin tattaunawa ta wayar tarho da mashawarcin gwamnatin India ta fuskar...
Manistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da tokwaransa na kasar Saudiya Faisal Bin Farhan a birnin Jeddah inda bangarorin biyu suka tattauna kan al-amuran da suka shafi yankin, musamman batun Falasdinawa da kuma halin da suke ciki musamman a yankin gaza. Inda HKI take kashesu da yuwan, sannan tana ci gaba da...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Dole ne duniya ta dauki matakin kalubalantar laifukan ‘yan sahayoniyya da magoya bayansu kan zaluncin Gaza Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, yayin da yake karbar bakwancin dimbin ma’aikata a yau Asabar, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan “Makon ayyuyka da Ma’aikata”...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Ce Kafa Hujja Da ‘Yan Tawaye Kan Iran Yankewar Kauna ce Ga Makiyanta
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Amfanin da fira ministan gwamnatin mamaya ya yi da ƙungiyar ta’addanci babbar alama ce ta cikakkiyar yanke ƙauna Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Matakin da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dauka na yi amfani da wata karkatacciyar kungiyar...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Allah Wadai Da Kai Hari Kan Ofishin Jakadancin Kasarsa A Kasar Sweden
Ministan harkokin wajen kasar Iran yayi Allah wadai da harin da aka kai kan ginin ofishin jakadancin kasarsa da ke Stockholm na kasar sweden Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi Allah wadai da harin da aka kai ofishin jakadancin Iran da ke Stockholm tare da yin kira ga gwamnatin Sweden da ta dauki...
Shugaban kungiyar ya yi magana Ibrahim Yusuf Babayo,Shugaban kungiyar Miyetti Allah masu kiwon dabbobi na kasa ya bayyanawa jaridar karshen mako cewar dukkan hare- haren da ake kaiwa dabbobin da kuma kashesu an sanar da jami’an tsaro daban- daban,da suka hada da Kwamanda na rundunar soja ta,3 kuma kwamandan Operation Safe Haben (OPSH), Manjo- Janar...
Burin Arsenal na lashe gasar UEFA a karon farko a tarihinta ba zai cika a wannan shekarar ba, sakamakon rashin nasarar da ta yi a hannun PSG a wasan zagayen na kusa da na karshe, Arsenal ta buga wasan karshe a UEFA sau daya a shekarar 2006 tsakaninta da Barcelona. Daga kanmu, magana ta...
Rundunar sojan Ruwan Amurka ta sanar da cewa; Jirgin sama samfurin F-18 wanda kudinsa ya kai dalar Amurka miliyan 67 ya fadi akan jirgin dakon jiragen ruwa na ” USS Harry Truman” a tekun “Red Sea”. Jaridar ” Washington Post” ta buga labarin dake cewa; Jirgin ta fado ne a lokacin da yake kokarin sauka...

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Yin Allah Wadai Da Hare-Haren ‘Yan Sahayoniyya Kan Kasar Yemen
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da zaluncin ‘yan sahayoniyya a kan kasar Yemen Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri da sojojin yahudawan sahayoniyya suka kai tashar jiragen ruwa na Hodeidah da sauran ababen more rayuwa na kasar Yemen, yana mai...

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Sha Alwashin Mayar Da Martani Cikin Gaggawa Kan Duk Wani Hari Kan Kasarta
Jamhuriayar Musulunci ta Iran ta sha alwashin mayar da martani cikin gaggawa ga duk wani kasadan ‘yan Sahayoniyya da Amurka kan kasarta Jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya jaddada cewa: Duk wani kasadan harin soji da Amurka ko wakilliyarta gwamnatin ‘yan sahayoniyya suke yi, ko...

Sharhin bayan Labarai: Ci Gaban Harkokin Kasuwanci Tsakanin Iran Da Kasashen Waje Duk Tare Da Takunkuman Kasashen Yamma
Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da “Bankasar tattalin arzikin Iran duk tare da takunkuman tattalin arziki masu tsanani wadanda kasashen yamma musamman Amurka suka doramata, wanda ni tahir amin zan karanta. ////…A dai-dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka take barazanar zata hana sayan danyen man fetur daga kasar Iran kwatakwata,...

Iran Ta Jaddada Cewa: Kungiyoyin Gwagwarmaya Ba Su Karbar Umarni Daga Wani Bangare, Gashin Kansu Suke Ci
Iran ta mayar da martani kan zargin da ake mata game da alakar ta da Yemen tana cewa; Taimakon da Yemen ke yi wa Falasdinu hukunci ne mai cin gashin kansa Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da wata sanarwa dangane da zargin da ake yi wa Iran dangane da alakar da ke tsakaninta...
Ministan Tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Za su mayar da martani mai tsanani da karfi kan duk wani ta’addanci da kasarsu za ta fuskanta Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, yayin da yake mayar da martani ga barazanar Amurka, ya tabbatar da cewa Iran za ta mayar da martani mai karfi tare...
Shugaban kamfanin Sarrafa Sinadaran man fetur na kasar Iran ya bayyana cewa kasarsa tana son da kasance cikin wadanda zasu gina kamfanin sarrafa sinadaran man fetur na jumhuriyar Nijer, iran tana son ta taimaka wajen samar da takin zamani ga kasashen Afirka. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya nakalto Hassan Abbaszadeh yana fadar...
Duk da nasarorin da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta samu a kakar 2023/24 na lashe kofuna 5, ciki har da Kofin Zakarun Turai, amma tana fuskantar ƙalubale a kakar bana, inda ake ganin da wahala ta iya lashe wani kofi bayan Super Cup da ta ci a farkon kaka, da ta ƙwace a...
Dakarun Yeman ta sanar cewa ta kai hari filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion na Falasdinu, a wani mataki na nuna goyon bayansu ga Falasdinawa da ke fama dake fusnkatar mamaya, zalinci da kisan kare dangi daga Isra’ila. Kakakin rundunar sojin Isra’ila ya ba da rahoton wani sabon hari da makami mai...
A gaskiya wannan matsalar takan faru ne a tsakanin ma’auratan da basa son juna sosai, hadin gida (auren dangi), ko babbar matsala na karya alkawari tsakaninsu, abu ne kuma wanda bai kamata ana yi wa yara hukuncin da ba laifinsu, wannan a bayyane cin zali ne da shirin maida yaro kangarerre. Ba shi da wani...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya yaba da sadaukarwar da ‘yan jarida suka bayar da suke ba da labaran irin wahalhalun da Falasdinawa ke ciki A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter na ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana jin dadinsa ga...
A cewar hukumar, kamfanonin mai da iskar gas da ke aiki a kasar sun samar da iskar gas na naira biliyan 22.3 daga ayyukansu na teku. Hukumar ta lissafa asarar ta amfani da Babban Bankin Nijeriya (CBN) na musayar canji na naira 1,520 zuwa dala daya. Hukumar kula da muhalli ta lura cewa...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce duk wani ci gaba da za’a samu a tattaunawa da Amurka ya dogara ne da muhimmancin da Washington ta ba tattaunawar. A wata tattaunawa ta wayar tarho da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, Araghchi ya ce barazana da kuma takunkumin da Amurka ke kakaba wa...
Barcelona ce ta yi nasara a wasan na El Clasico da cin 3-2, sannan ta lashe Copa Del Rey na 32 jimilla ranar Asabar. Daga baya Rudiger ya nemi afuwa, sai dai hukuncin laifin da dan wasan tawagar Jamus ya aikata, za a iya dakatar da shi daga buga wasa hudu zuwa 12, amma sakamakon...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Tattauna Da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kan Zaman Tattaunawan Amurka Da Iran
Ministan harkokin wajen Iran ya sanar da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ci gaba da ake samu a shawarwari makamashin nukiliyar Iran tsakanin Amurka da Iran amma ana buƙatar gaskiya da hangen nesa daga ɗayan ɓangaren A yammacin jiya Juma’a ne ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araqchi ya tattauna ta wayar tarho...

Ranar Maleriya Ta Duniya: ‘Yan Nijeriya Na Kashe Naira Tiriliyan 1.156 Duk Shekara Wajen Sayen Magunguna
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa, duba mara lafiya guda daya tak da ke dauke da cutar Maleriyar da ba ta yi karfi sosai ba a asibitin gwamnati, na lashe kimanin Naira 17,000, tsakanin ganin likita, yin gwaje-gwaje da kuma magunguna. Wadannan kudade sun kai kimanin Naira tiriliyan 1.156 da ake kashewa a kan wannan...

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce Kasar Oman Ce Ta Bukaci Dage Zaman Tattaunawan Iran Da Amurka
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: An dage zaman tattaunawan Iran da Amurka ne bisa shawarar kasar Oman Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi nuni da cewa: Ministan harkokin wajen kasar Oman ne ya sanar da sauyin lokacin zaman tattaunawan ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka,...

Hamas Ta Yi Allah Wadai Da Matsayin Amurka Na Goyon Bayan Haramta Hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa Ta UN
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramtacciyar kasar Isra’ila kan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa...
Kakakin kwamitin tsaron kasa a majalisar shawarar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; ” Ya zuwa yanzu ba za mu iya yin hukunci akan dalilan da su ka haddasa fashewar abubuwa a tashar ruwa ta Shahid Raja’i ba, amma za mu iya cewa babu hannu waje a ciki. Kakakin kwamitin tsaron kasar ta Iran Ibrahim...
Gwamnan lardin Hormozgan (mai hedikwata a Bandar Abbas), Mohammad Ashouri, ya ce wani bangare na lamarin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’i ya faru ne sakamakon keta sanarwar adana kayayyaki ne, wani bangaren kuma na da alaka da sakaci da rashin kulawa (a wajen ajiya). AShouri, wanda ya bayyana ta hanyar faifan bidiyo a wata...
Wannan ya sa wasan yau zai zama mai ɗaukar hankali, domin kowanne daga cikinsu na burin ɗaukar kofin a karo na farko, domin a dakatar da yawan dariyar da ‘yan adawa ke musu. A zagayen rukuni da suka haɗu a farkon wannan kakar, Arsenal ta lallasa PSG da ci 2-0. Kocin Arsenal yanzu, Mikel Arteta,...
Shugaban kasar Iran ya nuna murnarsa da yin maraba lalai da masu zuba hannun jari daga kasashen waje a Iran Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana Iran a matsayin dandalin da ta dace wajen zuba hannun jari da gudanar da harkar kasuwanci, yana maraba da masu zuba hannun jari na kasashen waje da ‘yan...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jadadda Cewa: Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kan Iran Zai Fuskanci Mayar Da Martani
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Duk wani harin wuce gona da iri kan Iran zai fuskanci mayar da martani daidai da shi cikin gaggawa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa Iran na da kwarin gwiwa kan iya dakile duk wani yunkuri da wasu bangarorin ke yi na kawo cikas...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Ci Gaba Da Killace Gaza Da Kashe Mutane, Laifi Ne Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ci gaba da killace Gaza da kuma kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, laifi ne da ba a taba yin irinsa ba a tarihin dan Adam A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badar Abdel Ati a yammacin jiya Lahadin...
A cewarsa, tuni aka shirya wuraren kwana da abinci ga maniyyatan a kasar Saudiyya. Abdulkadir ya tabbatar da cewa, ana shirye-shirye, inda za a yi alluran rigakafi a ranar 28 ga Afrilu, za a raba tufafi a 30 ga Afrilu, sannan kuma za a raba jakunkuna a ranar 1 ga Mayu. Ya kara...
Shugaban hukumar makamshin Nujkliya ta MDD ya zanda da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi kan al-amuran da suka shafi shirin nukliyar kasar Iran da kuma tattaunawar da ake gudana tsakanin ta da Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a tattaunawa ta wayar tarho tsakanin jami’an guda biyu a...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne a kawar da ta’addanci ta hanyar hadin kan kasashen yanki Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin ta’addancin da aka kai a birnin Pahalgam na kasar Indiya, tare da nuna alhini da juyayinsa ga gwamnati da al’ummar kasar Indiya, yana...
Sun ƙara da cewa, “Samun shugabannin matasa masu jajircewa a wannan yankin babbar albarka ce ga al’ummarmu. “Hakan na nuna mana cewa akwai kyakkyawar makoma ta ci gaba a Arewa gaba ɗaya.” Sannan sun bayyana cewa sun aike wa ƙungiyoyinsu a dukkanin jihohi 19 na Arewa goron gayyata domin naɗin sabbin muƙamai a Masarautar Daura....

Saboda In Nuna Wa Duniya Asalin Al’adar Bahaushe Ya Sa Na Fara Fina-finan Turanci A Arewacin Nijeriya – Jammaje
A wata hira da Jammaje ya yi da rfI Hausa an jiyo shi ya na cewa sunana Kabiru Musa Jammaje haifaffen Jihar Kano, nayi karatu a Bayero Unibersity da ke birnin Kano inda na karanci English kafin in tafi kasar Amurka domin zurfafa karatu, bayan na dawo gida Nijeriya kuma na shiga Jami’ar koyo daga...
Ministan harkokin cikin gidan Iran Askandar Mumini wanda ya kai Ziyara zuwa wurin da gobarar ta tashi ya sanar da cewa adadin wadanda su ka jikkata sun kai 750 da kuma wadanda su ka rasa rayukansu zuwa 14. Sai dai kuma daga baya ma’aikatar shari’a ta kasar Iran din ta ta sanar da karuwar wadanda...
“Abin takaici ne ganin yadda jami’an CJTF biyu da aka kashe a ranar Juma’a, sannan kuma wasu mutane 10 da suka je daji neman itace aka kashe su yau. “Mun riga mun birne mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, kuma an kwashe waɗanda suka ji rauni zuwa Maiduguri domin nema musu kulawar likitoci,” in...

Iran ta Bayyana cewa: TattaunawarMuscat Wata Dama Ce Ta Samun Zaman Lafiya Kan Batutuwan Masu Sarkakiya
Mai ba da shawara ga Jagoran juya juya halin Musulunci kan harkokin siyasa ya bayyana cewa: Tattaunawar Muscat wata dama ce ta samun zaman lafiya kan batutuwa masu sarkakiya Ali Shamkhani mai ba Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara kan harkokin siyasa ya yi tsokaci kan tattaunawar ba na kai tsaye ba da ake yi...
Gwamnatin Jihar Kano ta gano matsaloli a cikin tsarin albashin ma’aikatan ƙananan hukumomi, inda aka gano ma’aikata 247 da suka yi ritaya ko kuma sun mutu, amma suna ci gaba da karɓar albashi. Wannan bayani ya fito ne daga cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Musa Muhammad, ya fitar. A...
Kungiyar kwallon kafa ta PSG – wadda tuni ta lashe gasar League 1 ta Faransa na daya daga cikin kungiyoyin da ake ganin za su lashe gasar Zakarun Turai ta bana saboda karfin da tawagar take da shi sannan kuma kungiyar a gine take hadi da kwararren mai koyarwa, Luis Enrikue, tsohon kociyan Barcelona da...
Karo na hudu kenan da Arsenal ta kara da Real a kofin Zakarun Turai, inda ta ci uku aka yi canjaras daya. A ranar 29 ga watan Afrilu Arsenal za ta karbi bakuncin PSG a wasan farko, kafin a buga na biyu mako daya bayan haka. Kungiyar dai ita ce a mataki na biyu a...
Bayan ya sake daga sabowar tutar kasar Siriya a cibiyar MDD da ke birnin NewYork ministan harkokin wajen kasar Siriya Asaad Al-shaibani, ya gabatar da jawabi a gaban kwamitin tsaro na MDD a jiya jumma’a inda ya roki kwamitin ya dagewa kasarsa takunkuman tattalin arziki wadanda aka dorawa gwamnatin da ta shude. Jaridar Middle eart...
Gwamnan ya bayyana cewa ba za a yi amfani da kudin al’umma ba ga mutanen da ba za su iya kula da mahajjata yadda ya kamata ba. Gwamna Radda ya kara da cewa ya yi taro da shugabannin kananan hukumomi guda 34 domin tabbatar da cewa malaman da suka cancanta ne kadai aka zaba...

Kasar Sin Ta Goyi Bayan Rawar Da Hukumar IAEA Ke Takawa Wajen Warware Batun Nukiliyar Iran Ta Hanyar Diflomasiyya
Li ya kara da cewa, Sin da Rasha sun bayyana goyon baya ga Iran wajen karfafa tattaunawa da hadin gwiwa da hukumar IAEA. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...

Muscat Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Kama Hanyar Zuwa Birnin Domin Ci Gaba Da Tattaunawa Da Amurka
Ministan harkokin wajen Iran ya nufi birnin Muscat na kasar Oman a yau domin gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya sanar da cewa: A yau ne ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya nufi birnin Muscat na kasar Oman a karkashin jagorancin tawagar diflomasiyya...

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Yi Gargadin Munanan Sakamakon Da Zai Biyo Bayan Kashe Falasdinawa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran yayi kashedin kan illar ci gaba da killace Gaza da kuma hare-haren ta’addancin ‘yan mamaya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Ci gaba da rashin hukunta ‘yan sahayoniyya kan kisan gillar da suke yi a zirin Gaza da Gabar yammacin kogin Jordan, da kuma mamayar wasu yankunan...