An kama mutum shida yayin da ‘yan sanda suka kubutar da mutane uku da aka yi garkuwa da su a Bauchi.
Published: 16th, October 2025 GMT
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wasu mutane shida da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da ke gudanar da ayyukansu a karamar hukumar Toro ta jihar tare da ceto wasu mutane uku da aka sace ba tare da komi ba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), CSP Mohammed Ahmed Wakil, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Bauchi.
A cewar sanarwar, rundunar ‘yan sandan ta samu kiran gaggawa daga wani dan banga da ke kauyen Euga da misalin karfe 12:01 na safiyar ranar 29 ga watan Satumba, 2025, inda ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi awon gaba da wasu mutane uku wato Idi Umar, Idi Lawan, da Musa Lawal.
Wakil ya ce “A martanin da aka mayar, an kaddamar da wani aiki na hadin gwiwa wanda ya hada da rundunar ‘yan sanda ta Toro, Toro Division, Nabordo Division, da kuma jami’an tsaro na cikin gida.”
Ya kara da cewa rundunar hadin guiwa ta bin diddigin wadanda ake zargin har zuwa wajen kauyen, inda suka gudanar da wani samame na dabara wanda ya kai ga ceto wadanda lamarin ya rutsa da su tare da kama wasu mutane shida da ake zargi.
Wadanda aka kama sun hada da Abubakar Usman, Adamu Alo, Abubakar Aliyu, Umar Habu, Abubakar Mamman Abubakar, da Shehu Sambo.
Karshen/Alhassan.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Tsaro Bauchi wasu mutane
এছাড়াও পড়ুন:
An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa
SP Shiisu ya ce bincike na ci gaba domin gano musabbabin ɓarkewar rikicin.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su ƙara haɗa kai da jami’an tsaro da kuma gaggawar bayar da rahoto idan suka lura da wani abin da zai iya janyo rikici, domin kauce wa zubar da jini.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA