Makaman Rasha Masu Gudun Walkiya Da Ke Yi Wa Ƙasashen Turai Barazana
Published: 8th, September 2025 GMT
Saboda tsabar gudunsu da kuma zilliya inda suke da sauri ninki biyar na gudun sauti makamai ne da ka iya sauya yadda ake fafata yaki a yanzu.
Hakan ta sa yanzu kasashe ke rige-rigen samar da su.
Rasha, China, Amurka: rigegeniyar nuna iko Bikin faretin na Beijing ya jawo rade-radi game da barazanar da China ke yi wa kasashen Yamma da makamanta masu linzami.
Amurka kuma, na kokarin kamo su ne, yayin da Birtaniya kuma ba ta da su.
William Freer, wani mai nazarin harkokin tsaro a cibiyar Council on Geostrategy, na ganin dalilin da ya sa Rasha da China suka zarce saura abu ne mai sauki.
“Sun yanke shawarar zuba kudade masu yawa a wadannan fannonin tun shekaru baya.”
A gefe guda kuma, kasashen Yamma sun fi mayar da hankali tun daga shekara 20 da suka wuce wajen yaki da masu ikirarin jihadi a gida da kuma kasashen waje.
A lokacin, yiwuwar gwabza yaki tsakanin manyan kasashe masu karfin soji iri daya ba ta da yawa.
Aikin gwajin wani makami mai linzami mai matsakaicin nisa a Koriya ta Arewa
“Abin da ya faru shi ne, mun gaza wajen lura da barazanar China wajen inganta rundunar sojinta,” kamar yadda Sir Aled Younger, wanda ya bar mukamin shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta Birtaniya a 2020, ya bayyana.
Sauran kasashe na ta kokari su ma: Isra’ila na da makamin hypersonic mai suna Arrow 3 wanda aka kirkira domin kakkabo makamai.
Iran ta yi ikirarin cewa tana da shi, wanda ta ce ta harba wa Isra’ila lokacin yakin kwana 12 da suka gwabza a watan Yuni.
(Tabbas makamin ya yi gudun walkiya amma ba a tunanin yana da ikon zilliya mai yawa da za a kira shi cikakken hypersonic).
Koriya ta Arewa ma na ta yin aiki kan nata tun 2021, har ma ta yi ikirarin cewa tana da makamin.
Yanzu Amurka da Birtaniya na zuba kudade a fannin makaman hypersonic, kamar yadda saura kamar Japan da Faransa ke yi.
Amurka ta kaddamar da nata makamin mai gudun hypersonic mai suna “Dark Eagle”.
Amma dai a yanzu China da Rasha ne kan gaba sosai, inda wasu masana a kasashen Yamma ke cewa abin damuwa ne.
Dankaren gudu da mummunar barna
Kalmar hypersonic na nufin wani abu mai gudun tsiya kan ma’aunin March 5 ko sama da haka. Ma’ana mai gudu ninki biyar na sauti ko kuma gudun mil 3,858 cikin awa daya.
Wannan gudun nasu shi ne abin da ya sa ake fargaba game da su.
Makamin da aka sani mafi gudu zuwa yanzu shi ne na Rasha mai suna Abangard – wanda aka ce ya kan yi gudun Mach 27 (kusan mil 20,700 cikin awa daya), kodayake an fi ambato gudun Mach 12.
Game da barnar da suke haifarwa, irin wadannan makaman ba su fi sauran makamai masu linzami hadari mai yawa ba, a cewar Mista Freer.
“Wahalar ganowa da kuma kakkabo su ce ke sakawa ana tsoronsu sosai.”
Akan harba su ne da taimakon wata roka, idan suka kai kololuwar tashi sai kuma su shiga wani yanayi da ake kira “scramjet engine” wanda shi kuma zai yi musu jagora domin dira inda aka aika su.
Akan yi amfani da su ta hanya biyu, ma’ana bam din suke dauke da shi zai iya zama na nukiliya ko kuma gama-garin bam.
Kafin a ayyana makami a matsayin mai gudun walkiya na hypersonic, dole ne sai ya mallaki ikon zillewa makaman kariya. Wanda ya harba shi zai dinga sassauya masa hanyar tafiya ta yadda abokin gabarsa ba zai iya gane shi ba har sai ya dira kan wurin da ya nufa.
“Ta hanyar kauce wa nau’rorin leken samaniya, sukan kauce wa abokan gaba har sai lokacin da suke dab da isa wanda hakan zai sa babu damar da za a iya tare su,” Patrycja Bazylczyk, mai bincike a sashen Missile Defence Project na cibiyar Centre for Strategic and International Studies da ke Amurka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Rasha
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Tarayyar Turai Ta Gabatar Da Shawarar Jingine Aiki Da Yarjejeniyar KAsuwanci Da HKI
Hukumar tarayyar turai ta gabatar da shawara ga kasashe mambobi da su jingine aiki da yarjejeniyar da aka kulla ta kasuwanci da HKI saboda yakin Gaza.
A yau Laraba ne dai hukumar tarayyar turai din ta bijiro da wannan shawarar ga kasashen mambobi,sai dai kuma babu cikakken goyon baya daga mafi yawancin kasashen kungiyar da zai sa a yi aiki da shi.
Ita kuwa jami’ar harkokin wajen ta tarayyar turai din Kaya Kalas ta gabatar da shawarar a kakaba takunkumi akan wasu ministoci biyu na HKI da kuma ‘yan share wuri zauna da suke amfani da akrfi akan Falasdinawa.
Da akwai kungiyoyin kare hakkin bil’adama guda 84 da suke yin kira a yanke duk wata alaka ta kasuwanci da zuba hannun jari da HKI,daga cikinsu har da “Amnesty International”.
Kungiyoyin dai suna son ganin kasashen na turai da su ka hada tarayyar turai, kasar Birtaniya sun dauki matakai masu kwari na yanke alakar tattalin arziki da HKI.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa Kisan Kiyashi A Gaza September 17, 2025 Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila September 17, 2025 Hamas Ta Karyata Gwamnatin Mamayar Isra’ila Kan Shirga Karya Don Kare Muggan Manufofinta September 17, 2025 Iran Ta Bayyana Abubuwan Da Bata Amince Da Su Ba A Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar OIC A Birnin Doha September 17, 2025 Chadi: Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa September 17, 2025 Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila September 17, 2025 Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza September 17, 2025 Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan Musulmi game da halin da ake a yankin September 17, 2025 Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza September 17, 2025 Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza September 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci