Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Tun Bayan Barkewar Yaki Da Iran Babu Wata Hulda Tsakaninta Da Amurka
Published: 26th, August 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tun bayan barkewar yakin da Iran, babu wata hulda da ta hada ta da Amurka
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya jaddada cewa: “Turawa za su iya taka muhimmiyar rawa a shawarwari,” yana mai bayanin cewa: “Tun bayan barkewar yaki da Iran, kasar Iran ta daina yin mu’amala da Amurkawa, amma tana ci gaba da hulda da Turawa ko da a lokacin da ake tsaka da yakin.
A wata hira da jaridar Süddeutsche Zeitung ta Jamus dangane da shawarar da Turai ta gabatar na tsawaita wa’adin aiki da hanyar da za a bi wajen ganin an dawo da takunkumin majalisar dinkin duniya kan Iran, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i ya bayyana cewa: Iran ta yi imanin cewa, ko wanne lokaci, ko tsawaitawa takunkumi, ko kuma ci gaba da aiki da shi, ba ya dogara ne akan dalilai na shari’a, da ma’ana, ko kuma kyawawan dabi’u ba.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: “Babu wata hujjar cewa shirin makamashin nukiliyar Iran ya ci gaba da kasancewa karkashin kulawar kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, musamman ganin cewa ba a yin shawarwari cikin yanayi na yau da kullum.”
Baqa’i ya yi nuni da cewa: “An kai wa Iran hari ne a tsakiyar tattaunawar, don haka tana da ‘yancin neman sauran bangarorin su tabbatar da amincinsu.” Ya kara da cewa, “Turawa za su iya taka muhimmiyar rawa a cikin wannan tsari, tun bayan barkewar wannan yakin, Iran ta daina hulda da Amurkawa, amma tana hulda da Turawa ko da a lokacin yakin.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Makami Mai Linzamin Sojojin Yemen Ya Zame Mafarki Mai Firgitarwa Ga ‘Yan Sahayoniyya August 26, 2025 Shugaban Kasar Faransa Ya Ce: Kakaba Yunwa Laifi Ne Da Ya Wajaba Dakatar Da Ita Cikin Hanzari August 26, 2025 Iran da Turai za su gudanar da wani zagaye na tattaunawar nukiliya a Geneva August 26, 2025 Gaza: Isra’ila Ta Kashe Fararen Hula 90 Ciki Har Da ‘Yan Jarida 6 August 26, 2025 Sheikh Qassem: Hizbullah ba za taba mika makamanta ba August 26, 2025 Ministocin harkokin Masar da Tunisia sun tattauna batutuwan Gaza, Libya, da Sudan August 26, 2025 Sudan: Mutane sama da rabin miliyan sun koma Khartoum duk da matsalar yaki August 26, 2025 Iran Ta godewa Rasha Dangane Goyon bayanta Kan Hakkinta Na Tace Yuranium August 25, 2025 Iran da saudiya Sun Bukaci Hadin Kan Musumi Don Kawo Karshen Yaki A Gaza August 25, 2025 Iran Ta Yi Kira Ga Kasashen Musulmi Su Yanke Hulda Da HKI A Taron OIC A Jedda August 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Kakakin ma aikatar harkokin wajen
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce: Laifin da Isra’ila ta yi na kashe ‘yan jaridun Yemen babban ta’addanci ne
Kungiyar kare hakkin bil’ adama ta Human Rights Watch ta tabbatar da cewa: Harin da yahudawan sahayoniyya suka kai a ranar 26 ga watan Satumba kan ‘yan jaridun kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan jarida sama da 30, laifi ne da ba za a iya kubutar da girman laifin kan wanda ya aikata ba.
A cikin rahoton baya-bayan nan, kungiyar ta fitar ta bayyana cewa, ta tattara bayanan harin da makiya yahudawan sahayoniyya suka kaddamar a ranar 10 ga watan Satumba kan hedkwatar kafafen yada labarai a kasar Yemen, kuma ta yi la’akari da wannan laifi a matsayin misali na hadarin da ‘yan jarida a Yemen da Palastinu ke fuskanta daga hare-haren wuce gona da iri na ‘yan sahayoniyya.
Kungiyar ta yi nuni da cewa harin da aka kai wa cibiyar ‘yan jaridu a ranar 26 ga watan Satumba a kasar Yemen, ya zo daidai da laifuffukan da yahudawan sahyuniya suka aikata a yankin Al-Jawf, wanda ya yi sanadin jikkatar fararen hula da dama, wadanda akasarinsu ‘yan jarida ne.
Wannan bayani ya karyata ikirarin makiya na cewa sun kai hari ne kawai a ginin ma’aikatar kula da dabi’u, kungiyar kare hakkin bil’adaman tana mai cewa faifan bidiyo da shaidun ganin ido na ‘yan kasar, sun tabbatar da cewa da gangan makiya yahudawan sahayoniyya suka kai hari kan hedkwatar ‘yan jaridun fararen hula.
An lura cewa: ” Unguwar da aka kai harin, wani yanki ne mai yawan jama’a da ke kusa da tsohon birnin Sana’a, wurin tarihi na UNESCO.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida September 16, 2025 Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya September 16, 2025 An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna September 16, 2025 Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza September 16, 2025 Makaman ‘Drons’ Na Yemen Sun Fada Kan Wurare Masu Muhimmanci A HKI September 16, 2025 Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila September 16, 2025 Ministan Tsaron Venezuela Ya Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Juyin Mulki A Kasar September 16, 2025 Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya September 16, 2025 Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai September 15, 2025 Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar September 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci