’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 8 a harin kwanton ɓauna a Zamfara
Published: 17th, October 2025 GMT
Aƙalla jami’an tsaro takwas, ciki har da ɗan sanda guda ɗaya da masu tsaron al’umma bakwai, sun rasa rayukansu a wani harin kwanton bauna da aka kai musu a hanyar Gusau–Funtua da ke Jihar Zamfara a ranar Alhamis.
Lamarin ya faru ne a lokacin da gamayyar jami’an tsaro, waɗanda suka haɗa da ’yan sanda da mambobin rundunar tsaro ta jihar Zamfara ke amsa kiran gaggawa daga kauyen Tungawa da ke ƙaramar hukumar Tsafe.
“Maganar da nake yanzu haka, an kwashe gawarwakin jami’an da suka mutu zuwa Gusau domin jana’iza,” in ji wani shaida da aka bayyana sunansa da Tsafe.
Shugaban ƙaramar hukumar Tsafe, Hon. Garba Fanchan, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
Ya bayyana harin a matsayin “mugunta da rashin imani,” yana mai tabbatar wa jama’a cewa gwamnati na ɗaukar matakan gaggawa don dakile matsalar tsaro da ke ƙaruwa a yankin.
Gwamnan jihar, Dauda Lawal, shi ma ya aike da saƙon ta’aziyya ga iyalan mamatan.
A cikin wata sanarwa ranar Alhamis, gwamnan ya jajanta wa hukumomin tsaro tare da addu’ar Allah ya gafarta wa jami’an da suka rasa rayukansu.
“Waɗannan jaruman sun mutu ne a yayin da suke bakin aiki don kare al’ummarmu. Allah ya gafarta musu, ya sa sun huta,” in ji Gwamna Lawal.
Hanyar Gusau–Funtua na ƙara zama wurin da ake yawan kai hare-hare, inda rahotanni ke nuna cewa kusan kowace rana ’yan bindiga na kai farmaki ga matafiya a hanyar.
Hukumomi sun sha alwashin ƙara daukar matakai domin dawo da zaman lafiya a hanyar da kuma tabbatar da lafiyar matafiya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an FRSC Sun Mayar Da N6.2m Da Suka Tsinta Bayan Aukuwar Hatsarin Mota A Katsina
Wani daga cikin waɗanda suka ji rauni, wanda shi ne mai kuɗin, ya gode wa jami’an FRSC bisa gaskiya da amana da suka nuna, yana mai cewa abin koyi ne ga kowa.
FRSC ta gargaɗi direbobi da su riƙa kula da motoccinsu akai-akai tare da bin ƙa’idojin hanya domin guje wa aukuwar haɗura.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA