Aminiya:
2025-10-15@22:51:42 GMT

Gwamna Inuwa ya naɗa sabbin shugabanni a ma’aikatar lafiya ta Gombe

Published: 15th, October 2025 GMT

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da naɗa sabbin shugabanni biyu a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar.

An naɗa Dokta Lawan Bala a matsayin Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya, sannan Dokta Mohammed Bello Abdulkadir a matsayin Babban Sakataren Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Gombe.

Majalisar Dattawa za ta tantance Amupitan a ranar Alhamis Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba sai sun yi tuba na gaskiya — Radda

Kafin wannan lokaci, Dokta Lawan Bala shi ne Babban Sakataren Hukumar Kula da Asibitoci, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar.

Shugaban Ma’aikata na Jihar Gombe, Alhaji Ahmed Kasimu Abdullahi ne, ya bayyana amincewar gwamnan.

Ya ce wannan mataki yana cikin shirin gwamnati na ƙara inganta harkokin lafiya bayan nasarar taron ƙoli kan lafiya na farko da aka gudanar a jihar.

A wata sanarwa da Kakakin Gwamna, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar, ya ce Gwamnan ya amince da aiwatar da tsarin albashi na CONMESS da CONHESS ga ma’aikatan lafiya, tare da yin wasu gyare-gyare domin inganta shugabanci a wannan ɓangare.

Dokta Mohammed Bello Abdulkadir, wanda kafin yanzu shi ne Daraktan Harkokin Lafiya a Ma’aikatar Lafiya, ya kasance ƙwararre a aikin likitanci da gudanar da manufofin kiwon lafiya.

Ana sa ran sabbin shugabannin za su ci gaba a harkokin lafiya a jihar.

Gwamna Inuwa, ya bayyana cewa yana da cikakken tabbaci cewa za su yi amfani da ƙwarewarsu wajen inganta kiwon lafiya a Jihar Gombe.

Naɗin nasu ya fara aiki nan take.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwamna Inuwa Kiwon Lafiya Naɗi Ma aikatar Lafiya aikatar lafiya Jihar Gombe

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Buni ya ware N5.8bn don biyan haƙƙin tsoffin ma’aikata a Yobe

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da fitar da Naira biliyan 5.8 domin biyan haƙƙin tsoffin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya a jihar.

Kwamishinan kuɗi na jihar, Mohammed Abatcha Geidam, ya ce wannan mataki na nuna yadda gwamnatin ke ƙoƙarin inganta rayuwar ma’aikatanta, musamman waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.

Farashin kayayyaki ya sauka zuwa kashi 18.02 a watan Satumba — NBS Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Ya ce gwamnan ya bayar da umarni cewa daga yanzu, biyan haƙƙin tsoffin ma’aikata zai zama cikin jadawalin kuɗin wata-wata kamar yadda ake biyan fansho.

“Ina nufin daga yanzu za a riƙa biyan kudin a kowane wata tare da fansho, domin kauce wa taruwar bashi kamar yadda ya taɓa faruwa a baya,” in ji Kwamishinan.

Geidam, ya ƙara da cewa amincewar gwamnan babban mataki ne na tabbatar da cewa duk wani ma’aikaci da ya yi ritaya zai samu haƙƙinsa yadda ya dace.

“Hakan zai dawo da mutuncin tsoffin ma’aikata kuma ya tabbatar da cewa gwamnati tana nuna kulawa ga waɗanda suka yi mata hidima da gaskiya,” in ji shi.

Kwamishinan, ya bayyana cewa ma’aikatar kuɗi da ofishin shugaban ma’aikata suna aiki tare domin tabbatar da cewa an biya waɗanda abin ya shafa cikin lokaci ba tare da wata matsala ba.

Ya ƙara da cewa wannan mataki wani ɓangare ne na tsarin tattalin arziki da zamantakewa na Gwamna Buni domin tabbatar da jin daɗin al’ummar Jihar Yobe, musamman tsoffin ma’aikata da suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Indunusiya Ta Sanar Da Goyon Bayanta Ga Alummar Falasdinu
  • Gwamna Buni ya ware N5.8bn don biyan haƙƙin tsoffin ma’aikata a Yobe
  • Gwamnan Bayelsa ya fice daga jam’iyyar PDP
  • Jihar Kano Na Aikin Gyaran Cibiyoyin Lafiya Da Za Su Yi Gogayya Da Na Ƙasashen Duniya
  • Kudurorin Kafa Hukumomi 3 Sun Tsallake Karatu Na 2 A Majalisar Dokokin Jihar Jigawa
  • Araghchi : Trump bai cancanci mai samar da zaman lafiya ba yayin da yake haifar da yake-yake
  • Gwamnan Enugu Peter Mbah da kwamishinoninsa sun koma APC
  • Mahalarta Taron ‘Sherm-Sheikh” Sun Rattaba Hannu Akan Yarjejeniyar Zaman Lafiya
  • Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje