Manyan malamai, shugabanni na addini, gargajiya da siyasa daga sassan Arewacin Najeriya sun hallara a Kaduna domin Taron Musamman na Malaman Arewa (Special Northern Ulamah Summit), wanda ya mayar da hankali kan nemo mafita ta dindindin ga matsalolin tsaro da ƙalubalen tattalin arziki da ke addabar yankin.

 

Taron ya tattauna kan ƙarfafa haɗin kai tsakanin malamai, amfani da kafafen sada zumunta ta hanyar da ta dace, da kuma ƙarfafa hulɗa tsakanin shugabannin addini, gargajiya da na siyasa domin dawo da zaman lafiya da daidaito a al’umma.

 

Da yake jawabi, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na Uku, wanda Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya wakilta, ya kira malamai da shugabanni su haɗa kai wajen yaki da rashin tsaro, talauci da rarrabuwa. Ya gargaɗi malamai da al’umma da su guji amfani da kafafen sada zumunta wajen yada ƙarya da haifar da fitina.

 

Sarkin Musulmi ya jaddada cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali za su tabbata ne kawai idan aka samu haɗin kai na gaskiya tsakanin sassa daban-daban na al’umma bisa koyarwar addinin Musulunci.

 

A jawabinsu na haɗin gwiwa, Sheikh Abdullahi Bala Lau da Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi sun bayyana cewa son kai, rarrabuwa, da matsin tattalin arziki na daga cikin manyan abubuwan da ke kawo rashin tsaro a Arewa. Sun ce lokaci ya yi da shugabannin addini, gargajiya da siyasa za su buɗe tattaunawa mai fa’ida tare da yin aiki tare domin kawo ƙarshen rikice-rikice da koma bayan tattalin arziki.

 

Haka kuma, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar na Jihar Zamfara, Sanata Shehu Buba na Jihar Bauchi, da Honourable Alhassan Ado Doguwa na Jihar Kano, sun yaba da wannan taro suna mai cewa lokaci yayi da za a ɗauki mataki na haɗin kai domin ceto yankin Arewa daga ƙalubale.

 

Sanata Yari ya ce rashin tsaro na ci gaba da ƙaruwa ne saboda rashin daidaito da ƙarancin damar tattalin arziki, yayin da Sanata Buba ya jaddada muhimmancin ƙarfafa matasa da aiwatar da gyare-gyaren zamantakewa bisa ka’idojin Musulunci.

 

Honourable Doguwa, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Majalisar Wakilai na Arewa (Northern Caucus), ya tabbatar da goyon bayan majalisa ga sakamakon taron, tare da alkawarin haɗa hannu da hukumomi da shugabanni domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a yankin.

 

A ƙarshen taron, mahalarta sun amince da kafa Cibiyar Jagorancin Addinin Musulunci ta Ƙasa (National Islamic Leadership Forum), domin haɗa malamai, shugabanni da masu tsara manufofi a ƙarƙashin dandalin haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba.

 

COV: Shettima Abdullahi

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Arewa Haɗin Kai Rarrabuwa Rashin Tsaro Taron

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Shi

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Cutar kansar mama na ɗaya daga cikin manyan cututtukan da ke addabar mata a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

 

An kiyasta cewa mata sama da dubu ɗari biyu na kamuwa da cutar a kowace shekara a Najeriya, yayin da miliyoyin mata a duniya ke fama da wannan cuta. Abin damuwa shi ne cewa yawancin lokuta ana gano cutar ne a kurarren lokaci, wanda hakan ke sa magani ya yi wahala kuma ya rage yiwuwar ceto rayuwar wanda ya kamu da shi.

NAJERIYA A YAU: Halayen Da Ambasadoji Ya Kamata Su Mallaka Kafin Tura Su Wasu Kasashe DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?

Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Bude Taron Bikin Cika Shakaru 41 Da Kafa Kungiyar Tattalin Arziki Ta ECO A nan Tehran
  • NAJERIYA A YAU: Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Shi
  • ’Yan ta’adda sun kashe ɗan sanda a gidan DPO a Jigawa
  • Baqaei: Amurka Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya
  • Sarkin Musulmi ya buƙaci gwamnonin Arewa suke saurarar ƙorafin jama’a
  • ’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano
  • Likitoci sun gindaya sabon sharaɗi bayan janye yajin aiki
  • Dalilin da na koma jam’iyyar ADC — Atiku
  • Shugaban Najeriya Ya Mika Sunaye Sabbin Jakadun Kasar su 32 Ga Majalisa Domin Tantancewa
  • Yadda aka horar da mata 100 sana’o’in dogaro da kai a Gombe