An fara tantancewar da misalin ƙarfe 12:55 na rana, inda ake sa ran Farfesa Amupitan zai gabatar da tarihinsa da kuma amsa tambayoyin da ‘yan majalisar za su yi masa, kafin yanke shawara kan tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban INEC.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025 Manyan Labarai Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki October 16, 2025 Manyan Labarai An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato October 16, 2025.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali

Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta nemi hukumomin tsaro su gaggauta bincikar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, kan zarginsa da kalaman tayar da hankali.

Wannan na zuwa ne bayan kammala zaman majalisar zartarwa na 34 da aka yi ranar Alhamis a Fadar Gwamnatin Kano.

Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi CAF Tayi Watsi Da Alƙalan Wasan Nijeriya a Kofin Afrika Na 2025

Zaman ya mayar da hankali kan maganganun da Ganduje da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin suka yi, inda suka ce Kano na ƙara fuskantar barazanar hare-haren ’yan bindiga.

Ganduje ya bayyana aniyar ɗaukar mutum 12,000 aiki wanda hukumar Hisbah ta sallama daga aiki, a wata ƙungiya mai alaka da ake kira da “Khairul Nas”.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Juma’a, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce waɗannan maganganu na iya kawo koma baya ga harkar tsaro da ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi.

Majalisar ta kuma nuna damuwarta cewa ƙasa da awanni 48 bayan yin waɗannan maganganu, aka sake kai hari wasu yankuna na jihar.

Gwamnatin jihar ta sake godewa Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro kan goyon bayan da suke bayarwa wajen yaƙi da matsalolin tsaro.

Haka kuma ta yi gargaɗin cewa ba za ta bari wani ko wata ƙungiya ta kafa haramtacciyar rundunar tsaro ba a Jihar Kano.

A ƙarshe, gwamnatin ta roƙi jami’an gwamnati da’yan siyasa su guji yin maganganun da ka iya tayar da hankali.

Ta kuma tabbatar wa mazauna jihar cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da doka a faɗin Kano.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Lebanon: Wasikar Kungiyar Hizbullah Ga Paparoma
  • An sake zabar Eto’o a matsayin Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Kamaru  
  • Likitoci sun gindaya sabon sharaɗi bayan janye yajin aiki
  • Shugaban Najeriya Ya Mika Sunaye Sabbin Jakadun Kasar su 32 Ga Majalisa Domin Tantancewa
  • Hizbullah Ta Bukaci Shugaban Cocin Katolika Na Duniya Yayi Tir Da Hare-haren Isra’ila
  • Tinubu ya sake aike wa majalisa ƙarin sunayen jakadu 32
  • Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali
  • An Rantsar Da Sabon Shugaban Mulkin Soja Na kasar Guinea-Bissau
  • Ya kamata ’yan majalisar Najeriya su koma zaman wucin gadi – Ndume
  • An janye ’yan sanda 11,566 daga yi wa manyan mutane rakiya – Egbetokun