Majalisar Dattawa ta amince da Amupitan Shugaban INEC
Published: 16th, October 2025 GMT
Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da Joash Ojo Amupitan a matsayin sabon shugaban Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta INEC, bayan tantancewa.
Sabon shugaban Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta INEC, Joash Ojo Amupitan dai ya halarci zauren Majalisar Dattawan Najeriya domin zaman tantance shi a yau Alhamis ne.
Amupitan ya halarci zauren Majalisar tare da rakiyar Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Ododo da wasu jami’an gwamnati.
Za a kafa kamfanin ƙera kayan sola a Kano Kashi 16 na ’yan Najeriya ne kawai ke da wajen wanke hannu — UNICEFDa misalin ƙarfe 12:50 na rana ne, mai baiwa shugaban Ƙasa shawara kan Harkokin Majalisar Dattawa (Majalisar Dattawa), Sanata Abubakar Lado ne ya shigar da sabon shugaban INEC zuwa zauren majalisar dattijai, kuma tuni ya zauna gabanin fara aikin tantance shi.
An bar Amupitan ya shiga zauren majalisar ne bayan shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele ya bayar da umarnin a samar da doka ta 12 domin ba wa baƙi damar shiga zauren majalisar, kuma shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Abba Moro ya mara masa baya.
Matakin na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya aike wa majalisar wasiƙar buƙatar tantance shi.
A makon da ya gabata ne dai majalisar magabatan ƙasar ta amince da naɗin Farfesa Amupitan a matsayin wanda zai jagoranci hukumar zaɓen INEC.
Bayan tantancewa da amincewar majalisar dattawan, Shugaba Tinubu zai rantsar da shi a matsayin shugaban hukumar ta INEC.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Majalisar Dattawa Majalisar Dattawa zauren Majalisar zauren majalisar Majalisar da
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Bude Bikin Baje Kolin Kasuwanci Na Kasa Da Kasa Na 138 A Guangzhou October 15, 2025
Daga Birnin Sin Mujallar “Qiushi” Za Ta Wallafa Muhimmiyar Kasidar Shugaba Xi Jinping Kan Muhimman Shawarwari Hudu Da Ya Gabatar October 15, 2025
Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles October 15, 2025