2025-06-16@11:21:46 GMT
إجمالي نتائج البحث: 405
«Watsi Da Korafi»:

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Tattauna Darakta-Janar Na Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta Duniya
Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna da Grossi kan sabbin abubuwan da suka shafi tattaunawar nukiliyar Iran Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi da Darakta Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya Rafael Grossi sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da suka shafi tattaunawar nukiliya da kuma dage takunkumin da aka kakabawa Iran a...

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Gargadi Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta Duniya Da Wasu Kasashe
Iran ta gargadi hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya da wasu kasashe Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’ar kasa da kasa Kazem Gharibabadi, ya gargadi hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA da wasu kasashen duniya kan ci gaba da bin tafarki maras kyau da suka...
Gwamna Yusuf wanda a halin yanzu yake kasar Saudiyya don gudanar da aikin hajjin 2025, ya bayar da umarnin ware ranar Litinin 2 ga watan Yunin 2025 a matsayin ranar hutu domin bai wa al’ummar damar yin jimami tare da yi wa wadanda suka rasu addu’a. Ya kuma yi kira ga limamai da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Limamin Sallar Juma’ar Tehran Ya Jaddada Cewa: Babu Wanda Zai Dakatar Da Iran Tace Sinadarin Uranium
Limamin da ya jagoranci sallar Jumu’a a birnin Tehran ya jaddada cewa: Ba za su taba yin watsi da ‘yancin su na mallakar makamashin nukiliya na zaman lafiya ba Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya jaddada cewa: Iran ba ta neman...
Likitocin Iran sun yi bikin murnar nasarar da ta samu na dasa na’urar dawo da ji da inganta shi ga masu matsalar kurmantaka da raunin ji a lardin Khuzestan na kasar Ƙaunar sana’a, dagewa, da sadaukarwa sune sirrin nasarar kowane aiki da hidimar jin kai. Waɗannan kalaman ne Farfesa Nadir Al-Saki ya fara bude jawabinsa...
Bangarorin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa sun kai hari kan sojojin mamaya a wani farmakin hadin gwiwa da suka kai a Khan Yunus Dakarun Sarayal-Quds bangaren sojin kungiyar Jihadul-Islami da kuma dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwagrmayar Musulunci ta Hamas sun tabbatar da cewa: Sun yi nasarar kashe sojojin mamayar Isra’ila tare da raunata wasu a...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Tsokaci Kan Hanyar Warware Takaddamar Shirin Makamashin Nukiliyar Iran
Ministan harkokin wajen kasar Iran yayi tsokaci kan hasashe game da kusancin cimma yarjejeniyar nukiliyar da ke gudanarwa tsakanin Amurka da Iran Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Hanyar diflomasiyya tana bukatar a dage dukkan takunkumai da aka kakabawa Iran da kuma mutunta hakkin mallakar makamashin nukiliyar Iran, yana mai cewa:...
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Harin da “Isra’ila” ta kai wa filin saukar jiragen saman Sanaa, manufarsa ita ce yin matsin lamba akan matsayarmu ta taimakawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta.” Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kara da cewa; Komai girman hare-haren da Isra’ilan za ta kai ba zai...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i, ya sanar a marecen jiya Laraba cewa, Iran za ta iya dakatar da tace sanadarin Uranium a karkashin yarjejniyar da za a iya kullawa da Amurka. Kakakin ma’ikatar harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Dr. Baka’i ya yi watsi da labarin da kamfanin dillancin labarun “Reuters”...
Air Marshal Abubakar ya ba da misalin harin da sojin saman suka kai, inda suka dakile harin ‘yan ta’adda a sansanin soji na ‘New Marte’ da sanyin safiyar ranar 24 ga Mayu, 2025, a jihar Borno A wannan rana, gungun mayakan ISWAP sun yi yunkurin kutsawa sansanin soji ta hanyar amfani da babura da...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arachi ya tir da kalaman jakadan Burtaniya a Washington, Peter Mandelson, wanda yayi kira ga Amurka kada ta taba barin Iran ta tashe makamashin Uranium a cikin kasar. Ministan ya kara da cewa Mandelson yana son ya karkatar da tattaunawan da Iran take da Amurka. Ya kuma kara da ...
Ya ce, mahajjaciyar ta kamu da rashin lafiya ne jim kadan bayan kammala Tawafi – zagaye dakin Ka’aba, inda daga nan aka kai ta asibiti a ranar Lahadi, a ranar Litinin kuma Allah ya yi mata cikawa. “Kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, an yi jana’izar ta a Makkah a wannan rana, kuma an...
Shugaban kasar Iran wanda ya karbi bakuncin Fira ministan Pakistan da marecen jiya Litinin, ya bayyana cewa; Kasar Pakistan, makwabciyar jamhuriyar musulunci da muhimmanci, ta dubban shekaru. Shugaban kasar ta Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda yake Magana a lokacin taron manena labaru na hadin gwiwa da Fira ministan na Pakistan, ya kuma ce; Da akwai haduwar...
Bayanai daga Falasdinu na cewa wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai cikin dare a wata makarantar Gaza dake zaman matsugunni ga masu neman mafaka ya yi sanadin shahadar Falasdinawa 30, ciki har da yara da dama, a cewar jami’an kiwon lafiya da na fararen hula. Da sanyin safiyar yau litinin ne sojojin gwamnatin...

Ministan Harkokin Wajen Iran Yace Faransa Bata Da Yencin ZarginWata Kasa Dange Da Kare Hakkin Bil’adama
Mainistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Faransa bata da hakkin sukar wata kasa a duniya dangane da abinda ya shafi kare hakkin bil’adama. Bayan matsayinta a kissan kiyashin da HKI take aikatawa a gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa ministan yana maida martani ne...
05-Majiyar Sojojin kasar Yemen ta bayyana cewa sojojin kasar a safiyar yau ma sun cilla makamai masu linzami a kan tashar jiragen sama na Bengerion a birnin Yafa (telaviv) na HKI. Inda faduwar makaman ya dakatar da sauka da tashin jiragen sama a tashar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Janar Yahyah...
Ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ta gayyaci jakadan kasar Faransa dake nan Iran domin nuna masa kin amincewa da furucin ministan harkokin wajen kasarsa da ya shafi batunci ga Iran. Muhammad Tanhaye wanda shi ne mai kula da bangaren kasashen turai a ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran, ya bukaci Karin bayani...
Gwamnatin Sudan ta bayyana cewa: Sabbin takunkuman da Amurka ta kakaba mata, bakar siyasa ce ta nemen bata mata suna A cikin wata sanarwa da gwamnatin Sudan ta fitar, ta yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na kakaba mata sabbin takunkumai, tana mai bayyana hakan a matsayin maimaita kura-kurai irin na baya...

Kafafen Watsa Labarun Isra’ila: Kungiyoyin Kasa Da Kasu Sun Ki Shiga Cikin Shirin Isra’ila Da Amurka Na Raba Kayan Agaji
Kafafen watsa labarun HKI sun ce, Amurka ta bayyana cewa, MDD ta ki aiki tare da kamfanonin Amurka da na Isra’ila domin raba kayan agaji a Gaza. Majiyar ta HKI ta kuma kara da cewa; An jinkirta aiwatar da Shirin na raba kayan agajin saboda wasu dalilai na kayan aiki. Wuraren hudu ne dai aka...
“Fanin na kuma taimaka wa wajen samar da ayyukan yi da samar da abinci mai gina jikin Dan’adam da kuma bunkasa hada-hadar kasuwanci, musamman duba da wayar da kai da ake yi na samar da abinci mai gina jiki,“ in ji shi. Shi ma, a nasa jawabin a wajen taron, Daraktan Cibiyar Bunkasa Samar da...
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa; MDD ba za ta shiga cikin duk wani tsari da ba zai girmama dokokin kasa da kasa ba a Gaza. Bayanin nasa dai ya zo ne a matsayin mayar da martani akan maganar da ta fito daga HKI na cewa tana aiki tare da Amurka domin raba...
“Haƙiƙa muna alfahari da Dr. Sani Dauda Ibrahim da wannan ajin naku, musanman cewa akan ku na fara koyarwa a jami’a, kuma haɗin kan ‘yan wannan ajin ya zama na daban a cikin ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai, musanman saboda ayyuka da kuka gabatar na ci gaban ilimi a jami’ar Bayero da yadda kuke damuwar da al’amuran...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Kara Haske kan Batun Inganta Sinadarin Uranium Da Zamanta Da Amurka
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana sabbin ci gaban da aka samu a tattaunawar da aka yi a birnin Roma Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Ana gudanar da zagaye na biyar na tattaunawa ba na kai tsaye ba tsakanin tawagar Amurka da na Iran a cikin yanayi na kwarewa. Kakakin...
A karo na biyu sojojin kasar Yemen sun sanar da kai hari akan filin saukar jirgin sama na “Ben Gorion” a matsayin ci gaba da taimakawa Falasdinawa da sojojin HKI suke yi wa kisan kiyashi. Sanarwar ta sojojin na Yemen ta kuma ce; Makami mai linzamin da su ka harba, wanda ya fi sauti sauri...
An kashe ma’aikatan ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra’ila biyu a birnin Washington na Amurka Kafofin yada labaran Amurka sun rawaito cewa: An kashe ma’aikatan ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra’ila biyu bayan da aka harbe su a wajen dakin adana kayan tarihi na Yahudawa da ke birnin Washington D.C. na Amurka. Kafofin yada labaran Amurka sun...

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Bayyana Cewa Babu Wata Kyakkyawar Fata A Tattaunawar Iran Da Amurka
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Ba su tunanin cewa tattaunawar Iran da Amurka za ta haifar da kyakkyawan sakamako Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa: Iran ba ta jiran izinin kowa wajen inganta sinadarin Uranium, kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da manufofinta. Jagoran ya ce...
Mahaifinta, Everistus Nnadozie, ya ce an sanar da shi cewa surukinsa Esosa Imasuen ne ya yi wa ‘yarsa duka har ta samu raunika sosai. Ya ƙara da cewa an kai ta asibiti inda likita ya tabbatar da cewa tana fama da zubar jini a cikin jikinta. Ya ce kafin ya isa asibitin, ‘yarsa ta rasu....
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda yake mayarwa da Amurka martani ya bayyana cewa: Ya kamata su daina yin Magana maras ma’ana, fadin cewa Iran ba ta da izinin tace sanadarin Uranium, ganganci ne,domin jamhuriyar musulunci ba ta da bukatar izinin wani mahaluki.” Jagoran juyin musuluncin na Iran wanda...
A yau Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar bude dandalin hadin gwiwa na Shanghai ko SCO na 2025, game da rage talauci da wanzar da ci gaba, wanda ke gudana a birnin Xi’an, na lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin. Cikin sakon na sa shugaba Xi ya bayyana cewa,...
Wani harin kwanton bauna da rundunar sojin al-Qassam suka kai kan sojojin mamayar Isra’ila a Beit Lahiya ya yi sanadiyar halaka tare da jikkatan sojojin mamaya masu yawa Rundunar Izzuddeen al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta sanar da cewa: Mayakanta sun kai wani kazamin harin kwantan bauna a yankin al-Atatra da ke...
Wasu shugabannin kasashen Yamma suna barazana ga gwamnatin mamayar Isra’ila kan daukan matakan ladabtarwa kanta Shugabannin kasashen Faransa da Birtaniya da kuma Canada sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka bukaci mahukuntan haramtacciyar kasar Isra’ila da su dakatar da kai farmakin da suke kai wa Zirin Gaza tare da yin barazanar daukar...
Gwamnatin kasar Masar na shirin yin arangama ta soji da haramtacciyar kasar Isra’ila Kafofin yada labaran Isra’ila, musamman tashar talabijin ta 14, sun watsa wani rahoto cewa: Gwamnatin kasar Masar na kokarin karfafa karfinta na soji a tsibirin Sinai, tana mai gargadin abin da ta bayyana a matsayin “yiwuwar rugujewar yarjejeniyar zaman lafiya” da aka...
Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya aika ta’aziyya ga iyalan mutane 37 da hatsarin kwale-kwalen Gbajibo ya rutsa da su daga jihar Neja a karshen mako. A cikin sanarwar gwamna AbdulRazaq ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Neja kan wannan lamari mai ban tausayi. Gwamnan ya bukaci ma’aikatan jirgin da fasinjoji da su...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Kasarsa Ta Jajirce Kan Harkokin Diflomasiyya Domin Kare Hakkokinta
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Iran ta jajirce kan harkokin diflomasiyya kuma tana neman yarjejeniya ta gaskiya Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada kudurin kasar Iran kan harkokin diflomasiyya da kuma cimma daidaito bisa tsarin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, tare da cikakken mutunta hakkin nukiliyar kasar Iran, da...
Iran ta yi watsi da zarge-zargen taron kasashen Larabawa game da tsibirai uku na Tekun Fasha Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da zarge-zargen da ke kunshe a cikin bayanin karshe na taron kasashen Larabawa a Bagadaza dangane da tsibiran Iran guda uku na Babban Tunb, Karamin Tunb da Abu...
Samar da kyakkyawar sadarwa a tsakaninku Yawan magana da sadarwa mai kyau na hana matsala girma. Idan wani abu ya dame ku, kada ku boye, ku gaya wa juna ta hanya mai dadi da girmamawa. Gujewa kwatanta rayuwarku da ta wasu Kowanne aure yana da nasa halin. Kada ku kwatanta rayuwarku da ta wasu, domin...

Jagora: Jawaban Trump A Ziyar Da Ya Kai Wasu Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Abin Kunya Ne Gare Shi Ga Kuma Amurkawa
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya yi watsi da wasu kalaman shugaban kasar Amurka Donal Trump a ziyar da ya kammala a wasu kasashen larabawa na yankin Tekun farisa, ya kuma bayyana wasu kalamansa a matsayin kungiya ga kansa da kuma mutanen Amurka. Har’ila yau Jagoran ya kara...
Shugaban kasar Iran ya jaddadacewa: Sun yi Imani da tattaunawa, amma ba su jin tsoron duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa: Tabbas Iran tana gudanar da zaman tattaunawa da Amurka amma ba ta tsoron duk wata barazanarta, yana mai nuni da kalaman Trump da ke cin karo da juna,...

Rikici Tsakanin Faransa Da Aljeriya Ya Shiga Wani Sabon Salo Na Koran ‘Yan Kasashen Juna Daga Kasashensu
An samu bullar rikicin da ba a taba ganin irinsa ba a dangantaka tsakanin Aljeriya da Faransa Rikicin ma’aikatan harkokin diflomasiyya tsakanin Aljeriya da Faransa ya dawo kan gaba a fagen dakaddamar da ke tsakaninsu. Rikici dai na kara kamari ne tsakanin Aljeriya da Faransa, tun daga rikicin korar ‘yan kasar Aljeriya daga Faransa zuwa...
Sai ya ce “Na riga na amsa wannan tambayar amma har yanzu kana sake maimaita ta. Idan dai za a iya tunawa, ‘yan jarida 43 mazauna Kaduna ne suka halarci taron, ciki har da wasu ‘yan jarida daga wasu jihohin da suka raka gwamnonin nasu. Don haka, ba daidai ba ne a ce na hana...
A kokarin da yake yi na jigilar maniyyatan aikin hajjin bana, Kamfanin jiragen sama na Max Air yace zai kwashe daukacin Alhazan Jihar Jigawa cikin kwanaki biyu. Mataimakin mai kula da ofishin kamfanin dake jihar kano, Mr Barnabas Anderson ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a shelkwatar...
Wakilan kafafen yada labaran, sun tattauna kan kalubalen da fannin aikin noman kasar ke fuskanta da suka hada da rashin samar ainahin bayanai kan abin da ya shafi aikin noma. Rashin bayar da ingantaccen dauki ga fannin daga bangaren gwamnati, kalubalen rashin tsaro da zabar wasu ‘yan lelen kafafen yada labarai, musaman da gwamnatin kasar...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Karfin Tsaro Da Makamansu Masu Linzami Ne Suka Hana Makiya Kai Musu Hari
Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada cewa: Ƙarfin tsaron Iran da makamanta masu linzami suna ba su ƙarfin gwiwa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa, da a ce Amurka za ta iya lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, da ba za ta shiga zaman tattaunawa ba, yana mai jaddada cewa: Iran ta dogara...
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta zargi Isra’ila da amfani da katangewar da ta yi wa Gaza a matsayin makamin kawar da wata al’umma. A wani rahoto data fitar yau Alhamis, kungiyar ta Human Rights Watch ta zargi Isra’ila da yin amfani da shingen da aka yi wa Zirin Gaza a matsayin...
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ya sauka kaɗan a watan Afrilu 2025 zuwa kashi 23.71, daga kashi 24.23 da aka samu a watan Maris. Wannan na nuna cewa hauhawar farashi ya ragu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, inda a watan Afrilun 2024 aka samu kashi...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da jagoran da ya kafa majalisar bunkasa cinikayya ta Denmark dake kasar Sin ya aike masa, yana mai karfafa gwiwar cibiyar da kamfanoni mambobinta, da su samar da sabbin gudummawar raya alakar Sin da Denmark, da kawancen Sin da Turai, kana su zurfafa hadin gwiwa na cimma...

Shugaban Hukumar Makamin Nukliya Ta Kasar Iran Yace, Kasarsa Bata Buye Wani Shirinta Na Makamashin Nukliya Ba
Shugaban hukumar Makamashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Eslami ya bayyana cewa kasarsa bata boye wani wuri inda take sarrafa makamashin Nukliya wanda bata fadawa hukumar IAEA ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Muhammad Islami yana fadar haka a jiya Laraba, kuma don kare matsayin Iran na mallakar fasahar nukliya ta...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da zargin da shugaban kasar Amurka Donal Trump yayiwa JMI a lokacinda yake ziyarar aiki a birnin Riyar na kasar Saudiya a ranar talatan da ta gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na fadar haka a jiya Laraba ta kuma kara da...
Ministan harkokin wajen Iran ya mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan game da Iran Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Amurka ita ce ta kawo cikas ga ci gaban al’ummar Iran ta hanyar kakaba takunkumai, matsin lamba da kuma barazanar soji da ba na soji ba,...