Kasar Afirka ta Kudu tana ci gaba da shari’ar da ta shigar kan gwamnatin mamayar Isra’ila duk da tsagaita bude wuta da aka yi a Gaza

Ma’aikatar huldar kasa da kasa da hadin gwiwa ta Afirka ta Kudu ta tabbatar da cewa: Tsagaita bude wuta a zirin Gaza ba zai kawar da laifukan da aka aikata kan fararen hula ba, tana mai jaddada cewa: Karar da aka shigar kan haramtacciyar kasar Isra’ila a gaban kotun kasa da kasa na da nufin hana sake aukuwar keta haddi, ba wai don dakatar da su na wani dan lokaci ba.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a ranar Larabar da ta gabata ta ce: “Tsarin shari’ar ya nuna irin sadaukarwar da Afirka ta Kudu ta yi a tarihi wajen yakar wariyar launin fata da kuma kare hakkin al’ummar da ake zalunta,” yayin da ake ci gaba da shari’a kan haramtacciyar kasar Isra’ila kan aikata kisan kare dangi a Gaza.

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta jaddada aniyar ta na ci gaba da gudanar da shari’ar, duk da sanarwar tsagaita bude wuta tsakanin gwamnatin mamayar Isra’ila da bangarorin Falasdinu, la’akari da cewa adalcin kasa da kasa ba shi da alaka da abubuwan da ke faruwa nan take a kasa, sai dai a dora masu alhakin aikata manyan laifuka.

A watan Disambar shekara ta 2023 ne, Afirka ta Kudu ta shigar da kara a gaban kotun kasa da kasa, inda ta zargi gwamnatin mamayar Isra’ila da yi wa fararen hula kisan kiyashi a zirin Gaza.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gwamnatin Kamaru Ta Gargadi Dan Takarar Da Ya Shelanta Kansa A Matsayin Wanda Ya Lashe Zabe October 16, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kungiyar NAM Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Venezuela October 16, 2025 Sojojin Pakistan Sun Tarwatsa Tankokin Yaki 6 Na Afghanistan A Rikicin kan Iyaka October 15, 2025 Tawagar Super Eagles Ta Nijeriya Ta Lallasa Benin Da ci 4-0 A Uyo October 15, 2025 Matakin Kasashen Yamma Na Maidowa Da Iran Takunkumi Ya Sabawa Doka. October 15, 2025 Kasar Indunusiya Ta Sanar Da Goyon Bayanta Ga Alummar Falasdinu October 15, 2025 Isra’ila  Za Ta Sake Kai Hare-hare Idan Ta Karbi Dukkan Mutanenta Da Hamas Ta Kama. October 15, 2025 Trump Ya Fadawa Hamas Su Mika Makamansu Ko Kuma A Kwace Su Da Karfi October 15, 2025 Iran Ta Samarda Sabbin Hanyoyi Na Fuskantar  Barazanar Makiya October 15, 2025 Hamas Ta Ce HKI Tana Cikas Neman Gawawwakin Yahudawa A Gaza October 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Isra’ila ta taƙaita shigar da kayan agaji Gaza

Hukumomi a Isra’ila sun ce gwamnatin ƙasar ta yanke shawarar taƙaita shigar da kayan agaji zuwa zirin Gaza, sannan za ta ɗan dakata ta buɗe bakin iyakar zirin daga Rafas.

Isra’ila ta ce ta ɗauki wannan matakin ne saboda abin da ta kira jan ƙafa da a cewarta Hamas ke yi wajen mayar da sauran gawarwaki da ke hannunsu.

Zuwa yanzu dai gawarwaki huɗu kawai Hamas ta miƙa, sannan akwai rahotannin da ke cewa ƙungiyar za ta miƙa wasu gawarwakin guda huɗu, amma ta ce nemo gawarwakin na da wahalar gaske.

Shi ma Donald Trump ya yi ƙorafi, inda ya buƙaci Hamas ta mayar da gawarwakin “kamar yadda aka yi alƙawari,” in ji shi.

Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce wasu gawarwakin sun ɓace, kuma zai yi wahala a gano su.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Isra’ila ta taƙaita shigar da kayan agaji Gaza
  • Isra’ila  Za Ta Sake Kai Hare-hare Idan Ta Karbi Dukkan Mutanenta Da Hamas Ta Kama.
  • Hamas Ta Ce HKI Tana Jinkirta Neman Gawakin Yahudawa A Gaza
  • Iran Ta Yi Allah Wadai Da Kalaman Kin Jinin Iran Da Trump Ya Yi A Majalisar Dokokin Isra’ila                             
  • Shugaban Kasar Columbia Ya Yi Dirar Mikiya Kan Donald Trump Kan Bai Wa Isra’ila Makamai
  • Trump ya ce zai yi shawara game da batun kafa kasar Falasdinu
  • Ma’aikatar Harkokin wajen Kasar Iran Ta Yi Tir Da Jawabin Trump A Knesset Ta HKI
  •  MDD: Mutane 300,000 Su Ka Gudu Daga Sudan Ta Kudu A 2025
  • Aragchi: HKI Ba Zata Mutunta Tsaida Wuta A Gaza Ba