Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Za SU Iya Komawa Zaman Tattaunawa Da Amurka A Kan Wasu Sharudda
Published: 27th, August 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran ya ce: A shirye Iran take ta gudanar da shawarwari da Amurka, amma kan sharudda
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce; kasarsa a shirye take ta dawo da tattaunawar makamashin nukiliya da Amurka, amma tare da ba da tabbacin babu batun kai hari kan Iran. Ya bayyana cewa ba za a cimma abin da Amurka ke so ba ta hanyar kai harin soji kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, kuma a duk wata tattaunawa dole ne Amurka ta kare sharuddan da Iran ta gindaya mata domin samun ci gaba mai daure wa.
Araqchi wanda ya gana da Asharq Al-Awsat bayan halartar wani zama na musamman na ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi don tattaunawa kan goyon bayan Gaza da Falasdinu, bai nisanta yiwuwar bullar wata sabuwar arangama da haramtacciyar kasar Isra’ila ba, yana mai cewa: “Akwai yiwuwar komai ya faru, kuma Iran a shirye take ta kowane hali.”
Araqchi ya jaddada cewa: Iran a shirye take ta shiga tattaunawa ta gaskiya da adalci dangane da shirinta na makamashin nukiliya, yana mai cewa a halin yanzu ana ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai uku da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa domin tantance sabon tsarin shawarwarin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masu Binciken Hukumar IAEA Ba Za Su Shiga Wajen Da Amurka Ta Kai Hari Ba A Cibiyoyin Nukiliyar Iran August 27, 2025 Kasar Venezuala Ta Jinjinwa Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Kan Kyakkyawar Hadin Kai Da Ke Tsakanisu August 27, 2025 Kasar Rasha Ta Gabatar Da Shawara Ga Kwamitin Sulhun MDD Kan Shirin Makamashin Nukiliyar Iran August 27, 2025 Majalisar Ministocin Sudan Ta Fara Zamanta A Birnin Khartoum Fadar Mulkin Kasar Tun Bayan Barkewar Yaki August 27, 2025 Araqchi: Jakadan Australia a Tehran dan koren Isra’ila ne August 27, 2025 Rasha ta shirya daftarin dakile Shirin turai na mayar da takunkumin MDD kan Iran August 27, 2025 ECOWAS na Shirin hada rundunar dakaru 260,000 domin yaki da ta’addanci August 27, 2025 Trump ya yi barazanar korar Gwamnar Babban Bankin Amurka August 27, 2025 Syria: Adadin mutanen da suka mutu a harin Isra’ila a yankin Damascus ya kai 5 August 27, 2025 An Kammala Taron Iran Da E3 A Geneva August 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya tabbatar da haƙƙin kasashe na haɓakawa da amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Isma’il Baqa’i, ya yi ishara da shawarar da Iran ta gabatar na daftarin kudurin da ya haramta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukiliyar kasashe masu zaman lafiya, yana mai cewa: Dukkanin kasashe na da hakkin yin amfani da makamashin nukiliya don zaman lafiya da kuma hakkin samun ingantacciyar kariya daga duk wani hari ko barazanar kai hari.
A cikin sakon da ya aike ta dandalin X a yau Talata, Ismail Baqa’i ya yi ishara da shirin Iran a babban taron hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) da ake yi yanzu a Vienna, don ba da shawarar daftarin kudurin da ya haramta kai hari kan cibiyoyin makamashin nukiliyar kasashe masu zaman lafiya. Ya ce: “Iran, tare da China, Nicaragua, Rasha, Venezuela, da Belarus, sun gabatar da wani daftarin kuduri ga babban taron hukumar IAEA kan haramta kai hare-hare da kuma barazanar kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukiliya da ke karkashin hukumar sa-idon ta IAEA bisa tsarin kare martabar yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.”
Ya kara da cewa: “Kamar yadda aka bayyana a cikin daftarin kudurin, dukkan kasashe na da ‘yancin yin amfani da makamashin nukiliya domin zaman lafiya da kuma ‘yancin samun ingantacciyar kariya daga duk wani hari ko barazanar kai hari.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan September 16, 2025 Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida September 16, 2025 Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya September 16, 2025 An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna September 16, 2025 Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza September 16, 2025 Makaman ‘Drons’ Na Yemen Sun Fada Kan Wurare Masu Muhimmanci A HKI September 16, 2025 Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila September 16, 2025 Ministan Tsaron Venezuela Ya Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Juyin Mulki A Kasar September 16, 2025 Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya September 16, 2025 Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai September 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci