Game da siyasar Bayelsa, ya ce bai taɓa taka rawa a matsayin uban gidan Diri ba, sai dai kawai yana ba da shawara idan aka nemi ra’ayinsa.

Ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa naɗa Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC).

“A matsayinsa na Farfesa a fannin shari’a kuma SAN na farko da aka naɗa a wannan matsayi, ya fahimci nauyin da ke kansa.

Zan goyi bayan tabbatar da naɗinsa,” in ji Dickson.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ya Ƙara Raguwa Zuwa Kashi 18.02% October 15, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP October 15, 2025 Manyan Labarai 2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa October 15, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Rikicin kabilanci: Mutane 2 sun mutu, wasu 7 sun jikkata a Jigawa

Wani mummunan rikicin ƙabilanci a ƙaramar hukumar  Birniwa ta jihar Jigawa ya yi ajalin mutane biyu, yayin da wasu bakwai suka samu munanan raunuka.

Kakakin ’yan sanda ta jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake zantawa da manema labarai. Ya ce tawagar jami’an tsaro ƙarƙashin Operation Salama sun garzaya wurin domin dawo da zaman lafiya tare da cafke wasu mutane bakwai da ake zargi da hannu a rikicin.

Ganau sun ce lamarin ya faru ne lokacin da wasu da ake zargin Fulani ne suka kai farmaki ƙauyen Dagaceri, inda suka ƙona gidaje tare da kai wa mazauna garin hari da kibau a lokacin da suke barci. Rahotanni sun ce gidaje da dama sun ƙone a harin da ya faru a tsakar dare.

DSP Shiisu ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun ƙwato wayoyin hannu da layu daga hannun waɗanda ake zargi.

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 9, sun kwato kudin fansa a Borno Soja ya harbe matarsa, ya kashe kansa a Jihar Neja

Wannan lamari dai ya ƙara haifar da damuwa kan yadda rikicin ƙabilanci ke sake bayyana a wasu sassan jihar Jigawa.

A watan Satumbar 2024, akalla mutane 15 ne aka kashe a wani rikici makamancin wannan tsakanin kungiyoyin Fulani a ƙauyukan Zangon Maje da Yankunama a ƙaramar hukumar Jahun.

Sai dai duk da waɗannan matsalolin, Jihar Jigawa na daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Arewacin Najeriya.

Wani bincike mai zaman kansa da gwamnatin jihar ta gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa Jigawa na cikin jihohi biyar mafi kwanciyar hankali ta fuskar tsaro a cikin gida.

A watan Yuli 2025  Gwamna Umar Namadi ya gudanar da  bikin maido da zaman lafiya a ƙaramar hukumar  Guri, bayan shekaru da dama na rikicin manoma da makiyaya.

Yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin harin, mazauna yankin na kira ga gwamnati da ta ƙara  tsaurara matakan tsaro da kuma samar da  tsarin gargadin gaggawa na al’umma domin hana ci gaba da  zubar da jini.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jami’an FRSC Sun Mayar Da N6.2m Da Suka Tsinta Bayan Aukuwar Hatsarin Mota A Katsina
  • Ka da a ɗora wa Tinubu laifin rikicin da ke faruwa a PDP — Fayose
  • An kama mutum shida yayin da ‘yan sanda suka kubutar da mutane uku da aka yi garkuwa da su a Bauchi.
  • Ministan Yada Labarai Ya Bayyana Jihar Borno A Matsayin Mafi Juriya A Najeriya
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun sace dabbobi a Katsina
  • Gwamnan Bayelsa ya fice daga jam’iyyar PDP
  • ’Yan Majalisar Tarayyar Kaduna 3 sun sauya sheka zuwa APC
  • Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano
  • Rikicin kabilanci: Mutane 2 sun mutu, wasu 7 sun jikkata a Jigawa