Rahotanni na nuna cewa akwai yiwuwar Shugaban Kasa Bola Tinubu ya cire wasu sunaye daga jerin wadanda ya yi wa afuwa bayan cece-kucen da hakan ya jawo.

Hakan dai ya biyo bayan ci gaba sukar lamirin hakan da jama’a ke yi, musammam kan saka wasu rikakkun masu laifi da kotu ta yanke wa hukunci daban-daban.

Saudiyya ta zaftare wa Najeriya guraban Aikin Hajji da sama da kujeru 28,000 ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 8 a harin kwanton ɓauna a Zamfara

Afuwar shugaban kasa da ake bayarwa a lokutan bukukuwan ƙasa, ana yin ta ne don rage cunkoso a gidajen yari da kuma ƙarfafa sulhu da haɗin kai.

Sanarwar fadar shugaban kasa ta ce an yanke shawarar ne bisa shawarwarin Kwamitin Shawara na Shugaban Ƙasa kan Afuwa, wanda Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ke jagoranta.

Sai dai wannan lamari ya sake tayar da cece-kuce kan gaskiya da sahihancin tsarin afuwar Najeriya.

Amma a ranar Alhamis, Ministan na shari’a ya ce afuwar da shugaban kasa ya sanar ba a kammala tantance ta ba, kuma har yanzu akwai sauran matakan da ba a kammala cikawa ba.

Cece-kuce na ci gaba da tasowa kan wasu sunaye da aka haɗa a ciki, inda hukumar EFCC, ICPC da NDLEA da sauran hukumomin tsaro suka fara kokarin dakatar da sakin wasu daga cikin waɗanda ke cikin sunayen.

A taron Majalisar Koli da aka gudanar a ranar 9 ga Oktoba, 2025, fadar shugaban kasa ta shelanta sunayen mutum 175 da aka yi wa afuwar, ciki har da masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, masu laifukan ofis, masu laifukan miyagun ƙwayoyi, Manjo-Janar Mamman Vatsa, Farfesa Magaji Garba, Ken Saro-Wiwa, mutanen Ogoni, Maryam Sanda da ma wasu da dama.

Yayin da sunayen wasu ’yan siyasa kamar Herbert Macaulay da Farouk Lawan ba su haifar da cece-kuce ba, haɗa sunayen masu laifukan tashin hankali da karya doka ya jawo fushi daga jama’a.

Daya daga cikin sunayen da suka jawo cece-kuce shi ne Maryam Sanda, wacce aka yanke wa hukuncin kisa a 2017 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello.

Yayin da wasu daga cikin iyalan marigayin suka ƙi amincewa da afuwar, Alhaji Bello Isa (mahaifin mamacin) da Alhaji Garba Sanda (mahaifin Maryam) sun gudanar da taron manema labarai don karɓar afuwar ta shugaban kasa.

Shugaban kasa ya kuma yi wa Major S. Alabi Akubo afuwa, wanda aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai kan mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, da kuma Kelvin Prosper Oniarah, wanda aka danganta da hare-haren garkuwa da mutane a jihohin Delta, Edo, Ribas, Abia, Binuwai da Oyo, inda aka gano sansanoninsa na tsare mutane a Warri, Kokori, Ugbokolo, Benin City da Aba.

Kazalika, sunayen waɗanda aka yanke wa hukunci kan kashe jami’an tsaro, safarar miyagun ƙwayoyi, da satar kuɗi, da sauransu, sun jawo tambaya daga jama’a.

Rahotanni sun nuna cewa wannan cece-kuce ya sa fadar shugaban kasa ta fara nazarin sake duba tsarin afuwa, tare da yiwuwar cire sunayen da suka jawo suka daga jama’a.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Afuwa Maryam Sanda

এছাড়াও পড়ুন:

Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia October 21, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 3.5 Ga Shirin Samar Da Abinci A Zambia October 21, 2025 Daga Birnin Sin Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka October 20, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jihar Jigawa Za Ta Kashe Sama Da Naira Biliyan 2 Wajen Binciken Albarkatun Kasa
  • Birtaniya Ta Cire Kungiyar Tahrirush -Sham Daga Jerin Yan Ta’adda
  • Majalisa Ta Tabbatar Da Yusuf A Matsayin Sabon Shugaban NPC, Wasu 2 A Matsayin Kwamishinoni
  • Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin
  • Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar
  • Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara
  • Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Mukaman Gwamnatin Tinubu inji  Shugaban FCC
  • An kama ɗan uwan Nnamdi Kanu da lauyansa —Sowore
  • Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja
  • Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC