Ba mu ji dadin yi wa mahaifinmu afuwa tare da riƙaƙƙun masu laifi ba – Iyalan Herbert Macaulay
Published: 17th, October 2025 GMT
Iyalan marigayi Herbert Macaulay sun soki matakin gwamnatin tarayya na haɗa sunan fitaccen ɗan gwagwarmayar cikin riƙaƙƙun masu laifi a jerin waɗanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa afuwa bayan ransu.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a Legas ranar Alhamis, iyalan tare da goyon bayan dattijo kuma Atona Oodua na Yarabawa, Chief Olabode George, sun bayyana cewa kodayake sun yaba da yadda shugaban ƙasa ya girmama rawar da Macaulay ya taka a tarihin Najeriya, ba daidai ba ne kuma abin ƙasƙanci ne a haɗa shi da wasu da ake tuhuma da manyan laifuka.
“Idan za a girmama Baba, to a girmama shi ne shi kaɗai,” in ji George a madadin iyalan Macaulay.
Ya ƙara da cewa, “Herbert Macaulay ba barawo ba ne; ya kasance ɗan ƙasa na gari, mai hangen nesa, kuma jikan Bishop Anglican na farko a Afirka. Ya cancanci a ware shi don girmamawa ta ƙasa, ba a haɗa shi da masu laifi ba.”
Daga cikin iyalan da suka halarci taron akwai Erelu Adeola Macaulay, Mr. Lanre Oshodi, Ms. Mayokun Thomas, Miss Kofoworola Macaulay, Miss Adeyinka Macaulay, Mr. Ayo Ogunlana, da Miss Turi Akerele, da sauransu.
A cikin jawabin sa mai taken “Herbert Macaulay: Uban Gwagwarmayar Siyasar Najeriya”, George ya ce gudummawar da Macaulay ya bayar a matsayin ɗan gwagwarmaya, injiniya, da jagoran siyasa har yanzu tana da tasiri.
Ya ce Macaulay ne ya kafa tubalin wayewar siyasar zamani a Najeriya.
“An haifi Herbert Macaulay a shekarar 1864 cikin zuri’ar ilimi, addini da hidima. Da ya so, zai iya yin shiru a tsarin mulkin mallaka, amma sai ya zaɓi ya tsaya tsayin daka wajen adawa da zalunci da faɗa da ƙarya,” in ji George.
Ya bayyana yadda Macaulay ya yi amfani da jaridar Lagos Daily News wajen yaɗa manufofinsa, yadda ya kare Oba Eshugbayi Eleko daga mulkin mallaka, da kuma yadda ya kafa jam’iyyar NNDP a shekarar 1923, jam’iyyar siyasa ta farko a Najeriya.
“Siyasar Macaulay ba ta dogara da gata ba, sai dai manufa. Ya fitar da siyasa daga ɗakunan taron turawa zuwa tituna da kasuwannin tsibirin Legas,” in ji George.
Iyalan da magoya bayansu sun bukaci gwamnati da ta girmama Macaulay ta hanyoyi na musamman, kamar kafa wuraren tunawa da shi, bayar da guraben karatu, da shirye-shiryen horar da matasa bisa ƙa’idodin da ya tsaya kai da fata a kansu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Herbert Macaulay Herbert Macaulay
এছাড়াও পড়ুন:
Akwai yiwuwar matsin lamba ya sa Tinubu cire sunayen wasu da ya yi wa afuwa saboda cece-kuce
Rahotanni na nuna cewa akwai yiwuwar Shugaban Kasa Bola Tinubu ya cire wasu sunaye daga jerin wadanda ya yi wa afuwa bayan cece-kucen da hakan ya jawo.
Hakan dai ya biyo bayan ci gaba sukar lamirin hakan da jama’a ke yi, musammam kan saka wasu rikakkun masu laifi da kotu ta yanke wa hukunci daban-daban.
Saudiyya ta zaftare wa Najeriya guraban Aikin Hajji da sama da kujeru 28,000 ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 8 a harin kwanton ɓauna a ZamfaraAfuwar shugaban kasa da ake bayarwa a lokutan bukukuwan ƙasa, ana yin ta ne don rage cunkoso a gidajen yari da kuma ƙarfafa sulhu da haɗin kai.
Sanarwar fadar shugaban kasa ta ce an yanke shawarar ne bisa shawarwarin Kwamitin Shawara na Shugaban Ƙasa kan Afuwa, wanda Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ke jagoranta.
Sai dai wannan lamari ya sake tayar da cece-kuce kan gaskiya da sahihancin tsarin afuwar Najeriya.
Amma a ranar Alhamis, Ministan na shari’a ya ce afuwar da shugaban kasa ya sanar ba a kammala tantance ta ba, kuma har yanzu akwai sauran matakan da ba a kammala cikawa ba.
Cece-kuce na ci gaba da tasowa kan wasu sunaye da aka haɗa a ciki, inda hukumar EFCC, ICPC da NDLEA da sauran hukumomin tsaro suka fara kokarin dakatar da sakin wasu daga cikin waɗanda ke cikin sunayen.
A taron Majalisar Koli da aka gudanar a ranar 9 ga Oktoba, 2025, fadar shugaban kasa ta shelanta sunayen mutum 175 da aka yi wa afuwar, ciki har da masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, masu laifukan ofis, masu laifukan miyagun ƙwayoyi, Manjo-Janar Mamman Vatsa, Farfesa Magaji Garba, Ken Saro-Wiwa, mutanen Ogoni, Maryam Sanda da ma wasu da dama.
Yayin da sunayen wasu ’yan siyasa kamar Herbert Macaulay da Farouk Lawan ba su haifar da cece-kuce ba, haɗa sunayen masu laifukan tashin hankali da karya doka ya jawo fushi daga jama’a.
Daya daga cikin sunayen da suka jawo cece-kuce shi ne Maryam Sanda, wacce aka yanke wa hukuncin kisa a 2017 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello.
Yayin da wasu daga cikin iyalan marigayin suka ƙi amincewa da afuwar, Alhaji Bello Isa (mahaifin mamacin) da Alhaji Garba Sanda (mahaifin Maryam) sun gudanar da taron manema labarai don karɓar afuwar ta shugaban kasa.
Shugaban kasa ya kuma yi wa Major S. Alabi Akubo afuwa, wanda aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai kan mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, da kuma Kelvin Prosper Oniarah, wanda aka danganta da hare-haren garkuwa da mutane a jihohin Delta, Edo, Ribas, Abia, Binuwai da Oyo, inda aka gano sansanoninsa na tsare mutane a Warri, Kokori, Ugbokolo, Benin City da Aba.
Kazalika, sunayen waɗanda aka yanke wa hukunci kan kashe jami’an tsaro, safarar miyagun ƙwayoyi, da satar kuɗi, da sauransu, sun jawo tambaya daga jama’a.
Rahotanni sun nuna cewa wannan cece-kuce ya sa fadar shugaban kasa ta fara nazarin sake duba tsarin afuwa, tare da yiwuwar cire sunayen da suka jawo suka daga jama’a.