Kungiyar Hamas Ta Yi Maraba Da Matakin Wasu Kasashen Turai Na Nuna Kyamarta Zaluncin Isra’ila
Published: 30th, August 2025 GMT
Kungiyar Hamas ta yi maraba da Allah wadai da kasashen Turai 6 suka yi da matakin wuce gona da iri da gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka kan Gaza
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi marhabin da matakin da wasu kasashen Turai shida suka dauka na yin Allah wadai da wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka yi a kan birnin Gaza, tare da la’akari da shi a matsayin wani muhimmin mataki da ke kara habaka matsayar kasashen duniya na neman kawo karshen wuce gona da iri kan al’ummar Falastinu.
Kasashen da ake magana a kai su ne: Iceland, Ireland, Luxembourg, Norway, Slovenia, da Spain. Ministocin harkokin wajensu sun bayyana rashin amincewarsu da hare-haren wuce gona da iri kan Gaza, inda suka jaddada bukatar kawo karshen take-taken gwamnatin mamayar Isra’ila.
A cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar a yau Asabar, kungiyar ta Hamas ta ce: Wadannan matsayi na nuna rashin amincewa da laifuffukan da yahudawan sahayoniyya suka aikata, tana mai jaddada cewa: Kasashen Turai da ma duniya masu ‘yanci ne ke da alhakin fassara wadannan tofin Allah zuwa wasu matakai na zahiri da kuma daukan matakan ladabtarwa da za su dakatar da aikata laifukan kisan kare dangi, yunwa, da kuma keta dokokin kasa da kasa.
Tun a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023, yahudawan sahayoniyya tare da goyon bayan Amurka, suke ta aiwatar da kisan kiyashi a zirin Gaza, da suka hada da kisa, yunwa, barna, da kuma tilasta gudun hijira, tare da yin watsi da kiraye-kirayen kasa da kasa da umarnin kotun duniya na dakatar da shi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasar Denmark Tana Goyon Bayan Dakatar Da Yarjejeniyar Kasuwacin Da Isra’ila August 30, 2025 Moroko: Zanga-Zangar Rashin Amincewa Da Kisan Kiyashi Da Kakaba Yunwa A Gaza August 30, 2025 Guinea: An Fara Tattaunawa Kan Zaben Raba Gardama Na Sabon Kundin Tsarin Mulki August 30, 2025 Turkiyya Ta Bukaci A Dakatar Da Isra’ila (HKI) Daga Majalisar dinklin duniya August 30, 2025 Iran: IRGC Sun Kama Ma’aikatan Mosad A Arewa Maso Gabacin Kasar August 30, 2025 Iran Ta Yi Watsi Da Shirin ‘SnapBack’ Na Kasashen Turai August 30, 2025 E3 sun gindaya sharudda 3 kan dakatar da dawo da takunkuman MDD a kan Iran August 30, 2025 Amurka ta hana izinin shiga kasarta ga shugaban Falastinawa don halartar taron MDD August 30, 2025 Rwanda ta dauki bakin haure kashi na farko da aka kora daga Amurka August 30, 2025 Jami’in Sojin Isra’ila: Masu Tunanin Hizbullah Ta Yi Rauni Suna Mafarki Ne August 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Kasashen Turai
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces
Gwamnatin Sudan ta ce: Babu batun sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces na kasar wadanda take daukansu a matsayin ‘yan tawaye
Gwamnatin Sudan ta yi watsi da shawarar sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces (RSF) da kasashen kasashe masu shiga Tsakani suka gabatar, tana mai jaddada cewa, tana mutunta duk wani kokari da zai taimaka wajen kawo karshen yakin kasar, matukar dai ya mutunta diyaucin kasar da halaltattun hukumomin kasar.
Sa’o’i kadan bayan kaddamar da shirin na bangarori hudu masu shiga tsakani wanda ya hada da Masar, Amurka, Saudiyya, da Hadaddiyar Daular Larabawa, na kiran zaman lafiya a Sudan da kawo karshen yakin, dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan tashar samar da wutar lantarki da ma’ajiyar man fetur da kuma filin jirgin saman Kenana na jihar White Nile da jiragen sama marasa matuka ciki.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira da a ba da sanarwar yin watsi da shirin, inda ta yi nuni da cewa, yaƙin na da nasaba da al’ummar Sudan, kuma za ta tunkare shi, ta kuma yanke shawara da kansa.
Wani mai sharhi kan al’amuran siyasa Youssef Abdel Manan ya shaidawa tashar talabijin ta Al-Alam cewa: “Kasashen hudu masu siga tsakani ba su da wani hakki, ko na hukuma, ko na dabi’a, ko na siyasa, ko na kasa da kasa, da zai sanya su zama masu kula da al’ummar Sudan.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar September 15, 2025 Hamas ta bukaci kasashen musulmi da na Larabawa su dauki mataki mai tsari kan Isra’ila September 15, 2025 Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa September 15, 2025 Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Dakarun Sojin Yamen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ramon Na Isra’ila. September 14, 2025 Isra’ila Za ta Gamu Da Mummunar Martani Idan Tayi Gigin Afkawa Iran September 14, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Fara Taro A Qatar. September 14, 2025 Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Sabon Sharadi Na Bude Asusun Banki September 14, 2025 An Zabi Issa Tchiroma A Matsayin Dan Takara Daya Tilo A Kamaru September 14, 2025 Kasar Iran Ta Yi Fatali Da Zarge-Zargen Da Kungiyar G7 Da Kawayenta Suka Yi Kanta September 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci