Farashin kayayyaki ya sauka zuwa kashi 18.02 a watan Satumba — NBS
Published: 15th, October 2025 GMT
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, ta sauka zuwa kashi 18.02 a watan Satumba, 2025, idan aka kwatanta da kashi 20.12 da aka samu a watan Agusta.
A cewar rahoton hukumar, hauhawar farashin kayayyaki gaba ɗaya a watan Satumba ta kasance kashi 0.72, yayin da farashin kayan abinci ya ragu da kashi 1.
Cikakken bayani na tafe…
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Yada Labarai Ya Bayyana Jihar Borno A Matsayin Mafi Juriya A Najeriya
Ministan Yada Labarai Mohammed Idris, ya bayyana Jihar Borno a matsayin jiha mafi juriya a Najeriya, yana jaddada gagarumar nasararta wajen shawo kan ƙalubale da dama tsawon shekaru.
Yayin wata ziyarar ban-girma da ya kai wa Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Umar Isa Kadafur, a Maiduguri, Ministan ya yaba wa mutanen jihar bisa jajircewarsu da himmarsu wajen fuskantar matsaloli.
Wannan ziyara na daga cikin shirye-shiryen taron Kwamitin Kwamishinonin Yada Labarai na jam’iyyar APC.
Ya bayyana cewa abubuwan da suka faru a Borno cikin shekaru goma da suka wuce sun nuna jarumtaka da haƙurin mutanen jihar, waɗanda ke ci gaba da ginawa da tafiya gaba duk da matsalolin da suka fuskanta.
Ministan ya jaddada cewa ƙarfin gwiwar mutanen Borno abin alfahari ne kuma abin koyi ga ƙasa baki daya.
Daga Bello Wakili