Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya barazana ce ga wanzuwar tsaron yankin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya suna wakiltar wata barazana ga wanzuwa tsaro da zaman lafiyar yankin da kuma kasashensu. Idan ba a dakile wannan barazanar ba, to babu shakka yankin zai fuskanci yake-yake marasa iyaka.

A yayin taron manema labarai na mako-mako a ranar Litinin, Baqa’i ya yi ishara da zagayowar ranar 28 ga watan Mordad (19 ga Agusta, shekara ta 1953, yana mai cewa: Ba za a iya mantawa da wannan lamari mai zafi ba, juyin mulkin da ya hambarar da zababbiyar gwamnatin al’ummar Iran tare da hadin gwiwar Amurka da Birtaniya.

Dangane da ci gaban yankin kuwa, Baqa’i ya bayyana cewa: Babban abin da ya fi daukar hankali a halin yanzu shi ne laifukan kisan kiyashi da ake ci gaba da wanzuwa a Falasdinu. A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, an shaida matakin da yahudawan sahayoniyya suka dauka na kakaba wa Gaza cikakken shingen da fice, inda a kullum ake kashe akalla mutane 80 da ba su ji ba ba su gani ba.

Ya kara da cewa, “kasashen duniya sun bayyana kin amincewarsu da manufar tilastawa Falasdinawa gudun hijira, amma duk da goyon bayan Amurka da kuma ci gaba da aiwatar da munanan manufofin Isra’ila na rashin hukunta ta, hukumar Isra’ila ta dage kan ci gaba da aikata laifukan da take aikatawa, wanda ya zama ci gaba da manufofin kisan kiyashi. A ranar Asabar din da ta gabata, yahudawan sahayoniyya sun kai hari kan yankunan kasar Yemen, kuma Iran ta jaddada yin Allah wadai da kakkausar murya, kuma harin kan ababen more rayuwa laifi ne na yaki.”

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Da Armenia sun kudiri aniyar kara bunkasa alakokinsu a dukkanin fagage August 19, 2025 Hamas da sauran bangarorin Falastinawa sun amince da shawarar tsagaita wuta August 19, 2025 DR Congo da mayakan M23 sun kasa cimma matsaya a  yarjejeniyar Doha August 19, 2025 Burkina Faso: Ba mu da bukatar Kodineta ta  MDD a kasarmu August 19, 2025 Araqchi: Iran Ba Za Ta Amince Da Sauyi A Kan Iyakokin Yankin Siyasa Ba August 18, 2025 Mataimakin Kwamandan Dakarun IRGC Ya Jadadda Cewa; Suna Sanya Ido Kan ‘Yan Sahayoniyya Da Magoya Bayansu August 18, 2025 Mai Ba Da Shawara Ga Kwamandan Sojojin Iran Ya Ce; Akwai Yiwuwar Sake Yaki, Don Haka Suna Cikin Shiri August 18, 2025 Shugaban Amurka Ya Ce: Yaki Tsakanin Iran Da Isra’ila Bai Kare Ba August 18, 2025 Trump Yace Zelensky Zai Kawo Karshen Yaki Da Rasha Tare Da Barin Batun NATO Da Crimea August 18, 2025 MSF Ta Ce Yawan Mutanen Da Suke Mutuwa A Gaza Sun Ninka Har Sau Uku Bayan Fara Aikin GHF August 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Pezeshkian: Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Kasar Qatar Zalunci Ne Ga Diflomasiyya

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan Qatar zalunci ne ga diflomasiyya

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Harin wuce gona da iri kan kasar Qatar, wani hari ne da kungiyar yahudawan sahayoniyya ta shirya kai wa, da nufin dakile yunkurin diflomasiyya na kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza.

Shugaba Pezeshkian ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a yayin taron gaggawa na shugabannin kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa dangane da harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan Qatar.

Shugaban ya kara da cewa, wannan cin zarafi na diflomasiyya ya wuce matsayin laifi kawai; ya zama sanarwar aikin rashin kunya da ya zama a yanzu rundunar soji ita ce mai yanke hukunci, ba doka ba.”

Ya ci gaba da cewa, “Abin takaici, ‘yan ta’adda a Tel Aviv sun kara jajircewa da dogewa, inda suka samu kariya daga irin wannan cin amanar diflomasiyya ta hanyar kai wani kazamin yaki kan al’ummar kasar Iran.”

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya September 16, 2025 Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan   September 16, 2025 Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida September 16, 2025 Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya September 16, 2025 An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna September 16, 2025 Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza September 16, 2025 Makaman ‘Drons’ Na Yemen Sun Fada Kan Wurare Masu Muhimmanci A  HKI September 16, 2025 Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila September 16, 2025 Ministan Tsaron Venezuela Ya Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Juyin Mulki A Kasar September 16, 2025 Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila
  • Hamas Ta Karyata Gwamnatin Mamayar Isra’ila Kan Shirga Karya Don Kare Muggan Manufofinta
  • Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila
  • Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki Guda 5 A Wajen Taron Kolin kere-kere .
  • Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta.
  • Pezeshkian: Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Kasar Qatar Zalunci Ne Ga Diflomasiyya
  • Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar
  •  Dan Kasar Iran Mai Kirkira Ya Sami Kyautar Yabo A Kasar China
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha
  • Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces