Kaso 16 na ’yan Najeriya ne kawai ke da wajen wanke hannu — UNICEF
Published: 16th, October 2025 GMT
Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), ya bayyana cewa kashi 16 cikin 100 na ’yan Najeriya ne kawai ke da wajen wanke hannu mai tsafta a gidajensu.
Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Chisom Adimorah ce, ta bayyana haka a ranar Laraba yayin bikin Ranar Wanke Hannu ta Duniya ta 2025, wanda Ma’aikatar Ruwa da Tsaftar Muhalli ta Tarayya ta shirya.
Adimorah, ta nuna damuwarta kan wannan matsala, inda ta ce duk mutane biyar cikin shida a Najeriya ba su da waje da za su iya wanke hannunsu yadda ya kamata.
Ta yi kira ga gwamnati, ƙungiyoyi, kamfanoni da kuma ’yan ƙasa su haɗa kai wajen inganta tsaftar hannu a ƙasar.
Ta kuma tabbatar da cewa UNICEF za ta ci gaba da taimaka wa Najeriya wajen inganta manufofin tsaftace muhalli domin su dace da sabbin ƙa’idojin WHO da UNICEF kan tsaftar hannu.
Ministan Ruwa da Tsaftar Muhalli, Injiniya Joseph Utsev, ya bayyana muhimmancin wanke hannu wajen kare lafiyar jama’a, inda ya ce “wanke hannu na ceton rai tare da kariya daga barazana.”
Utsev, ya ƙara da cewa ‘Taswirar Najeriya ta Tsaftar Hannu’ wadda aka ƙaddamar a shekarar 2022, ita ce har yanzu ke jagorantar ƙoƙarin wayar da kan jama’a kan wanke hannu a faɗin ƙasar nan.
Ya jaddada cewa dole ne a fara koyar da wanke hannu tun daga makarantar firamare domin yara su saba da wannan ɗabi’a tun suna ƙanana.
A nasa jawabin, Aghogho Gbetsere, wanda ya wakilci Ministan Muhalli, ya shawarci ’yan Najeriya su riƙa wanke hannunsu a kai a kai, inda ya ce hakan na iya rage hatsarin kamuwa da cututtukan gudawa da kashi 50 da kuma cututtukan da suka shafi numfashi da kashi 25.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan Najeriya wanke hannu wanke hannu
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Yadda Cire Darasin Lissafi Zai Taimakawa Dalibai Shiga Jami’a
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Cire darasin Lissafi daga jerin wajibcin da ake buƙata domin samun shiga manyan makarantu ya samu karɓuwa daga wasu ɓangarori na dalibai da malamai. Wasu dalibai sun nuna farin ciki da wannan mataki, suna ganin zai sauƙaƙa musu damar samun shiga jami’a da sauran manyan makarantu ba tare da shan wahalar lissafi ba.
Sai dai wasu masana sun bayyana cewa, duk da wannan sauƙin, ya kamata a yi taka-tsantsan saboda lissafi na taka muhimmiyar rawa wajen gina tunani da fahimtar ilimin fasaha, kimiyya da injiniya. Wannan ya sa ake tambaya ko cire lissafi daga wajabcin shiga manyan makarantu ba zai iya rage ingancin dalibai a nan gaba ba.
NAJERIYA A YAU: Shin Babu Wata Hanyar Magance Matsalolin ASUU Ne Sai Yajin Aiki? DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne?Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan