Aminiya:
2025-12-01@12:33:04 GMT

Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba sai sun yi tuba na gaskiya — Radda

Published: 15th, October 2025 GMT

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da ’yan ta’adda ba waɗanda ke kashe mutane ba gaira ba dalili.

Gwamnan, ya bayyana hakan ne a yau a wajen bikin yaye sabbin jami’an tsaron cikin gida (Community Watch Corps – CWC) guda 100, a karo na uku da aka gudanar a Katsina.

Gwamna Buni ya ware N5.8bn don biyan haƙƙin tsoffin ma’aikata a Yobe Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Radda, ya karyata rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai suka yada cewa gwamnatinsa tana tattaunawa da ’yan bindigar da ke ɓoye a dazuka.

A cewarsa: “Babu wata tattaunawa ko sasanci da gwamnati ke yi da ’yan ta’adda. Wadannan labarai ƙarya ne, kuma manufar gwamnati ita ce kawo ƙarshen ta’addanci, ba yin sulhu ba.”

Sai dai ya ce, gwamnati za ta iya rungumar zaman lafiya idan waɗannan mutane sun yi tuba na gaskiya, tare da miƙa wuya, suka daina zubar da jini.

Gwamna Radda, ya bayyana cewa horar da jami’an CWC wani ɓangare ne na sabuwar dabarar gwamnati ta inganta tsaro, musamman a yankunan karkara da suka fi fama da hare-haren ’yan ta’adda.

Tun bayan ƙaddamar da Katsina jami’an tsaron a shekarar 2023, an horar da dubban matasa sama da 2,400 daga sassa daban-daban na jihar.

Wadannan jami’ai na aiki tare da ’yan sanda, sojoji, da jami’an Sibil Difens, don taimakawa wajen samun bayanan sirri da hana hare-haren ’yan ta’adda.

Gwamnan, ya ce horar da waɗannan jami’ai zai taimaka wajen kawo ƙarshen satar mutane da hare-haren ’yan bindiga, tare da tabbatar da zauna lafiya a Jihar Katsina.

Ya kuma yi kira ga al’umma su bai wajami’an tsaro haɗin kai, su rika bayar da bayanai domin ganin an samu nasara a yaki da ta’addanci.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Gwamna Radda hare hare yan ta adda

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Garin Eruka Na Jihar Kwara

Daga Ali Muhammad Rabi’u 

’Yan bindiga kimanin guda huɗu dauke da makamai sun kai hari a garin Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a jihar Kwara, inda suka sace wani manomi mai suna Mista Aasaru.

Rediyon Najeriya ya ruwaito  cewa wannan hari shi ne na biyu da aka kai wa garin Eruku cikin wata guda, kuma ya faru ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin tarayya ta samu ’yantar da mambobin Cocin Christ Apostolic Church (CAC) 38 da aka yi garkuwa da su a yankin.

Majiyar da ta yi magana da Rediyon Najeriya ta ce ’yan bindigar sun farmaki Aasaru ne a wani daji da ke kan hanyar Koro.

Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ’yan sandan jihar Kwara, Toun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarta, jami’an ’yan sanda daga sashin Eruku sun karɓi korafi a ranar Lahadi cewa wasu mutane huɗu dauke da makamai sun kutsa wata gona a kan hanyar Koro, Eruku, inda suka sace wani Mista Aasanru mai shekaru 40.

Ejire-Adeyemi ta ce ana cigaba da ƙokari wajen ganin an kubutar da manomin da aka sace.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Garin Eruka Na Jihar Kwara
  • ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa  masu ibada a Kogi 
  • N750,000 kuɗin bikin yaye ɗaliban Jami’ar MAAUN ya tayar da ƙura a Kano
  • ’Yan bindiga sun sace amarya da ƙawenta 14 a Sakkwato
  • Sojoji sun ceto mutum 7 da ’yan bindiga suka sace a Kano
  • ’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano
  • Likitoci sun gindaya sabon sharaɗi bayan janye yajin aiki
  • Muna buƙatar taimakon ƙasashen waje kan tsaro a Najeriya — Obasanjo
  • Yadda aka horar da mata 100 sana’o’in dogaro da kai a Gombe
  • Kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi Ta Soki Shirin Donald Trump Na Bayyanata A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda